Page 22

1.9K 84 0
                                    

_*® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*_ 💭💭💭

💞💞💞 💞💞💞
*BURINA*
💞💞💞 💞💞💞


©
*ZULAYHEART RANO*💞

*Dedicated to AYSHA ALIYU GARKUWA*

Am back in sha Allah, daga yau babu tsayawa har sai mun kai karshe da yaddar mai du ka. Ina godiya sosai gareku masoya yan facebook da WHATSAPP har ma da wattpad duk ina ganin sakonninku na tabbatar ana tare irin har abada ɗin nan.

2⃣2⃣

Wani irin kallo Zainab ta aikawa da Alhaji wanda ke tsaye gabanta, wannan kallon shi ya haddasa masa tsayawar maganar bakinsa, buɗe kofar motar ta yi daidai da isowar IK da Fawzan "Please Malam ina bukatar hanya." IK ya yi maganar yana kama murfin motar, "Ok." Alhaji ya Faɗa yana ja baya jikinsa a sanyaye. Shi kam IK sam bai wani lura ba sai ma shiga motar ya yi Fawzan na yi masa surutu, dukar da kai Zainab ta yi zuciyarta na yi mata mugun zafi, bata ma san time ɗin da IK ya tada mota ba.
Alhaji na ganin IK ya cilla motarsa a titi ya yi saurin shiga ta shi motar, wanda ya amsa wajen abokinsa cikin ikon Allah ya yi nasarar bin su a baya, ɗago da kai Zainab ta yi ta hango Alhaji na biye da motarsa a baya duk maganar da IK ke yi mata bata fahimta, ita yanzu babban matsalar ta shi ne Allah yasa kada Alhaji ya san Fawzan yaron shi ne, saboda zata jure komai amma banda rabata da Fawzan tana wannan tunanin ta ji motar ta tsaya, da wani irin yanayi ta ɗago kai sansanyar ajiyar zuciya ta sauke ganin Alhaji bai shigo gidan ba, addu'a take kada Allah ya kawo shi.
"Wai lafiya kuwa Ummu Fawzan?" "Me ka gani Abu Fawzan?" "Naga tun da kika amshi Fawzan a hannun mutumin can kike ta damuwa?" Murmushi ta kalkalo wanda iyakar sa laɓɓa ta ce "No babu komai fa kawai ciwon kai ne amma yanzu idan muka shiga zan sha magani." "Ayya sannu Allah ya sauwake, ki yi kokarin shan maganin kinga gobe za ki tafi Rano kar ki jewa Baba cikin rashin lafiya." "In sha Allah zan yi yadda ka ce." Daga haka suka fita daga motar inda suka nufi cikin gida, IK na gaida Umma suka kuma fita da Fawzan, ya yin da Zainab ta kule uwar daki tana hawaye don tasan ba su da karfin hana Alhaji amsar yaron shi idan ya bukata, gabanta ya yi mummunar faduwa tunawa da Mummy.
Haka ta kwana sam jikinta babu kuzari, duk tambayar da Umma ta yi mata amsar kenan babu komai, har garin Allah ya waye suka hau shiri karfe goma suka gama komai sannan suka dauki hanyar Rano, tun da suka kama hanya ta ɗan samu sauƙin zuciyarta domin tunawa yau zata ga Babanta mai share mata hawayenta. IK da Fawzan a gaba Umma da Zainab suna zaune a baya karfe sha daya da rabi suka isa garin Rano, gidan Baba suka wuce, sosai suka yi farin cikin ganin juna babu ma kamar Baba da ya ga Fawzan farin cikinsa kasa boyuwa ya yi.
Shima Fawzan sai tsalle yake a jikinsa, bayan sun ci abinci sun huta umma ta nufi gidan yan'uwanta su kuma suka nufi gidan da IK ya gama ginawa domin bikin saura kwana shida ya rage, kuma a cikin gidan za su fara zama kafin su koma kano, gida ne babba na gani na fada tsayawa faɗan girmansa bata lokaci ne, an k'awata shi da kayan dakin zamani kudi sosai IK ya narkawa gidan duk don ya faranta ran Zainab, bangaren Fawzan kadai abin kallo ne babu abin da babu na wasan yara har wani fili aka yi masa mai kyau ga yi ma dai daici irin wanda zai rika buga ball a ciki, Zainab kasa ɓoye farin cikinta ta yi domin sosai IK ya gama faranta mata ita da danta, kullum addu'arta Allah ya karawa IK budi na Alhairi, kai masha Allah komai ya yi sai mu yi fatan a tare lafiya.
Bayan sun dawo IK ya koma Kano Zainab na zaune tare da Malam Sa'idu suna hira irin ta uba da 'ya Malam Sa'idu ya gyara zama tare da duban Zainab ya ce "Zainabu kwanaki mijinki Baban yaron nan ya zo don rashin kunya wai yana neman ki." "Ya zo Baba yana nema na na yi masa me?" Da mamaki ta yi tambayar. "Oho! Masa na ce masa Ni ban san inda kike ba kuma ya nemo ki duk inda kike." "Yawwa Abbana idan ya kuma dawowa karka sakar masa fuska ni wallahi tsorona daya kar ya ce zai amshi Fawzan." Da karaya ta yi maganar. "Kar ki damu da wannan domin kin san dole wata rana sai haka ta faru to ki yi wa danki addu'a da fatan Alhairi." Gyada kai ta yi cikin gamsuwa da maganar sa, sai dai tana jinjina ranar da zata rabu da Fawzan ɗin.
Haka ta ci gaba da zama cikin Rano bata koma Kano ba saboda shirye-shiryen biki da ya kankama, ita sai a yanzu ta tabbatar da zata yi aure ba irin aurenta da Alhaji ba wanda babu komai ciki sai tarin takaici da zallar bakin ciki, amma yanzu yadda take murna yan'uwa da mahaifinta yake murna sai ta ji abin ya kara birgeta Burinta ta ganta gidan IK matsayin matarsa.

****
Sannu a hankali yake biye da motarsu domin ya tabbata wannan ita ce Zainab ɗinsa matarsa farin cikin sa, kuma yana zaton wannan yaron da lokaci ɗaya ya ji sonsa ɗansa, a haka ya ga sun shiga wani gida shi ma ya tura hancin motar zai shiga amma sai mai gadin ya hana, saboda IK Bai faɗa masu yana tare da wani ba, kuma shi bai fadi wajen wacce zai je ba ganin mai gadin ya hana shi shiga sai ya juya kawai, amma cikin ransa murna ne fal domin tun da ya gane inda take ba shi da sauran matsala. Motarsa ya ja ya nufi gidan Mummy, bayan ya yi fakin ya shiga falon da sallama.
Kwance ya samu Mummy tana waya zama ya yi yana faɗin "washh!." Mummy Bata jima ba ta gama wayar tare da maida hankalinta kansa ta ce "na yi tunanin ka tafi fa?" Mtsww ya ɗan saki tsaki "wallahi Mummy ban tafi ba na so tafi yau Allah bai nufa ba, am Mummy yau fa na ga Zainab har gidan da take naje." "What? Mummy ta tambaya tana zare ido." "Haba Mummy Menene na ta yar da hankali kuma?" "Au Allah! Lallai Alhaji wato kai sam baka ji zafin abinda yarinyar ta ja min ba kenan? Ina zaune da mijina ko sau daya bamu taɓa samun matsala ba amma zuwan ta aurena har mutuwa ya yi nikam mai zan yi da yarinyar nan wallahi na tsaneta." A zafafe ta gama maganar.
"Ki yi hakuri Mummy ki bar cewa Zainab ta jawo aurenki ya mutu ki kaddara haka Allah ya ruwaito kinga kuma dole sai ya faru, don Allah ki sota ko dan jinina dake tare da ita." A tsanake Alhaji ke maganar, jikin Mummy ya Dan Yi sanyi don haka bata furta komai ba ta ci gaba da abin da take yi, shi ma ganin haka sai ya nufi bedroom wanka ya soma yi ya yi salloli domin har an yi issha sannan ya kwanta yana mai addu'ar Allah yasa gobe ya ga Zainab.
Washegari karfe sha daya da mintina ya tashi, wanka ya soma yi kafin ya shirya cikin kananun kaya a tsaitsaye ya yo break sannan ya nufi unguwar da ya ga Zainab jiya, daga ɗan nesa ya yi parking sannan ya nufi kofar gidan yana buga kofar, mai gadi ya leko yana tambayarsa ko lafiya? "Eh lafiya lau dama na zo wajen Zainab ce." Ya dire maganar yana washe baki. Kallonsa sosai mai gadi ya yi ya tuna shi ne mutum jiya don haka sai ya ce "Ai sai dai ka yi hakuri domin Hajiya yau sun tafi ita da Alhaji garinsu za a daura masu aure..." Wani irin tari ne ya sarke shi jin furucin mai gadin. Tari mai zafi ya ke yi da kyar ya iya kai kansa wajen motarsa....

Mu je zuwa dai

*RANO*✍

BURINA COMPLETEWhere stories live. Discover now