Page 15

2.3K 108 1
                                    

💞💞💞                    💞💞💞
                       *BURINA*
💞💞💞                     💞💞💞

   
                          ©
                        *Z&R*💞

*Dedicated to AYSHA ALIYU GARKUWA*

                        1⃣5⃣

Wani irin figar mota ya yi sam baya cikin nutsuwarsa, Ikon Allah ne ya kai su wani asbiti dake kusa ko kyakkyawan parking bai yi ba ya fita dauke da ita yana kwalawa Dr kira, jin kiran da yake yi ne ya sanya Nurse suka fito da sauri hannunsu dauke da keken da ake gungura mara lafiya, ganin halin da take ciki da sauri suka nufi emergency room da ita, shi kam yana tsaye bakin kofar hankali tashe, ba ya da wani buri sai na ganin ta samu lafiya.
    Likitan ne ya fito cikin sauri, da sauri ya nufi Dr yana tambayarsa ya ake ciki? Wani Pepar Dr ya mika masa tare da cewa "Ka kwantar da hankalinka ranka ya dade in sha Allah zata samu lafiya, amma ka yi mana sing a nan domin ceto ranta da abin da ke cikinta saboda gaskiya matarka na cikin wani hali." Sam bai wani tsaya sauraron abin da Dr ke faɗa ba kawai ya amshi takardar da sauri yasa hannu yana mai addu'ar Allah yasa a dace. Shi ma Dr komawa ciki ya yi inda ya ci gaba da aikinsa, shi kam in banda kaiwa da komowa babu abin da yake, har aka yi awa daya shiru babu wanda yaga ya fito daga ɗakin, hankalinsa ya kara tashi da yaga awa daya da rabi ya yi, wata doguwar ajiyar zuciya ya sauke ganin ana taɓa kofar alama za a fito, Nurse biyu suka fito fuskarsu dauke da murmushi, ɗaya tana rungume da baby cikin wani kyakkyawan towel milk color, daret wajen sa suka nufa har suna hada baki wajen cewa "Congratulations Sir an samu baby boy." Wani irin murmushi ya ziyarci shi na jin dadi, haka kawai ya samu kansa da farin ciki musamman da suka ce an samu baby boy ai da sauri ya ce
     "Thank you so much ya jikin Madam?" "Babu wata matsala sai dai bata farfaɗo ba." Nurse din ta gama magana tana mika masa Yaron, amsa ya yi bakinsa dauke da bismillah, ya rungume yaron yana mai jin sonsa har cikin zuciyarsa buɗe masa fuska ya yi da sauri ya furta masha Allah domin dai ya kyakkyawane addu'a yake kwarara yaron ta neman tsari da shiriyar Allah, kara rungume yaron ya yi a jikinsa. "Sir zamu tafi da shi dakin a jiya zuwa anjima za a fito da shi." Mika masu yaron ya yi badan ransa ya so ba, don yana jin sa kamar shi ne uban yaro, hannu ya zira cikin aljihu ya ciro kuɗi Wanda baima san yawan su ba ya mika masu tare da cewa "Ga goron albishir nan." Amsa suka yi cikin farin ciki suna zuba masa godiya, ko ta kansu bai biba don hankalinsa kacokan ya koma ga Zee ɗinsa, yanzu burinsa kawai yaga an fito da ita, aiko babu jimawa aka fito da ita don kaita ɗakin da za a kwantar ta. Ya juya zai bisu Dr ya ce yana son ganinsa a ofis.
    Kusan a tare suka shiga ofis da Dr,  mika masa hannu ya yi suka gaisa sannan ya zauna, Dr ya gyara zaman gilashin idonsa sannan ya soma magana cikin faɗa faɗa "abokina gaskiya ya kamata ku rika kula da matanku, musamman idan kunga sun shiga watan haihuwar su, yanzu badan Allah yasa matarka tana da sauran shan ruwa ba rasa ta zaka yi har jaririn don ta jigata sosai." Sai anan ya tsagaita.
    "In sha Allah zamu rika kulawa, mun gode kwarai Allah ya saka da Alhairi."
   "Amin sai a kula da ita ban da ɗaukar abu mai nauyi domin dikin da ke jikinta, ga wannan magungunan a saya yau zuwa nan da six hours zata farka in sha Allah."
    "Mun gode za a kula." Daga haka suka yi sallama da Dr ya fita daret dakin da aka kwantar da Zainab ya shiga, kwance ya sameta da ledar ruwa a hannu. Zama ya yi yana kallon ta wani irin tausayin ta ya kamashi.

Zuciyarsa cike da mamakin yadda mijinta ya barta ta fito a wannan yanayin, yanzu da ta mutu shi kenan "Kai Allah na gode maka daka sa naga Zee." Yana nan zaune sallah kawai ke tayar da shi, sam ya manta da wata aba wai waya har sai da yaga mutane suna amfani da ita kafin ya tuna tana cikin motarsa, don haka da dan sauri ya je wajen motar yana bude motar ya dauki wayar miss Call ya gani over ciki har da na Umma da sauri ya bi na Umma bugu biyu ta dauka, cikin ladabi ya gaida mahaifiyarsa har take tambayarsa yana ina yanzu?
      "Eh! Umma ina Abuja yanzu haka ma ina asbiti." "Wane irin asbiti kuma?" "Wallahi Umma Zainab ce na gani a halin ciwo, gamu a asbiti har an yi mata aiki an fitar da yaro namiji." "Masha Allah Allah ya raya bisa sunna, ya aka yi kuka haɗu?" Da mamaki Umma ta yi tambayar. "Ki yi hakuri Umma anjima ko gobe idan ta farka zamu dawo za ki ji labari." "Allah ya kaimu ka gaida min da ita anjima zan kira mu gaisa."  "Amin." ya amsa.
   Bayan sun gama ne ya kira abokinsa Usman suka yi magana, sai dai bayyi masa maganar Zainab, ya yi waya da mutane da yawa sannan ya koma ciki. Zuwa wannan lokaci kuwa Zainab ta farka tun tana ganin dishi-dishi har idonta ya ɗan soma washewa, motsi bakinta yake a hankali *Ya IK ka taimake ni mutuwa zan yi* shi ne abin da take faɗa, shi ma  sai ka saurara da kyau kafin ka fahimci abin da take cewa, dai-dai da turo kofar da ya yi ganin yadda take yasa ya koma cikin sauri ya kira Dr a tare suka shiga dakin da sauri Dr ya matsa kusa da ita ya fara duba ta, cire mata ledar ruwan ya yi don ya kare sannan ya yi mata duk abin da ya kamata kafin ya juya ga Nurse din da ta shigo ya ce
    "Billy ki haɗa mata tea ga magunguna nan sai ki bata." Daga haka ya fita.
    Sai a lokacin Zainab ta tuna da abin da ya faru da ita, cikin sauri ta kai hannunta saman cikin ta, wayam ta ji aiko wasu zafafan hawaye suka soma zubowa daga idonta, cikin zuciyarta ta ce " *Shi kenan na rasa BURINA su Mummy sun yi nasara a kaina*" ta kara fashewa da wani sabon kuka, domin dai Zainab bata san operation aka yi mata ba, a nata zato ɗan ya mutu ne. Da kyar Nurse ta lallasheta har ta yi shiru sai ajiyar zuciya take.

Shi kam Khalil dake gefe gyara tsayuwa ya yi yana kallonta tausayinta da soyayyar ta suka masa yawa har gobe yana jin son Zainab baya jin zai iya son wata idan ba burinsa ba, sosai ya shagala da kallonta ya ma manta a cikin asbiti suke. Cikin kankanin lokaci har Nurse din ta gama duk abin da Dr ya sanyata, duk da dai da kyar Zainab ta sha shayin sai da Nurse din ta haɗa da lallasheta kafin ta sha fin rabin cup, sallama ta yi masu ta fita, shiru dakin ya yi sai karan fanka kawai sam Zainb bata  yi tunani Khalil na cikin ɗakin ba, anata tunanin yana kawota ya wuce amma sai  ta ji kamshin turare ya cika dakin ta yi tunanin turaren Dr ne, sai dai har Dr ya fita bata daina jin kamshin ba, don haka sai ta yi zargin mai turaren yana cikin ɗakin don kamshin ya yi yawa a hankali ta soma ɗago da kai fes ta sauke idonta akan na Ik dake tsaye sanye cikin rigar yan ball da dogon wando irin ta sanyin su hannunsa harde a kirkinsa ya na mata wani irin kallo, rigar jikinsa fara ce jessy sai wandon blue, sosai kayan suka amshi jikinsa kallo ɗaya zaka masa kasan hutu ya zauna musamman da skin ɗinsa sai wani sheki take kamar dai wanda baya shiga rana.

" *BURINA* " ya furta cikin daddaɗar muryar sa yana matsawa inda take." Maimakon ta amsa sai sabbin hawaye suka soma zarya a fuskarta.

Ya ja kujera da niyyar zama, Nurse din ɗazun ta yi sallama hannunta dauke da jaririn IK ta mik'awa tana faɗin "Ga beby nan yana bukatar ganin Momynsa da Daddynsa." Amsan yaron ya yi cikin jin dadi ya ce "Haka Momy da Daddy suke buƙatar ganin bebynsu." Murmushi Nurse din ta yi ta fita, Zee dai sarautar Allah ta zubawa ido, kafin ta yi magana IK ya yi saurin mika mata yaron yana faɗin "Ga jaririn ki." Nokewa ta yi wai ita a dole kunya take, sai ga wasu hawaye masu zafi na zallar tausayin kanta da abin da ta haifa, amma cikin zuciyarta wani irin daɗi ta ji tare da gode wa Allah da ya sanya jaririn bai mutu ba "Ke amshi danki ya ji dumin jikinki sai ki bada Number a kira mijinki don yasan inda kike." IK ya yi maganar fuskarsa babu wasa. Shiru ta yi ta kasa bashi amsa domin kukan da take ya ci karfin ta, ganin bata da niyyar yin shiru sai ya ce "ki yi hakuri Zee don Allah ki yi shiru tunda baki bani amsa." Da kyar ta ce  "don Allah ya aike ka kaini Rano."  "To ki yi shiru kin ga ba lafiya ce dake ba dauki danki." Ya karasa maganar yana daura mata yaron a jiki ya fita don sam ya tsani hawayen Zee.
   Tana ganin ya fita ta soma kallon yaron tun daga kafafunsa har fuskarsa ta Alhaji ce duk da yana jariri kamanninsa da mahaifinsa ya bayyana a jikinsa. Gyara rikonsa ta yi tana tofesa da addu'a jin son yaron take ako wane lungu da sako na jikinta.

Sai muce Allah ya raya maki jaririn ki Zainab, gobe kuma zamu waiwaya domin ganin a wani hali Alhaji yake bayan barin Zainab gidan sa.

A yi ta hakuri dani fa, wallah typing Babu sauki, ina sonku fisibilillahi kuma ina kaunar comments ɗin ku

            *RANO*✍

BURINA COMPLETEWhere stories live. Discover now