Page 19

1.8K 75 1
                                    

_*® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*_ 💭💭💭

💞💞💞                    💞💞💞
                       *BURINA*
💞💞💞                     💞💞💞

   
                          ©
                        *Z&R*💞

*Dedicated to AYSHA ALIYU GARKUWA*

_dis page for you Sadiya Taheer ki yi yadda za ki yi da shi in kinso ki hana kowa karantawa sai ke kaɗai, ganin farko naga kin shiga raina ina kaunar ki fisibilillahi_😍😍😍

                        1⃣9⃣

Ganin ta ruga daki sai ya saki murmushi tare da girgiza kai, Umma kallonsa ta yi da mamaki domin ganin da ta yi masa a tsaye, murmushi ya kuma saki a karo na biyu tare da kai hannu ya amshi Fawzan ya ce "Umma kin tsaya kina ta kallona." "Ai dole in kalleka Khalil, shi ne ka taho babu sanarwa?" "Wallahi Umma dama na ce bazata zan yi maku, da kyar aka barni na taho duk kewarku musamman Fawzan yasa na taho BURINA in yi ido hudu da kyakkyawan yarona." Ya dire maganar yana kara rungumar Fawzan wanda sai dariya yake kamar wani yasan IK. "Madallah! Da zuwa ka je ka yi wanka sai Zainab ta kawo maka abinci, bani Fawzan ɗin." "A'a Umma da shi zan tafi ina sonsa kusa dani." "To ai shi kenan dama Mommansa ya yiwa barna ta sanya mutane gaba da kuka shi ne zamu bar mata falon." "Fawzan ne ya yi barna Umma?" "Eh takadda ya yaga mata."  Murmushi ya yi yana barin falon.
     Zainab kam tana koma wa bedroom dankwali ta ɗaura sannan ta koma toilet, alwala ta yi ta gabatar da sallah kafin ta nufi kicin, kallon abincin ta yi tare da girgiza kai ta ce a fili "duk babu cimar da ta dace da Ya IK Dole sai na girka masa wani." Tana gama maganar ta nufi firij kunun ayar da ta haɗa masu ɗazun ta ɗauki gora daya da glass cup ta ɗaura akan tire da snaks ta nufi bangaren sa dake gefen baya, a hankali cikin nutsuwa take tafiya har ta isa kofar nocking ta yi bata san kofar bude take ba sai  da ta ji an ce "shigo" sannan ta tura bakinta ɗauke da sallama. Kan lallausan kafet ta daura kafafunta.
   Yana kwance akan doguwar kujera, jikinsa sanye da bakin gajeren wando da farin  singileti, Fawzan na zaune a saman cikinsa yana masa wasa sai dariya suke kyalkyalawa, kallo ɗaya zaka yi masu su burgeka. Domin sun bala'in dacewa da hadaden falon, a hankali Zainab ta ware ido tare da kallon dakin cikin sakan sittin.
Idan mutum ya shiga falon da lallausan kafet mai kalar bonbita da ratsin madara  zai fara karo, haka ma fentin falon milk be sai  wasu lafiyayyun kujeru da aka k'awata falo kalar kafet ɗin, manne jikin bangon falon kuma kayan kallo ne plas ma da home tiyata da dai duk wasu kayan kallo A kan Centre table ɗin da ke tsakiyar falon ta a je tiren tana faɗin "barka da hutawa Ya IK." "Yawwa Momman Fawzan, ya gida ya Fawzan da Ummana?" "Duk muna lafiya." Ta ba shi amsa. "Ya karatu? Insha Allahu zuwa nan da karshen wata zaki fara zuwa school domin Usman ya ce ya amsan maki admitiong." Yana maganar tare da tashi ya zauna. "Na gode Ya IK Allah ya saka da Alhairi." Kanta akasa hawayen farin ciki ya soma zuba.
    "No! Zee BURINA babu maganar godiya tsakanin mu ki yi dai min addu'a BURINA ya cika, bani da wani babban buri sama da na mallakeki, rabon Fawzan yasa na bar gari sai ga shi Allah ya kuma haɗa mu in sha Allah na ji a jikina ke matata ce, BURINA uwar ya'yana." A kunyace ta ce "to Allah ya kara rufa mana asiri Ubangiji ya cika mana burinmu." Daga haka ta mik'e, kallonta ya yi ya ce "kuma ina zaki je muna hira?" "Zan shiga kicin in sama maka abinci, ka fara shan kunun da snaks kafin na gama." "A fito lafiya." Ya yi maganar yana gyarawa Fawzan kwanciya.
    Tana fita kicin ta shiga cikin nutsuwa ta soma aikinta, farar shinkafa ta dafa sai ta soya miyar jajjage wanda ta ji hanta, farfesun kayan cikin rago ta yi masa mai romo wanda ya ji citta da tafarnuwa sosai gidan ya cika da kamshin abincin, har Umma dake falo sai da ta shigo tana faɗin
       "Kamshin menene ya cika min falo haka?" "Umma abinci nake haɗawa Ya IK fa." "Shi ne ya cika gidan da kamshi? Lallai Khalil ɗan gata ne." Tana gama faɗin haka ta wuce." A sauri sauri ta shirya abincin a babban tire, ta zubawa Umma bayan ta kai mata ta gyara kicin ɗin ɗin tsaf sannan ta shiga wanka, bata wani jima ba ta fito, cikin atamfa riga da siket ta shirya sosai kayan suka mata kyau turare baya baya ta sanya sannan ta ɗauki tiren.
      Kai tsaye falon ta shiga da sallama, Usman dake zaune ya yi saurin amsan tiren tare da amsa sallamar ta.  "a'a Ummin Fawzan ke da kanki?" Murmushi ta yi ta ce "Sannu da zuwa Ya Usman ina yini?" "Lafiya lau." Ya amsa da sakin fuska. Sai a lokacin ta kula da ba Usman kawai ne a falon ba, don haka sai su ma ta gaida su kafin ta mik'e zata bar falon har ta juya sai muryar IK ta tsayarta.
     "Zee tsaya ki wuce da Fawzan don ya yi bacci kuma fita zan yi."  To ta amsa tana mika hannu don ta amsheshi sai ko ya yi firgigi ya tashi kankame IK ya yi a nufin shi ba zai je wajen Zainab ba. Murmushi ta yi lokacin da ta fita kofar falon, domin kallon da abokan IK suke mata bata so shi yasa ta fita "ka gani ko yaya Allah ka bar shi a wajen ka idan ba haka ba kuka zai ta yi." "To je ki idan na tashi tafiya zan kawo shi da kaina." Da murmushi yake maganar yana aika mata da wani kallo wanda ke rikita zuciyar Zainab da sauri ta shige falon Umma.

****
Alhaji ne yake ta kai komo tsakanin dakin baccinsu da falo, tsab ya kammala shirin sa cikin suit ash kolo Wanda suka masa kyau, turaruka ya feshe jikinsa da shi sannan ya ɗauki yar jakar da yake tafiya da ita office din, ya juya zai wuce idonsa ya sauka kan Feenah dake aikin bacci, mtsww ya ja tsaki kwata-kwata haushin ta yake ji, shi ya rasa abin da Mummy ta gani ta hada shi aure da wannan mara Kunyar yarinya, tsaki ya kuma ja akaro na biyu sannan ya yi wucewar sa don ganin zai yi litti ga uban yunwa da ke azalzalarsa.
     Suna zaune a falo Ammar da Fatima bayan sun kammala break, hira suke don yau Ammar ba shi da lafiya shi yasa ita kuma Zainab sai da sha biyu zata je, ko sallama babu haka ta fado falon ayam ta galla masu harara tana zama kan kujera, ko kula ta ba su yi ba sai ma ci gaba da hira suka yi ganin basu da niyyar nuna sun ganta sai ta ce "kai kawo min break." Wani kallon rainin wayau Ammar ya aika mata kawai ya tashi daga falon. Itama Fatima tsaki ta yi ta mik'e. "Yan iska masu gadon walak'anci ko Asma'u bata isa ba bare ku." Feenah ta faɗa tana gyara zama. An yi rashin sa a Fatima ta ji don haka cikin wani irin yanayi ta isa gaban Feenah ta daga hannu zata mareta Mummy ta fito.
     "Ke kam baki da hankali uban me ta yi maku haka?" "Mummy zagina fa take yi har da ke." Feenah dake zaune tana tauna cingam kamar tsohuwar kilaki ta ce "Mummy kinsan wannan maganar hankali ba zai ɗauka ba don nikam ban zage ki ba." "Wallahi Mummy karya take ta zage ki ni da kunnena na ji." Ajiyar zuciya Mummy ta yi, tasan halin Fatima ta tsani Feenah. Mtsww ta ja tsaki tare da watsawa Fatima mugun kallo ta ce
    "To na ji." Tana gama faɗin haka ta yi wucewar ta, wani sabon kuka Fatima ta fashe da shi tana takaicin halin Mummy.

A yi hakuri da wannan wallahi bani da lafiya ne kwana biyu, ina barar addu'ar ku.

      *RANO*✍

BURINA COMPLETEWhere stories live. Discover now