Page one

8.3K 355 8
                                    

💞💞💞              💞💞💞
                    *BURINA*
💞💞💞                    💞💞💞

                     ©
                 *Z&R*💞

*Dedicated to AYSHA ALIYU GARKUWA*

11/ 8 /2018

  *Sabuwar marubuciya ce yihakurida error typing*😹😹😹

      0⃣1⃣

       *WUSE II ABUJA NIGERIA*

A hankali cikin wani irin salon tafiya yake takawa, kai idan ka kalle shi ka ce tausayin ƙasa ya ke ji, sanye yake cikin ƙananun kaya riga da wando, rigar red ne shi kuma wandon blue sosai kayan sun amshi jikinsa, hannunsa riƙe da makilin motarsa wanda ya yi parking a parking space na gidan, diret falon gidan ya shiga

Kan lallausan kafet ya ɗaura ƙafarsa, lumshe ido ya yi ya buɗe, yana hamdala ga Allah da Ya b asu ni'imarsa, kan wata haɗaɗɗiyar kujera ya zauna yana furta

        "Ya ilahi."

Murmushi ne kwance a kan fuskar wata farar mace dake zaune a falon, tun shigowar sa ta saki fara'ar ganin sa cikin sanyin murya ta ce

      "Daga gani a gajiye ka kake."

     "Wallahi kuma Mami na gaji sosai." Da ƙyar ya iya furta maganar.

     "Ka yi wanka sai ka ji daɗin jikinka, food is ready."

     "Ok Mami." Ya yi maganar yana tashi tsaye sai wani lumshe ido yake uwa dai mai jin barci.

      "Alhaji! Mami ta ƙira sunansa.

      "Na'am Mamina."

       "Ina fatan baka manta da batun zuwa Rano ba, kasa dai bikin Auwal ya zo ko?"

        "Oh! Sheet Mami wallahi har na manta da maganar bikin fa, zan duba yiwuwar zuwan nawa."

       "Ka duba kam domin dai Auwal ba ƙashin yarwa ba ne."

        "In sha Allah Mami." Daga haka ya haye sama.

Ajiyar zuciya Hajiya ta sauke,

Hajiya Asma'u da Alhaji Ahmad sune iyaye ga Umar Faruk, Alhaji Ahmad  shahararren mai kuɗi ne,, wanda duniya tasan  da zaman sa, shi mai Company *DS DESIGNER* Wanda suka shahara wajen zana gidaje, 'yan asalin jihar Kano a Rano local Government, harkar kasuwanci ne ya kai shi Abuja, matar aurensa ɗaya da yara biyar, maza uku sai mata biyu, Aminu shi ne ɗan su na farko, wanda yake garin Kaduna da aiki, sai Ameena da ke aure a Rano gidan sarki, sai Abdullahi wanda suke kira Alhaji yana aiki ne tare da mahaifin sa a *DS DESIGNER* shi ne *MD* na company, sai Fatima auta Ammar.

Duk cikin 'ya'yan Hajiya Asma'u ta fi son Alhaji domin yana amsa sunan mahaifinta, komai Alhaji yake so tana ƙoƙarin yi masa.

Wannan kenan.

_*Rano local government*_

Filin Federal school dake cikin garin Rano, cike yake tam da mutane, baka jin komai sai ihun jama'a abin da ya ba ni mamaki ƙwallo suke kallo wanda ya yi mugun tafiya da hankalinsu,  ana buga ball ɗin ne da club  ɗin *Rano Miller's and Autan Bawo FC*. Inda Rano Miller's ta ci one zero, saura minti goma sha biyar a tashi, yan Autan Bawo FC sun dage sai sun rama, ya yin da yan Rano Miller's suka ki yarda, saura minti uku a tashi Allah Ya ba shi sa'a ya jefa ƙwallon cikin raga gaba ɗaya suka ɗauki ihun murna, shi kam sama aka yi da shi sai juya shi suke domin ya ci masu zazzafar wasa *Rano Miller's* ta ci two zero, kallon rigar Jessy jikinsa na yi naga an yi rubutu biyu da manyan harfa *IK* min's *Ibrahim Khalil*

Su kam 'yan Autan Bawo FC takaici kamar zai kashe su, don wani a wajen har kuka ya yi, domin dai wannan Ball ɗin ita ce final, haka suka bar filin, shi kam cike da farin ciki jama'a sai yaba ma ƙoƙarin da suke ya nufi hanyar gidan su, yana tafe da abokansa suna hiran yadda wasan ta kaya sai hangota ya yi cikin, da sauri ya ja burki, da sauri abokinsa Usman ya ja tsaki ya ce

    "Kai kam wallahi IK baka yi ba, ya muna tafiya zaka ja ka tsaya?"

     "Kuna iya tafiya ina ruwan ka da tsayuwata?"

     "Babu nasan wancen yarinyar ka hango shi yasa ka wani ja burki, Allah dai Ya kyauta."

     "Amin in har da gaske ka ke yi, ku tafi nikam sai na gana da abar sona."

Dariya suka yi gaba da ya ba tare da sunce komai ba suka ci gaba da tafiyar su, domin a time ɗin gaf ake da kiran Sallah.

Yana nan tsaye har ta matso inda yake, sallama ta yi masa cikin siririyar muryar ta.

       " *Zainab*." ya ambaci sunan ta a hankali, bayan ya amsa sallamar ta.

        "Na'am." Ta amsa tana ɗago jajanyen idonta wanda daga gani babu tambaya kuka ta yi.

Wani irin tashin hankali ya ziyarce shi ganin yadda idon nata ya yi ja,

      "Zeey mai ya sameki?" ya yi maganar cikin zafin zuciya.

     "Babu komai." ta bashi amsa.

      "No! Zeey wallahi akwai abin da aka maki, faɗa min gaskiya Please?"

    Kuka ta fashe masa da shi mai tsuma zuciya, harda shashsheka, jin kukan yake har cikin zuciyarsa, da kyar ta iya furta

       "Inna ce."

      "Me kika mata?"

      "Sun zube." ta ba shi amsa wasu sabbin hawaye suna zubowa.

        "Sun zube ko sorry my Zeey in sha Allah kin kusa fita daga cikin wannan masifa, ki yi haquri duk tsanani yana tare da sauki kin ji ko? Duk wannan maganar suna tafiya ne suke yinsa.

Gyaɗa masa kai ta yi, cikin zuciyarta kuwa tunanin bugun da zata sha wajen innarta take yi, har cikin gida ya rakata da yake shi din sanan ne ne a unguwar.

Durkusawa ya yi yana gaida Inna Uwale, a walak'ance ta amsa tana zabga masa harara, wanda ya sanyaya jikin IK, ya buɗe baki zai yi magana kenan ta yi sauri cewa

      "Karka faɗa min komai domin ba zan saurareka ba, kudina da ta zubar matuƙar ba'a biya ni ba wallahi sai na jibgeta kamar kayan wanki, domin ni ba na ɗaukar asara." Cikin bala'i da masifa ta dire maganar.

     "Ki yi hakuri don Allah, ki barta idan na samu kuɗi wallahi na yi alkawarin zan kawo maki har gida kin ji na rantse."

     "Kai gafara can shashashan wofi, a ina zaka samu kuɗin? Kai ai ina jin baka da rabon arziki a duniya mutumin da ya zauna ba shi da aiki sai buga ƙwallo wallahi ka yi asara, don haka tashi ka bani waje." Ta faɗa tana nuna masa hanya.

Kallon Zeey ya yi wacce ke hawaye a inda take, mugun tausayinta ne ya kama shi, jiki a sanyaye ya bar gidan...

Yawan comment zai sa a ci gaba da typing😹😹😹

BURINA COMPLETEWhere stories live. Discover now