Page 20

2.1K 90 1
                                    

_*® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*_ 💭💭💭

💞💞💞                    💞💞💞
                       *BURINA*
💞💞💞                     💞💞💞

   
                          ©
                        _*ZULAYHEART RANO*_ 💞

*Dedicated to AYSHA ALIYU GARKUWA*

                        2⃣0⃣

Bayan wucewar Mummy sai Feenah ta fashe da dariya har tana rike ciki, sosai Fatima ta ji haushin dariyar tsaki ta ja ta nufi hawa sama muryar Feenah ta ji tana fadin "wannan abin shi ne karami daga tanadin da na yo maku sai na tarwatsa farin cikin gidan nan." Don takaici bata jira jin karshen maganar Feenah ta yi wucewar ta cike da takaici.
    Feenah kam dining table wuce sai da ta cika cikinta kafin ta koma bangaren ta, ta jawo wayarta ta soma kiran uwarta "hello Momi kina jina kuwa? Ta ci gaba "wallahi Momi yarinyar nan Fatima tana niyyar bata mana aiki, domin ta yi mugun samun ido." Mtsww Momi ta ja tsaki ta ce "menene wani ruwanki da kanwarsa tunda kina samun kudi a hannunsa? Ke ni ba wannan ne matsala ta ba so nake ki san yadda za ki yi ki ɗauko min gold ɗin Hajiya Asma'u wanda ta saya kwanaki." "Momi gold kuma ke me za yi da shi?" "Ke bana son tambaya fa, kin san kuwa adadin kudin gold ɗin? To miliyan biyar ta saya ki ɗauko kema da naki kason a ciki, sannan wannan maganin ki dage karki yi sake har Alhaji ya soma magana akan kayansa kin dai san sharadin da boka ya bamu ko?" "Eh Momi zan kula kuma zan dauko maki gold din amma fa idan an sayar miliyan daya za ki bani." "An gama ke dai ki yi duk yadda za ki yi." Daga haka suka yi sallama da Mominta.

Yau ta kasance ranar Lahadi kuma a yau ne Alhaji Ahmad zai dawo gaba daya gidan sai shirye-shiryen dawowarsa suke, lungu da sako duk an tsaftace abinci kala kala aka shirya masa, Mummy sai faman rawan kai ta ke yi, da tasan abin da zai sameta a yau da bata yi wannan rawan kan ba. Karfe ɗaya Alhaji Ahmad ya shiga gidansa cikin zallar farin ciki da kewa, tun daga bakin get ma'aikatan gidan suke masa sannu har ya shiga falonsa, sosai Fatima ta cika da farin ciki da dawowar Abban ta. Sai da ya ci abinci ya yi sallah sannan ya zauna suna hira da ya'yansa yana jin damuwar kowa, Feenah ce ta fito daga ɓangaren ta cikin irin shigar da ta saba, falo ta shiga ko kallon yan cikin falon bata yi ba, firij ta nufa ta ɗauki goran ruwan Faro.
    Daddy da tun shigowar Feenah ya fara tunanin wacce ya yi gyaran murya ya ce "Asma'u wannan wacece?" Washe baki Mummy ta yi ta ce "Feenah ce matar Alhaji ai yarinyar akwai waye..." Wani kallo da Daddy ya watsa mata yasan ya ta yin shiru. Ya buɗe baki zai yi magana kenan Feenah ta riga shi "Hello Daddy sai yau kake dawowa?" Gaba daya suka zuba mata ido cikin mamaki, ita kam ko a jikinta sai ma bude ruwan ta yi tana sha.
       "Ke Feenah ba ki san dawa kike magana bane?" Mummy ce ta yi maganar cikin tsawa. "Haba Mummy kuma ya kike son na yi masa magana? Gaskiya bana son takura." Ta dire maganar tana fita. Girgiza kai Daddy ya yi ya ce "wannan ce kika aurawa Alhaji? Lallai Hajiya kin cuci yaron nan sam wannan bata dace da shi ba , ina ita Zainab yarinya mai hankali da nutsuwa?" Daddy ya yi tambayar tare da kafe Mummy da ido. Tsiru-tsiru Mummy ta yi jin tambayar da Alhaji Ahmad ya yi mata, Fatima kuwa murmushi ta saki tana jiran amsar da mummy zata bada.
       Zazzare ido Mummy ta fara alamar rashin gaskiya ta bayyana karara, ta ma kasa furta ko wacce kalma sai sadda kai kasa ta yi da kyar ta iya cewa "ta tafi Rano duba mahaifinta baya da lafiya" saurin ɗago kai Fatima ta yi don jin karyar da Mummy ta shirga, Ammar kam ko kallonsu bai yi ba don shi mutum ne mara son magana.  Murmushi Daddy  ya yi domin sam bai yadda da amsar Mummy don haka sai ya ce "Hajiya Asma'u kenan ina son ki buɗe kunne da kyau ki ji, wallahi matukar na tambaya na ji saɓanin amsar da kika bani to zamanki ya zo karshe a cikin gidan nan, domin ba zan zauna ke ce za ki rika iko da gida na ba, shi kuma Alhajin zan ganshi." Yana gama faɗin haka ya bar falon.
   Fatima ma tashi ta yi ta haye sama zuciyarta fes, dama wannan ranar take jira kuma ga shi Allah ya nuna mata a fili ta furta "masha Allah! Yau Daddy ya cika min *BURINA* ."

****

Zaune take cikin bedroom bisa sallaya hannunta rike da Alkur'ani mai girma tana karantawa, cikin muryar ta mai dadi da sanyi abin da zai birge mutum yadda take ba ko wanne harafi hakkinsa, Umma dake gefe sai sauraronta take yi har ta dire, sanna ta yo addu'a a tare suka shafa da Umma "Umma na idar da karatun." "Madallah! Yar budurwa ta yanzu dai je ki maida Kur'ani wajen zamansa sai ki amso Fawzan wajen ladidi." "To." Zainab ta amsa tana nufa wajen da ake aje kur'anan. Bayan ta aje ta fita falo don amso Fawzan kamar yadda Umma ta umurta, babu ladidi a falon sai ta nufi bangarensu.
    "Sannu Uwardakina." Cewar ladidi tana washe baki. "Yawwa." Zainab ta amsa cikin sakin fuska. "Ina Fawzan Ummata ce yana wajenki?" "Eh, yana wajena sai ranka ya dade ya amsheshi." Murmushi Zainab ta yi don ta gane wanda take nufi. "Ok shi kenan bari na wuce." Zainab ta yi maganar tana tafiya, wayarta ce ta fara kara don neman agaji tana duba Number din ta ga sunan IK wanda ta rubuta da manyan ba'ki *BURINA IK* murmushi ta saki sannan ta ɗauka, tare da yin sallama cikin siririyar muryarta.
     "Assalamu Alaikum." Daga ɗaya bangaren Khalil ya amsa ya ce "ki sameni bayan gida." Daga haka suka a je wayar.
Cikin nutsuwa take tafiya har ta isa wajen da IK ya faɗa mata, zaune ta gansu shi da Fawzan sai dariya Fawzan ke yi shi kuma IK murmushi, sallama ta yi tare da jan daya daga cikin fararen kujerun dake wajen ta zauna tana faɗin "barka da yammaci BURINA." "Barkammu dai BURINA Momman Fawzan." A lokaci guda suka saki dariya irin ta zallar farin ciki, hira suka shiga tabawa cikin kwanciyar hankali kafin IK ya gyara zama ya fuskanci Zainab ya ambaci sunanta da murya mai cike da nutsuwa.
    Kai ta sadda kasa tare da amsawa muryarta har yana rawa "kina jina ko Zainab ya kamata zuwa yanzu mu san matsaya a tarayyar mu, domin dai daga ni har ke ba yara bane ina son ki bani dama a karo na biyu in kuma shiga rayuwar ki." Tsagaitawa ya yi yana kallonta. Hawayen fuskarta ta share ta ce "Ya IK ai tsakanina da kai yanzu babu maganar gabatar da kai ko maganar ci gaban soyayya, a'a yanzu maganar da zamu tsaya akai shi ne na aurenmu ka shirya ka je wajen Baba ku daidaita, amma kaima ka sa ni da Zainab da abin da Zainab ta mallaka duk karkashin ikon ka muke, indai ni kake neman amincewa to kasa aranka daga yau ka sameni."
    "Alhamdulillah! Ya furta cikin murya mai alamar jin dadi, ya kuma rungume Fawzan ya ce "na gode sosai Zainab da Allah ya bani ke matsayin mata uwar ya'yana in sha Allah ba zaki taɓa kuka ba a rayuwar aurenmu dake." Nan suka shiga fira irin ta masoyan da suka mutu akan juna. Ni kaina Yar Mutan Rano soyayyar Zainab da Khalil tana burgeni, soyayya ce su ke yi mai tsafta.
         Ba a dau dogon lokaci ba IK ya je wajen Baban Zainab, take Baban ya bashi Zainab kuma ya ce sadaki kawai zai amsa ya kuma sanyawa abin albarka, har ranar auren aka sanya idan IK ya kuma dawowa nan da wata biyar ko huɗu.

****
Mummy ce cikin bedroom ɗinta sai famar zazzage zazzage take, daga gani wani abin take nema mai muhimmanci saboda yadda ta maida hankali, Fatima ta kwalawa kira cikin daga murya, babu jimawa Fatima ta bayyana tana faɗin "gani Mummy." Harara Mummy ta aika mata ta ce "wane shegen kika ga ya shiga bedroom ɗina?" Dan bata fuska Fatima ta yi ta ce "ni ban ga kowa ba sai wancan Feenah jiya bayan kin tafi dakin Daddy naga ta fito." Dafe kirji Mummy ta yi ta ce "na shiga uku! Feenah? Feenah ce ta shiga bedroom ɗina?" "Eh! Ita na gani Mummy." Fatima na gama faɗin haka ta yi wucewar ta, take Mummy ta daga waya ta soma kiran yan sanda tana sanar masu da su zo gidan ta yanzu.
     Feenah na daki sai ganin Mummy ta yi da yan sanda, basu tsaya tambayar ba'a siba suka sanyawa Feenah ankwa tare da tasa keyarta suka tafi da ita. Duk wannan abu da ake Alhaji da Daddy basu sa ni ba.
    Domin daddy ya tirke Alhaji a falon sa, kallo ɗaya zaka masa kasan ba a cikin nutsuwa yake ba musanman yadda Daddy ke aika masa da mugun kallo. "Ina jin ka Alhaji ina ka kai min yar mutane? Domin mahaifinta ya tabbatar min bata gida." "Ka yi hakuri Daddy wallahi Mummy ce ta koreta bayan ta tilasta min sakinta." Wani irin zabura Daddy ya yi ya ce "saki Abdallah matar taka ka saka?" "Mummy ta sanya ni dole." "Ok shi kenan." Alhaji Ahmad ya yi maganar yana kara waya a kunnensa "ki zo falona yanzu." Daga haka ya kashe wayar. Wani irin faduwar gaba ya ziyarci Mummy ganin fuskar Daddy sam babu wani rahama sai zallar fushi. Gyara zama ya yi ya ce
    "Da farko dai babu abin da zan ce maka Alhaji sai Allah ya saka da Alhairi domin sosai ka yi kokarin cika min BURINA, don haka duk wani abu da kasan mallaki na ne yau nake son ka tattaro ka dawo min da shi saboda baka faranta min ba wallahi nima ba zan faranta maka ba, nan da kwana biyu na baka, kuma dole ka nemo min Zainab a duk inda take tashi ka bani waje mutumin wofi kawai." Wani irin zufa ne ya soma tsiyayowa tundaga kan Alhaji har kafafunsa, tashin hankali karara a fuskarsa. Kafin Alhaji ya yi wani yunkurin sai jin amon muryar Daddy ya yi yana faɗin "ke kuma Asma'u kamar yadda na faɗa maki matuk'ar amsa ta saɓa wanda kika faɗa min kina da hukunci to don haka ki je na baki sak...

Ihun da Mummy ta yi shi yaja wayar hannuna fadi. Ku biyoni don jin yadda zata kaya.

    

          *RANO*✍

BURINA COMPLETEWhere stories live. Discover now