page four

2.6K 135 2
                                    

💞💞💞                    💞💞💞
                       *BURINA*
💞💞💞                     💞💞💞

   
                          ©
                        *Z&R*💞

*Dedicated to AYSHA ALIYU GARKUWA*

*Gaisuwa gareku bazata kare ba Masoya, domin kune abin alfahari ina jin dadi yadda kuke son wannan buk sosai, ina yinku fa kar wacce ta manta da sakon fatan alheri na*😻😻😻

                        0⃣4⃣

Tsayuwar sa ta yi dai dai da fitowar Zee daga cikin gida. Faɗada fara'ar sa ya yi sosai yau cikin farin ciki yake domin zai kai shaidar da gidan su abar kaunarsa, zai cika burinsa.

" *BURINA*" ya furta cikin muryarsa mai daɗi.

"Na'am." Ta amsa fuskarta ɗauke da murmushi.

"Sai ina haka da yamman nan?"

"Zan dibo ruwa ne."

"Mu je na raka ki."

Sun fara tafiya, Zainab ta kalleshi tana faɗin

"Ya Khalil yau baka je ball ɗin bane?

"Banje ball ba BURINA, saboda wani abin farin ciki da ya samemu."

"Ya Khalil abin farin, kai wallahi har na fara murna tun kafin naji ko menene."

"Hmm! Kedai bari mu je famfo, in baki labari."

Suna tafe suna hira har suka isa famfon, sun samu da mutane a wajen sosai, don haka sai suka koma gefe zama suka yi akan wani itace

"BURINA." Ya faɗa yana mai da hankali kanta.

Ɗagowa ta yi tare da kallonsa ba tare da ta amsa ba, shi kam ganin haka sai ya ci gaba

"Na samu ci gaba gobe zamu tafi Abuja a yi mana kwaji akan ball, idan Allah yasa muka haye satin sama za'a wuce da mu Ingila."

"Ingila?" Ta yi  da sauri hawaye suna zubowa daga idonta.

Hankalinsa ya tashi da ganin hawayen Zee, idan da abin da ke saurin daga hankalinsa to hawayen Zee ne, bakinsa har yana rawa wajen tambayarta

"Zee lafiya me yasa ki hawaye?"

"Ya Khalil Ingila ka ce zaka tafi, dole na yi kuka idan ka tafi dawa zaka barni? Ya Khalil kuɗi fa zaka je ka yi ka manta da wata Zee, don Allah ka fasa tafiya wallahi ina sonka ko baka da sisi *BURINA* in kasance da kai har abada."

"Please share hawayen ki, wa ya faɗa maki zan manta da ke? Idan har za iya manta Zee BURINA, to wallahi zan iya manta kaina, Zee Khalil din ki baya cikin masu butulci ko a wane hali zan iya zama dake, kuma kuɗin nan domin in sanya ki farin ciki zan fita nemansu, duk wuya duk rintsi bazan barki ba Zee sai na cika BURINA." Cikin tausasa murya ya ke maganar.

" Na gamsu da duk bayanin ka, amma ina alhinin rabuwa da kai kada bayan tafiyarka wani abun ya fa, don Allah kasa a daura mana aure sai ka tafi wallahi  ya Khalil haka kadai zai sani kwanciyar hankali."

"Babu abin da zai faru sai Alhairi, ina ji a jikina Zee tawa ce babu mai rabamu dake, ki kwantar da hankalinki anjima Baba zai kawo kuɗin gaisuwa, da na dawo sai a daura mana aure kin ji abar sona?"

Murmushin farin ciki ne ya suɓuce mata, wanda ita kanta bata san da zuwan sa ba ta ce

"Allah ya kaimu ya baka nasara Ubangiji ya cika mana burinmu."

"Amin Zee tawan, Yanzun dai ga wadinnnan kuɗin sai ki rike a hannunki, duk da ba isarki zai yi ba."

"A'a yaya kai yanzu ka fini buk'atar kuɗi, don haka ka rike a hannunka."

"Kina nufin kudin sun yi maki kadan kenan?" Fuska daure ya yi maganar.

"Ba nufina kenan ba, don Allah ka yi hakuri kada ranka ya ɓaci." Maganar take bayan ta amshi kudin tana faɗin

"Nagode."

"Babu godiya tsakanin mu, tashi mu je yamma tana kara yi." Ruwan ta diba IK ya ɗauka, duk da da kyar Zainab ta yadda, har kofar gida ya kai mata kafin sukai sallama, akan da dare zai dawo su yi sallama.

Duk yadda IK yaso yin sallama da Zainab abin bai yiwu ba, domin bayan rabuwar su da ita aka yi masa waya akan ya je kano, sam ransa bai soba ya tafi bayan ya yi sallama da iyayensa.

Suna zaune bayan sun kammala cin abincin dare, Zainab ko koshi bata yi ba duk kuwa da cewar ita ta girka abincin, muryar Babanta taji yana kwala mata kira da sauri ta amsa tare da nufa dakin, da sallama ta shiga ta zauna tana gaida mahaifin nata.

Fuska sake ya amsa tare da ciro kuɗi ya mika mata, hannu biyu ta sa ta amsa tana tambayarsa

"Babana wannan kuɗin fa?"

"Kudin auranki ne." Ya bata amsa kai tsaye.

Murmushi ta saki, a zatonta wanda Khalil ya faɗa mata ɗazun ne, sai ta ji Baban na cewa

"Ki yi hakuri Zainab domin na zartar da hukuncin da bazai maki daɗi ba, domin nima bai min ba, amma kunya da darajar Malam Suleiman suka sa na yadda, ɗazun Malam Suleiman suka zo nan da bukata, wacce bazan iya bijire masu ba Alhaji Ahmad ne ya bukaci da na bama yaronsa aurenki ni kuma na amin..."

Tun bai karasa ba Zainab ta yi wani irin mik'ewa, har kuɗin dake hannunta ya watse bakinta ya kasa furta komai sai da kyar ta ce

"Ba-ba-ba kana nufin ba ga ya Khalil zaka auras niba?"

"Ki yi hakuri Zainab na shiga hakkinki, amma wallahi inda har baki son Auren, na fasa domin har abada farin cikin ki nake so, BURINA shi ne inganki cikin walwala, wallahi Zainab idan baki so ba zan yi maki dole ba, zaki auri zabin ki, duk da ɗazun mun hadu da Malam Sa'idu mun tattauna akan maganar ya yi min kyakkyawar fahimta, kuma tabbas naso ki auri Khalil don yaro ne na gari, amma ki yi hakuri."

Wani irin tausayin Babanta ya kamata, duk duniya babu wanda ya nuna mata kauna kamar Babanta da Khalil, don haka bazata taɓa bijirewa umarnin sa ba, murmushi ta saki duk da fuskantar da hawaye ta ce

"Har abada bazan taɓa bijirewa umarnin Babana ba, don haka na amince da zabin, indai haka shi zai saka a farin ciki."

"Allah ya maki albarka Zainab, in sha ba zaki taɓe ba, biyayyar da kike min kema Allah zai baki masu yi maki."

"Amin." Ta amsa, kamar daga sama sai ga maganar Inna uwale ya cika dakin.

"To Malam naji komai, da yake munafurci aka shirya shi ne ko a nemoni, saboda ka je ka yi tallar 'yarka wa mai kuɗi, lallai Malam sai yau na yadda kafin kowa son kuɗi a duniya, kuma an ci amanar Khalil sai Allah ya saka masa, yaron da ya like ma yarinya duk kuɗin da ya samu a kanta yake karewa, amma yau shi aka ci wa amana lal..."

Bai bari ta k'arasa ba ya daga mata hannu cikin kunar rai ya ce

"Uwale fitar min a daki." Ganin yadda ya yi maganar yasa ta fita bayan ta tsuguna ta kwashi wasu daga cikin kuɗin ta ci gaba da fadin

"Dole na dibi kuɗi domin ni na wahala da yarinyar don haka nima na kwashi rabona."

Girgiza kai Baba ya yi ya ce da Zainab ta je ta kwanta, ta ci gaba da addu'a, haka Zainab ta tafi kwana ta yi kuka da addu'a kamar yadda Baba ya faɗa mata.

*****

Washe gari su Alhaji suka koma Abuja, inda suke ci gaba da harkokin su, Mummy sam ta manta da maganar da Daddy ya yi akan auren Alhaji karami don haka bata wani damu ba.

Shi kam Daddy sai shirye-shirye yake, kusan komai ya saya sai yan wanda ba'a rasa ba, suna zaune a falon Daddy bayan ya dawo daga office,  suna dan taɓa hira tare da kallon labaran karfe tara

Gyara zama ya yi yana ci gaba da kallon tv

"Yau saura kwana shida bikin Alhaji karami, sai ki fara shiri."

"Ban gane ba wane Alhajin kuma?" Mummy ta yi tambayar hankali tashe.

"Alhaji nawa gareni? Abdullahi nake nufi, ko har yanzu baki gane ba?"

"Inna lillahi! Ta furta cikin tashin hankali, Alhaji kana nufin aure zakawa Babana ban sani ba?" A fusace ta dire maganar.

"Ban isa yin haka ba kenan?"

"Ina sam..."

              *RANO*✍

BURINA COMPLETEWhere stories live. Discover now