Page 25

1.9K 96 0
                                    

_*® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*_ 💭💭💭

💞💞💞                    💞💞💞
                       *BURINA*
💞💞💞                     💞💞💞

   
                          ©
  *ZULAYHEART RANO*💞

*Dedicated to AYSHA ALIYU GARKUWA*

Godiya gareku masoya ina jin dadin yadda kuke nuna kaunar ku ga wannan labarin Allah ya bar mu tare har gaban abada.

Fatan Alhairi gareki
Khadijah Iman Bello

Jinjina da yabo ga My Besty Khadija S Moh'd Allah ya barmu tare Alhairi Allah ya tabbata a gare ki.

                        2⃣5⃣

Gaba daya yan dakin kan Zainab suka yi a firgice suna kuka tare da tambayar abin da ya faru, daidai zuwan Abba hankali tashe a fili ya furta "Ta faru ta kare." Domin ganinta kwance babu alamar numfashi ya tabbatar masa da ta ji abin da ya faru, zufar da ya tsatsatsafo masa ya yi saurin sharewa ya ce da raunanniyar murya "ku taimaka a kaita asbiti
noomin tana da buk'atar taimako." Cikin lokaci ƙalilan suka isa babban asibitin dake garin ta Rano kuma a daidai lokacin ake shigo da IK, gaba daya accident and emagerncy aka shigar da su, likitoci suka duk'ufa sosai a kansu.

Duk iya kwarewar su sun zuba amma abin ya faskara, musamman akan IK har gara Zainab wance aka samu da kyar ta farfaɗo, amma numfashin ta bai daidaita ba sai da aka sanya mata abin zuko numfashi. A jiga ce likitocin suka fito aka barsu tare da wasu likitocin dab Nurse, ai da sauri Abba ya yi kan likitocin yana tambayarsu ya jikin. "Ka kwantar da hankalin ka Baba mu je office sai mu yi magana." Jikin Abba ya gama sanyi hatta kafa da kyar yake iya dagawa Umma kam ta kasa cewa um bare um-um sai kallon kawo take zuciyarta na yi mata wani irin suya. Cikin office din Dr bayan ya nunawa Abba in da zai zauna sai ya fara rubuce-rubuce a littafin dake gabansa kamar minti biyu sannan ya ɗago tare da kallo Abba wanda ya yi tsiru yana son jin bayanin Dr.

"Da farko dai Baba Ina mai maka nusiha akan yadda da kaddara, domin wannan shi ne kaddara yara biyu su samu matsala a lokaci daya, duk iya kokarinmu mun yi amma mun kasa domin kuwa har yanzu IK Bai farfaɗo ba hasalima bai san wanda ke kansa ba, dalilin halin da ya tsinci kansa a ciki kara biyar ne a jikinsa ga raunika da ya ji, babban matsalar shi ne kansa ya bugu sosai amma in sha Allah zai warke."  "Karaya biyar Dr?" Abba ya tambaya cikin sauri. "Eh, amma wannan kar ya tashi hankalinka zamu yi bakin k'ok'arin mu." "Allah ya baku iko." "Amin  gara Zainab mun samu numfashin ta ya dawo sai dai bai koma normal ba kuma bata san wanda ke kanta ba, amma a yi hakuri a ci gaba da addu'a komai zai daidai zamu yi iya bakin k'ok'arin mu har Allah ya basu lafiya."  A jiyar zuciya Abba ya sauke cikin damuwa ya ce "babu komai Dr in sha Allah zan ɗauki kaddara kuma zan ci gaba da addu'a har Allah ya basu lafiya." "Amin Baba ga. Daga haka Dr ya sallami Abba ya fita jikinsa babu kwari ji yake kamar zai fadi.

Usman ne ya shigo asbitin a firgice domin shi kansa sai yanzu aka samu ya farfaɗo daga sunan da ya yi tun time ɗin da motar su ta yi accident, gaban Abba ya zube yana wani irin kuka mai ban tausayi, duk wanda ya ganshi yasan yana cikin tashin hankali daga kansa Abba ya yi ya ce "ka yi shiru haka Usman addu'a za ka yi wannan kukan ba shi ne mafita ba." "Dole na yi kuka Abba domin ɗazun muke da IK lafiya lau yanzu a ce ya shiga irin wannan halin Abba dole na yi kuka." "Na sani amma ka daure ka yi addu'a Allah ya bashi lafiya tunda ba mutuwa ya yi ba kuma ai cuta ba mutuwa ba ce." "Zan yi Abba." Nusiha sosai Abba ya yi wa Usman har ya tsayar da kukansa sai addu'a yake wa IK da Zainab.

Ya tuna ɗazun bayan sun gama shiryawa shi da sauran abokan IK sai suka nufi inda IK me zaune ya zuba tagumi da gani ya afka tunanin duniya, da sauri Usman ya k'arasa wajensa yana faɗin "kai IK Menene haka ka zauna ko wanka ba ka yi ba gamu duk mun shirya?" "Ka bari kawai Usman wallahi ji nake kamar kar na je Rano gabana faduwa yake kamar wani abu zai faru." "Haba dai me zai hana ka zuwa bayan yau ranar farin ciki ce a gareka ranar da burinka zai cika zaka mallaki Zainab matsayin mata uwar ya'yanka, Please tashi ka yi wanka ka riƙa maimaita Inna lillahi sha Allah lafiya za a yi komai." Da kyar Usman ya lallaɓa shi ya yi wanka ya feshe jikinsa da turaruka masu kamshi cikin wata dakakkiyar shadda fara kal ya shirya, sosai ya yi kyau nan fa abokansa suka fara masa kirari "Ango kasha kamshi kaga angon Zainab." Murmushi kawai yake dokawa domin shi kaɗai yasan yadda yake ji duk da yana son ya yi farin ciki domin yau burinsa zai cika zai mallaki Zainab matsayin mata amma ya kasa jin farin ciki sai alhinin tafiya.

A haka suka fito harabar gidan lokacin ne ya kira wayar Zainab yana faɗa mata ga shi sun dauki hanya, fatan alheri ta yi masa daga haka ya aje wayar, da yake motarsa wani abokin IK ke jan motar da IK ke ciki, shi kuma Usman yana jan wasu daga cikin abokan da mutanen da za su halarci taron daurin auren, sun yi nisa a tafiya har sun zo barkun garin ratse wa wata akuya ne motar ta kwace a hannun sa duk iya yadda ya yi domin taro motar abin ya gagara sai kiran sunan Allah suke, ita kuma mota ta fara yawo abisa hanyar tana juyi wata bishiya motar ta daka shi ne ta tsaya cak, ganin haka ya sanya su Usman da sauran abokan masu raunin zuciya suma wanda basu san har lokacin da aka fitar da IK zuwa asbiti ba, shi ko direba take Allah ya amshi kwanan sa.

****

A cikin Kano kuwa da kyar aka samu numfashin Alhaji ya dawo, hankalin Mummy ya dan kwanta don haka cikin sauri ta kira Daddy tana sanar masa da halin da Alhaji ke ciki, halin ko in kula ya nuna wa Mummy ta dalilin ce wa"Allah ya ba shi lafiya ki ce masa ya yi gaggawar nemo min yarinya tun ban kawo masa yan sanda ba." Kuka Mummy ta fashe da shi tana faɗin "Alhaji wani irin laifi Abdallah ya yi maka da har kake yin irin wannan maganar alhalin yana cikin ciwo? Don Allah ka yi hakuri ka zo ka yafe wa Abdallah na rokeka." Mtsww ya ja tsaki tare da kashe wayar. Yana kashe wayar Mummy ta ci gaba da kuka tana nadamar abin da ta yi bata taɓa jin ta yi nadama ba irin wannan ranar.

Shi kuwa Alhaji Ahmad bayan ya aje wayar sosai ya shiga tashin hankali domin yasan tabbatas alhakin Zainab ke bibiyar Alhaji, Fatima dake tsaye tun farkon fara wayar ta nufo Daddy da sauri cikin kuka ta ce"don Allah Daddy ka yi hakuri ka yafe wa Ya Alhaji kuma ka je kafa halin da yake ciki, tun da Mummy ta yi magana babu mamaki yana wani halin ne Please Daddy." "Shere hawayen ki Fatima, zan je duba Alhaji amma  saboda rokon da kika min je ki shirya ke da Ammar." Yana gama maganar ya wuce bedroom ɗinsa.

Karfe biyu da rabi suka isa kano da yake ba su biya Rano ba, Aunty Ameena da Ya Al'ameen a asbitin suka sake su, domin Daddy ya yi masu bayanin ciwon Alhaji, sosai suka firgita da halin da yake ciki Fatima kam kuka ta fara na tsananin tausayin Alhaji, addu'a suka duk'ufa yi masa na Allah ya ba shi lafiya. A zuciyar Daddy ya kudurci idan a kwana biyu bai samu wani sauki ba zai fita da shi kasar Germany domin ya ga kwararrun likita.

                      *RANO*
Sai da IK ya kwana biyu cur kafin ya fara motsi shima badan yana gane mutane ba, sunan Zainab kadai yake ambato a haka ɗin ma sai ka saurara da kyau kake ganewa, zuwa lokacin kuwa Zainab ta ɗan dawo hayyacinta kadan bata da magana sai na Ik haka, wajensa take wuni da kwana kullum cikin kuka. Kamar yau ma da suke zaune ita da Umma Fawzan na gefe guda yana wasan sa IK ne ya motsa da sauri Zainab ta matsa kusa da shi tana faɗin "sannu yaya." "Yawwa." Ya amsa da kyar "ina Zainab?" Ya tambaya. "Yaya gani nan." "Zainab ce Fawzan fa?" "Ga yi can yana wasa." Ta bashi amsa da raunanniyar murya har hawaye sun wanke mata ido. "Zee kin ga yadda Allah ya mai da ni ko? Ki yi hakuri Zee da duk halin da kika tsinci kanki, wannan jarabta ce daga Allah, don Allah Zee ki kula da Fawzan idan mahaifinsa ya dawo gareki ki yi hakuri ki karɓe shi a karo na biyu, duk yadda naso cika BURINA Allah bai so ba, kuma ya fimu sanin dalilin haka karki bijirewa Allah ki yi min alkawarin ba zaki juyawa Abban Fawzan baya ba?" "Please yaya kabar yin wannan maganar cuta fa ba mutuwa ba ce, maganar Abba Fawzan ka ajeta gefe don Allah, ko zaka mutu sai mun cika burinmu karka manta kaine BURINA Zee ce fa ta Khalil." Wani irin murmushi ya yi da gani kasan yana shan azaba ya ce "Zee kenan duk abin da nake faɗa maki gaskiyaa ne, abu daya nake son shi ne karki manta da ni ko da yaushe ki rika yi min addu'a..." Saurin rufe masa baki ta yi hawaye na tsiyaya daga idonta, girgiza masa kai take jikinta babu inda baya rawa hankalinta ya tashi wannan wacce irin magana yake?

"Umma..." Bata gama maganar ba ta ji yana jan salati "La'ilah Ha'illal Lahu Muhammadu Rasulullah..." "No! Please yaya don girman Allah karka yi min haka, umma ki ce kada ya mutu Please..." Ita kanta Umma dake gefe ta shiga rudu hankalinta ya tashi sosai da yadda Khalil ɗin yake yi...

Yar Mutan Rano tana ba kowa hak'uri.

  *RANO*✍

BURINA COMPLETEWhere stories live. Discover now