Page 12

1.9K 110 8
                                    

💞💞💞                    💞💞💞
                       *BURINA*
💞💞💞                     💞💞💞

   
                          ©
                        *Z&R*💞

*Dedicated to AYSHA ALIYU GARKUWA*

*Ku yi hakuri fan's domin rashin ganin post jiya haka ta faru ne sakamakon bikin babbar aminiyata da za'ayi ranar Saturday, zan tsaya da typing har sai bayan biki yauma na yi ne don karku jini shiru* i love You 😘😘

_Gaskiya ina jin dadin comments dinku ku ci gaba da yi wallahi yana sanya Ni farin ciki, da alama kowa ya tsani ALHAJI DA MUMMY don kusan kowa akan su yake magana🤣🤣_

*TEAM ALHAJI ABDULLAHI AA*😜

                        1⃣2⃣

Ta buɗe baki da niyyar magana kenan suka ji sallamar Alhaji, washe baki Mummy ta yi tare da amsawa

"Baban Mummy lafiya ka dawo yanzu?"

Zama ya yi kusa da ita yana faɗin

"Lafiya lau Mummyna wasu takaddu nazo ɗauka."

"Oh! Ai da har na tsorata da dawowarka yanzu, amma tunda lafiya ai shi kenan."

"Ke! Lafiya kika tsaremu da ido?" Mummy ta yi maganar cikin tsawa.

"Babu komai." Shi ne amsar da Zainab ta ba ma Mummy.

"To tashi ki bani waje."

Tashi ta yi ta je tana ci gaba da aikinta. Bayan tafiyarta Alhaji ya dubi Mummy ya ce

"Mummy yiwa yarinyar can magana ta same ni bangarena." Yana maganar ne yana tashi tsaye.

A firgice Mummy ta ce "Me zata yi Babana?"

"Abu kawai zata dauko min, domin ita na ba wa ajiya."

"To ka dai yi a hankali don na lura yarinyar can shaidaniya ce tana iya ribatarka har ka soma kulata."

"Got for bit Mummy, me zata riba ce ni da shi." A ɗan zafafe ya yi maganar.

"Allah ya huci zuciyar manya." Mummy ta yi maganar cikin sigar lallashi.

Alhaji na wucewa ta kwalawa Zainab kira, cikin sauri ta je tana faɗin

"Gani Mummy."

Harara ta watsa mata ta ce

"Ki je Alhaji na kira."

Zainab tana jin Mummy ta ce Alhaji na kiranta ta ce a zuciyarta "Jarababbe kawai ita tasan jarabarsa ce ta motsa to kawai ta amsa, ta nufi bangaren bata same shi a falo ba don haka ta ce

"Af ai nasan jarabarce, kuma bani binsa sai dai yau ya biyoni." Ta kai karshen maganar tana shiga bedroom ɗinta.

Kan gado ta fada tana furta "wash! Domin dai sosai ta gaji.

Alhaji dake daki duk ya kosa Zainab ta shi sai ya ji shiru duk da ya ji motsin shigowar ta, a fusace ya fita falon wayam ya gansa babu kowa sai karar tv, bedroom ɗinta ya nufa yana cewa. Turus ya yi ganinta kwance a kan gado ta mimmike

Da sauri ya ida shiga ɗakin, yana fadin

"Lallai wannan ta mugun raina min hankali zan yi maganin ki."

Duka ya daka mata a santala santalan cibiyoyinta, a ɗan firgice ta buɗe ido domin har bacci ya soma daukarta.

"Ke Mummy Bata ce maki ina neman ki bane?"

"Wallahi ya Alhaji mantawa nayi bacci ne sosai a idona."

Mtsww ya ja tsaki, bai iya ce mata komai ba sai shafar ta ya soma yi, cikin zafi zafi takaici sosai ya rufe Zainab, don ta lura ita ɗin ba mai amfani ba ce sai idan bukatarsa ya tashi, hmmmm tana gudun ranar da Alhaji  zai shiga hannunta, tana jinsa har ya gaji don kan sa ya barta, ko sauraronta bai ba ya wuce bedroom ɗinsa.

Da ta kaici Zainab ta yi wanka, cikin zuciyarta tsanar Alhaji da na Mummy ne suka cika ta.

****

Haka ta ci gaba da rayuwa cikin wannan gida, ita dai sam bata iya dorarar da wani farin ciki da ta samu, sai ma zallar takaici, tana zaune da yamma a falonta a hankali take shafa cikinta wanda ya soma fitowa don yana cikin wata na bakwai kenan, tana zuba masa addu'a don sosai Zainab ke son abin da ke cikinta, tana inama wannan cikin na yaya Khalil ɗinta ne, tabbas tasan da yanzu cikin farin ciki suke, Allah sarki ko a wane hali yake yanzu? Ta yiwa kanta tambayar da babu amsa.

Da sauri ta soma istigfari don tasan wannan tunanin da ta yi zata iya dibar zunubi.

A kwanakin nan hankalinta a kwance yake domin Alhaji ya yi tafiya kusan watansa biyu kenan shi yasa take jin dadi har dan kiba ta yi, domin da cikin jikinta ya bi ya kwanta a kirji da mazaunai, amman yanzu cikin ya ɗan fito sai ya yi mata kyau sosai.

Har dai zuwa yanzu babu wanda yasan da cikin don kullum cikin hijjab take, don bai hanata komai ba har gara lokacin da yake karami ta yi fama da amai amma yanzu kam Alhamdulillah! Bata jin komai.

Fatima ce ta yi sallama da sauri Zainab ta amsa tana faɗin

"Sis wai yau ina kika shiga ne?"

"Ki bari kawai sis ai yau muna can wajen kallon ball, wallahi gayen ya iya wasa ga shi kuma ɗan Nigeria amma zo kiga yadda yake zura kwallo a raga."

Murmushi ne ya kubcewa Zainab tana addu'ar Allah yasa yaya Khalil ɗinta shima ya zama abin kwatance a Nigeria da sauran ƙasashe.

"Daga maganar Ball sai ki hau murmushi?"

"Eh wallahi nima ina da wani dan uwane mai bugawa yanzu haka yana Ingila."

"Ikon Allah amma shi ne baki taɓa sana min ba?"

"Kin san magana kamawa take, amma in sha Allah duk lokacin da muka je Rano zan kai ki har gidan su."

"Allah ya kaimu."

Zainab na bude baki da niyyar magana suka ji sallamar Alhaji, da sauri Fatima ta ce

"Sannu da dawowa Ya Alhaji."

"Yawwa Fatima kina nan kina taya ta hira ne?"

"Eh! Ta amsa kanta a kasa tana mamakin yadda yau ya yi mata magana ba cikin faɗa ba, ko da ta ɗago bata ganshi a falon ba ai da sauri ta fita ko sallama bata yiwa Zainab ba, wacce ta zama mutum mutumi da fargaban dawowar Alhaji, ɗan cikinta sai wutsilniya yake a cikin har kamar zai tsaga ya fito

Karfin hali ta yi ta mik'e daret dakinsa ta shiga, bakinta ɗauke da sallama, amsawa ya yi yana ci gaba da abin da yake,

"Bari na haɗa maka ruwan wanka." Zainab ta yi maganar tana nufa toilet.

"No! Zo na dan rage zafi a matse nake." Ya yi maganar yana riko hannunta.

Haɗe bakinsu ya yi waje daya yana aika mata sakonnin da, tsayuwa ta gagaresu sai zubewa a kan kafet suka yi duk da haka bai saki bakinta ba, sosai ya duk'ufa don samawa kansa lafiya tafiya ta yi nisa, Zainab har tana maida masa martani sai ta ga ya tsaya cak! Ko kafin ta samo dalilin tsayawarsa har ta ji maganar sa wanda yasa ta faduwar gaba.

"Ke menene yasa Cikin ki tauri har ya soma girma?" Domin shi har ga Allah bayyi tunanin ciki bane.

A kidime Zainab ta ce

"Cic ciki ne." Da in ina ta yi maganar

"What! Ci me...?

Tsawan Alhaji yasa wayata faduwa daga hannunna, don haka sai na ce maku sai ranar Monday ko Tuesday idan Allah ya kaimu an gama bikin, i love You fisibilillahi😘

Wai me kuke tunanin Alhaji zai cewa Zainab?
Shin idan Mummy ta ji maganar cikin Zainab har yana daf da fita duniya wane mataki zata dauka?

Duk amsar tana ga alkalamin Marubuciyar, sai kun bini sannu a hankali har na warware maku

Kar mutum ya wuce sai ya yi comment ehhe🤨


      *RANO*✍

BURINA COMPLETEWhere stories live. Discover now