page 8

2.3K 101 0
                                    

💞💞💞                    💞💞💞
                       *BURINA*
💞💞💞                     💞💞💞

                           ©
                        *Z&R*💞

*Dedicated to AYSHA ALIYU GARKUWA*

*Wannan page din Sadaukarwa ne ga duk wani masoyin wannan buk ɗin*

'''Fatan alhairi ga HASSAN ATK & HUSSAIN ATK'''

                        0⃣8⃣

"Kina jina ko? Buɗe kunne sosai ki ji daga yau duk wani aiki dake gidan nan ke zaki rika yin sa, kama daga gyara min bedroom falo da kicin, duk ke ce mai alhakin gyara shi domin ban ga amfanin zaman ki a gidan ba."

Kan Zainab akasa ta amsa da "To."

"Tashi ki bani waje baki da hutu anan."

Tashi ta yi jikinta a sanyaye, ta nufi bangaren ta, bata tsaya a falo ba domin tunawa da gargadin Alhaji da ya mata, zama ta yi a kasa tare da zuba uban tagumi tana tunani rayuwar da zata yi cikin gidan, ta dade zaune kafin ta tashi.

Washe gari su Aunty Ameena suka tattara sai Rano, aka bar Mummy da Zainab.

Bayan sun gama kammala break wanda ita Zainab bata samu yi ba ta soma aiki kamar yadda Mummy ta bata umurni, sosai ta yi aikin Allah yasa tasa da wahala ko a gida, shi yasa yau ma ta zage damtse, ko break bata yi ba sai da sha biyu ta gota, a haka ma Mummy sai mata masifa take yi.

Sam bata damu ba don har gara masifar Mummy domin bata dukanta amma Inna uwale har dukanta take, tasa a ranta ba zata taɓa kosawa da wannan aikin da Mummy ke sa ta ba, zata jure kuma zata yi biyayya.

Tun daga ranar Zainab ta kasance cikin wahala ta aikin gidan, kullum bata da hutu sai Daddy ya dawo, don akwai ranar da ya sameta tana aikin ya tsare Mummy da tambaya, sai cewa ta yi ai Zainab ɗin ce ta ce zata yi aikin, Daddy bai yadda ba sai da ya tambayi Zainab ta tabbatar masa da haka,  nan Daddy ya yi ta sanyawa Zainab albarka.

  Ko da yaushe cikin aiki Zainab take, sam babu tausayi haka take kasancewa kamar wata jaka, sai dai duk da haka jikinta ya canza domin fatarta ta yi fresh.

****
IK kam yana kasar Ingila cikin farin ciki da nasarori, ya samu karɓuwa sosai wajen mutane, dama Allah ya yo shi da farin jini kowa sonsa yake, cikin watanni uku da ya yi a kasar ba karamin kyau ya yi ba, jikinsa ya sauya sosai duk wanda ya ganshi ba zai ce shi ne IK dan garin Rano ba, domin IK na yanzu ya zama ɗan guy ko wacce mace zata yi burin samunsa matsayin mijin aure.

Ba ya da wani buri da ya wuce ya auri Zainab ya kyautata mata, ya mallaka mata dukkan kansa da abin da ya mallaka, burinsa yaga Zee cikin farin ciki kamar ko wacce mace, duk wani tanadin da yake akan Zainab da iyayensa yake.

Yanzu haka maganar da ake manyan club biyu da ake ji da su a duniyar ball  ne suka zo domin sayan IK don ya iya buga wasa, uban gidansa yana k'ok'arin duba inda IK zai samu farin ciki ne.

Gaf IK yake da samun yancin kai, sai mu ce Allah ya taimaka.

****
Kamar kullum yau ma Zainab ta kammala da aikinta na safe, ko break ta kasa yi don bata jin dadin jikinta, tun da ta tashi mararta ke ciwo dama idan irin wannan lokaci ya yi haka take fama ko a gida, jin ciwon na ɗaɗa gaba yasa ta aje tsintsiyar da ke hannunta Allah yasa ta kammala aikin,  dafe mararta ta yi tare da ci je leɓe da kyar ta furta

"Wash."

A hankali cikin azaba ta nufi bangaren ta, ko kallon gabanta bata yi a falo ta zube tana ta famar juye juye kamar mai shirin haihuwa. A zaba kawai ta ke ci, tun safe har la'asar kuma har lokacin babu wanda ya lekota. Har ta canza kamani don ciwo.

BURINA COMPLETEKde žijí příběhy. Začni objevovat