page six

2.3K 110 2
                                    

💞💞💞                    💞💞💞
                       *BURINA*
💞💞💞                     💞💞💞

   
                          ©
                        *Z&R*💞

*Dedicated to AYSHA ALIYU GARKUWA*

Wannan page din naki kadai domin jin dadin ki UMMYN YUSRAH😍😍, ki daɗe ki yi lastin ki yi shekaru irin ta dabino, Allah ya kara maki lafiya da basira💞, matsalar ki ɗaya kin daina typing mana mawak'ine☹ zanga-zanga za mu yi maki kwanan nan fa🤺🤺🤺

*Ga gaisuwa da fatan Alhairi ga KHADIJA S MUHAMMAD*

                        0⃣6⃣

IK kam kwanan sa daya a Kano suka dauki hanyar Abuja, cikin nasara a gwajin da aka yi masu IK ne mutum na farko da ya soma nasara, ya cika da farin ciki ya tabbata addu'ar iyaye ke bibiyarsa har yake samun nasara. Shi kansa Jamal ya yi matukar mamakin yadda yaga IK na buga wasa cikin manyan yan kwallon Nigeria. Duk da tashin farko IK ya samu nasara amma ba'a barshi ba har sai da aka kuma sanya shi wasannin uku, cikin nasara kuma ya lashe su.

Take kam aka tabbatar da IK cikin wannan suka samu nasarar lashe wannan gasar, cikin su goma su biyar ne suka samu nasara. Kula suke samu sosai ta fannin abinci da tsaro, duk da tarin ni'imar da yake ciki kullum sai ya tuna Zainab dinsa, abar sonsa kuma burinsa babu abin da yake muradi irin ya ga ya aureta. Allah ya cika maka burinka IK

Kwana su bakwai a Abuja, kafin jirginsu ya daga sai  England, cikin wani hadadden hotel aka sauke su, komai nasu abin sha'awa ko yaushe IK Addu'a yake Allah ya bashi nasara, nima ina taya ka IK ko dan ka cika burin ka.

Nasarori sai samuwa suke akan IK, ta kowanne fanni, addu'ar iyaye akan ya'yansu bata da hijabi tsakanin ta da Allah kai tsaye take zuwa, don haka iyaye mu rika yiwa ya'yanmu addu'a har abada basu taɓewa.

****
Karfe shida na yamma suka sauka Abuja, su Inna uwale sai gwale ido ake ana kallon gine-gine, ita kam Zainab shiru ta yi idonta a lumshe, babu abin da take tunani sai yadda rayuwar ta zata kasance a gidan mijin da bata sanshi ba, shi menene halinsa wani irin mutum ne? Tunani dai barkatai haka ta rika yi, ji ta yi inna karima tana faɗin

"Zainab fito har mun iso." Sai a time ɗin hankalinta ya dawo jikinta, wani irin zare ido ta yi ganin irin gidan da suke ciki da kyar ta iya fitowa daga motar bakinta na ambaton sunan Allah.

Kai tsaye sashin da aka gyarawa Alhaji aka wuce da Zainab, domin tare suke da Aunty Ameena tana nuna masu kofar shiga ta juya zuwa sashin Mummy, inna karima ta umurci Zainab ta shiga ɗakinta da kafar dama sannan ta yi bismillah, masha Allah bangaren Zainab ya yi kyau, babu abin da ba'a sa ba, babban falo ne mai dauke da ɗakunan bacci uku, ko wannensu da toilet, sai kicin gefe guda kuma dining table be, ɗakin da suka gani abude nan aka sanya Zainab wacce keta sharar hawaye, Inna karima sai mata nasiha take.

Basu wani dade da shiga ba, aka kawo masu abinci shinkafa ce ta mangyaɗa, ta ji nama da kayan miya, nan fa su Inna uwale aka hauci domin dama muguwar yunwa take ji Zainab kam da kyar Inna karima tasa ta ci, domin sam ji ta yi bata jin yunwa kwata-kwata, da ta danci sai ta tashi ta domin so take ta yi alwala ko azahar bata yi ba ga magriba tana daf, fita ta yi tana faɗin

"Inna karima sallah nake son yi."

"Tofa ga shi kuma kamar babu ruwa, duk da naga akwai toilet a ɗakin matsalar ban iya amfani da shi ba."

"Balle kuma ni da ko taɓa ganin irin sa ban yi ba." Zainab ta bata amsa.

"Bari na fita ko Allah zai sa inga wata ko wani su taimaka, tunda ko famfo ban gani a gidan ba." Inna karima ta yi maganar tana fita daga falon.

Fitarta harabar gidan sai suka yi kicibus  da Fatima wacce ta fito daga falonsu,  ta na ganinta ta saki murmushi ta ce

"Baiwar Allah ina zamu samu ruwa don Allah?"

Itama Fatima murmushi ta maidawa Inna karima, domin bata da walak'anci halin Daddy ke gareta kowa nata ne ta ce

"Ai akwai ruwa a cikin sashin."

"Bamu iya amfani da shi bane ko zaki taimaka."

"Babu damuwa mu je." Inna karima tana gaba Fatima na biye da ita a baya har falon.

Nuna masu yadda ake amfani da famfon toilet din Fatima ta yi kafin ta fita, cikin lokaci ƙalilan Zainab ta yi alwala tare da gabatar da sallah, sannan suma su Inna karima suka gabatar da tasu sallar, suna zaune sai hira suke har a wannan lokaci babu wanda ya leko da sunan yi masu barka da zuwa, sosai Inna karima ke mamakin halin mutanen gidan.

Har garin Allah ya waye basu ga kowa ba, da yake Alhaji Ahmad ya faɗa masu kwana ɗaya zasu yi, suna tashi suka yi wanka gama wankarsu ke da wuya aka kawo masu abin break,

"shayi ne." In ji Inna uwale data buɗe bokatin.

Sai kular ferfesun kan rago, da dafaffiyan shinkafa.

"Wai dana sha, Alkur'an yau zamu cire kwadayin shekara guda, irin wannan garar arziki." Su dai basu takan mata ba.

Da kanta ta dauki Plet ta zuba mai yawa dan hadama, babu wanda ya mata magana su kam Inna karima ta zuzzuba masu komai da komai, suna ci suna santi Zainab ko tunanin cin wani abu bata yi ba domin ji ta yi ta tsani komai, lallashin duniya sun yi amma sam taki. Haka suka gama da yake ta yi wanka kuma ta shirya sai Inna karima tasa ta dauki gyalen ta don zuwa sashin Mummy.

Da kyar Mummy dake zaune a falon tare da Alhaji ta amsa, shi kam ko kallonsu bai yi ba, cikin su babu wanda ya yi zaton Alhaji ne mijin Zainab domin yadda ya nuna masu, haka dai suka gaidata ta amsa a dakile

"To Hajiya mu dai mun shirya ga amana nan mun kawo maki, Allah ya baki ikon rikewa." Cewar Inna karima.

Ko kallonsu Mummy bata kuma ba, sai ma ci gaba da hiransu ita da Alhaji da suka yi, jikisu ya yi sanyi, Aunty Ameena ce tare da Fatima suka shigo falon fuska dauke da murmushi suka gaida su Inna karima,

"Ba dai har zaku tafi ba?" Ta yi tambayar cike da fara'a.

"Eh! Wallahi mun gama shiryawa."

"Allah ya kaiku gida lafiya mun gode sosai."

"Amin." suka amsa.

"Karku tafi ina zuwa." Ta yi maganar tana mik'ewa.

Bata wani jima ba ta dawo, hannunta dauke da kwalin turare da tirmin zani, mikawa Zainab dake lulluɓe da gyale ta yi tana faɗin

"Kanwata ga wannan ki yi hakuri, in ji Mummy." A kunyace ta amsa tana godiya.

Sannan ta mika masu Inna karima dubu ashirin, tana ta kara godiya, su ma godiya suke kamar sa ari baki.

Mummy kam harara ta watsawa Aunty Ameena, jiki a sanyaye suka bar falon, don yanayin Mummy ta tsinka masu zuciya, amma Inna uwale da yake muguwa ce sai fadi take a zuciyarta

"Allah ya kara ba ubanki ya aurar dake ga masu kudi ba, to ashe anyi gudun gara ne aka fadawa zago, babban BURINA shi ne Zainab ki dauwama cikin rashin jin dadi, to yau BURINA ya cika.

Suna fitowa suka yi karo da Daddy, fuska sake ya gaida su

"Yanzu nake shirin aikawa wajen ku, domin mai kaiku ya shirya."

"Muma mun shirya shi yasa muka kaita wajen Hajiya kar lokaci ya kure, bari mu kwaso kayanmu."

"To madallah! Ga motar nan tana jiranku, ina son fita ne don Allah ku kara yiwa Malam Ali godiya in sha Allah zan zo da kaina don na kara gode masa."

"Zai ji suka tabbatar masa."

Tiramen zannuwa ne guda bibbiyu da kudi dubu goma goma Daddy ya basu.

Nasiha sosai Inna karima kewa Zainab akan zaman Aure, banda aikin kuka babu abin da Zainab ke yi ji take kamar ta bisu, tana kallo suka shiga mota direba ya ja suka tafi, kuka take sosai a haka ta koma ciki, a falo ta yadda zango bayan tasha kuka har ta gode Allah.

         *RANO*✍

BURINA COMPLETEWhere stories live. Discover now