Page 26

1.9K 84 10
                                    

_*® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S P.M.L*_ 💭💭💭

💞💞💞                    💞💞💞
                       *BURINA*
💞💞💞                     💞💞💞

   
                          ©
  *ZULAYHEART RANO*💞

*Dedicated to AYSHA ALIYU GARKUWA*

*Kullu Nafseen zaeekatul maut, Allah sarki haka rayuwa take yanzu ana tare da kai mintina kadan sai ace ka mutu, Allah yasa mu cika da imani Ubangiji kasa mu yi kyakkyawan karshe Amin*

'''Ku yi hakuri fans na yi iya bakin k'ok'arina amma abin ya gagara, wallahi Ni kaina mutuwar ta girgiza ni har kuka sai da na yi.

Nasan da yawanku zaku ce kun daina karanta wannan labarin, lallai zan yi bakin ciki in har Naga an daina karantawa, ina so ku sani cewa shi fa mutuwa dole ne idan lokacin mutum ya yi babu tsimi babu dabara sai mutum ya amsa kiran mahalicci domin mutuwa tana kan kowa kuma ko wacce rai da buri take mutuwa, babban burinmu shi ne mu mutu cikin imani da tsoron Allah.'''

Sakon ta'aziyya ga daukacin mabiya labarin burina, musamman yan BURINA FAN'S su da tun jiya suke zaman makoki, Zainab ta ce tana godiya da nuna kulawa gareta.

                        2⃣6⃣

Da sauri ta sake shi ta nufi kiran Dr hankali a tashe ta isa office din tana faɗa masa halin da IK ke ciki, kusan a tare suka shiga dakin waje suka tura su Umma "Dr da kar ku bata lokacin ku domin nasan rai ya yi halinsa, kuma na yadda da hukuncin Allah." Kai tsaye Umma ta yi maganar. Jingina karfin halin Umma suka yi sannan da kyar suka lallashi Umma ta fita akan za su duba shi, a lokacin tuni Zainab ta yi nisa cikin kuka tana fita dirshen ta zauna tana ci gaba da kuka su kuma suka duk'ufa akansa, awannin biyu suka dauka cur akan shi duk iya kokarin su abin ya gagara dole suka hak'ura domin mai shi ya amsa abin sa (Allahu Akbar rai bakon duniya, Allah ya jikan Ibrahim Khalil ya sa aljanna ce makoma.), Zainab a waje banda aikin kuka babu abin da take ta kasa ko da matsawa nan da can, amma Umma akwai karfin hali da farko har ta ɗan firgita amma da ta tuna mutuwa da rayuwa ta Allah ce sai ta shiga yin hamdala ga Allah, tana me nemarwa IK sassauci ga mahaliccin mu.

Wani irin bugu kirjinta ya yi har kamar zai faso, hannunta ta daga wanda ya daɗe da sagewa ta dafe kirjinta da wata irin murya ta furta "ya Allahu." Kallon fuskar Dr kaɗai ya sanya ta mummunar faduwar gaba jikinta kyarma ya fara da kyar ta ya kafa zuwa gaban likitan ta kasa furta komai sai hawaye girgiza kai take domin bata son jin abin da zai faɗa mata, rinannun idonsa ya zuba mata na yan mintina kafin ya girgiza kai share zufa ya yi ya ce "Ki yi hakuri." yana gama faɗin haka ya nufi office ɗinsa. Gani haka sai ta nufi dakin da IK yake hango shi ta yi kwance rufe ruf da zanin dake kan gadon, buɗe baki ta yi tana son yin magana amma wani abu ya tokareta Kara cakume kirjin ta yi tana nuna IK wani irin duhu ne ya ziyarce ta a hankali ta sulale kasa daidai da zuwan Abba.

"Hasbinallahu wa ni'imal wakil Zainab." Abba ya furta a kidime, da sauri Nursee suka taimaka suka shiga da ita wani daki domin ceto ranta. Yana ganin an shiga da ita ya yi saurin shiga, jiri ne ya dibe shi da sauri ya dafe bago yana faɗin "Inna lillahi wa'inna ilaihir a! Kullu Nafseen zaeekatul maut shi kenan Ibrahim Khalil yau Allah ya amshe ka." Sai da ya dawo hayyacinsa ya nufi inda Umma ke zaune kamar mutum mutumi, tausayinta ya rufe shi har ya kasa magana sai share hawaye da ya yi ya ce "Habiba ki yi hakuri ki ɗauki wannan kaddarar."

Murmushi ta yi wanda ya fi kuka ciwo ta ce "tuni na yi hakuri kuma na dauki kaddara tun ganin farko na san Khalil ba lallai ya kai labari ba, ko da yaushe rahamar Ubangiji nake nemar masa kuma Alhamdulillah da kunnena na ji yana salatin Annabi, kuma na san zuwa ka yi don ka ce in Yi hak'uri ya mutu ko? Na san ya mutu Malam." "Haka ne." "Yanzu ina Zainab a wane hali take?" Ta tambaya tana mik'ewa da sunan Allah. "Tana can likitoci suna kanta don ta suma."

Lokaci kalilan aka kai Ibrahim Khalil gidansa na gaskiya tare da rakiyar duban jama'a, halinka nagari ya bika Allah yasa can ya fi maka nan, an dawo gida ana ci gaba da amsan gaisuwa, Usman ya yi kuka har kamar ransa zai fita ko da yake bai gama ba domin duk idan aka zo gaisuwa sai ya zubar da hawaye na tausayin kansa  domin ya yi  babban rashi na aboki  mai amana da tausayi samun madadin IK yasan abu ne mai matukar wahala. Duniyar Ball ma gaba daya ta girgiza da rasuwar hazikin matashi mai ji da kurciya da lokaci wato Ibrahim Khalil (IK)..

Ita kam Umma ko kwalla bata yi ba, sai dai kukan zuciya wanda har ta gwammaci ta yi hawaye, domin wannan zuciyarta ke suya ta rasa danta mai tausayinta da jinkanta addu'a kawai take yi masa. Kwana Zainab Uku sannan ta farfaɗo da wani irin kara tana faɗin "Baka mutu ba wallahi baka mutu ba, Abba da gaske ne ya IK ya mutu?" Da ganin yadda take yi zaka gane bata cikin hayyacinta, don haka sai Abba ya fara tofa mata addu'a da kyar ta samu nutsuwa har ta bude ido tana ganin Abbanta ta yi saurin tashi "Abba bai mutu ba ko? Abba don Allah ka ce min bai mutu ba shi ne BURINA idan ya mutu zan iya mutuwa Abba na rokeka kar ce ya mutu."

"Ki kwantar da hankalinki Zainab ki nutsu ki dauki kaddara addu'a za ki yi masa." "Abba me kake nufi? Kana nufin ya mutu?" Girgiza kai ta yi ta ce "Ya IK Yana nan bai mutu ba ai ya ce ba zai mutu ba sai mun cika burinmu, don haka yanzu zan je dakin da yake sai na ce masa ya ce ka daura mana aure ina son da a haka." Kwalla Abba ya share na zallar tausayin Zainab domin gani yake kamar ta haukace, "kina son ganinsa?" "Eh" ta faɗa da sauri. "To sai kin nutsu tukun." "To ai Abba na nutsu zaka kaini wajen sa?"

"Eh amma sai kin yadda da kaddara." "Kaddara Abba? Wacce kaddarar?" "Wacce Allah ya daura maki." "Abba kaddara Allah ya daura min? Ta yi tambayar tana dube dube. Girgiza kai Abba ya yi tabbas Zainab ta fara rasa hankalita, domin wannan maganar da take yi ba irin ta masu hankali ba ce "Abba ka yi shiru faɗa min mana ba ka ce in natsu ba? To ai na nutsu." Gyada kai ya yi ya ci gaba da magana "ki san dai Yadda da kaddara mai kyau ko mara kyau na daga cikin imani ko? To ki yadda Allahn da ya baki Khalil ya amshi abinsa yau kwana uku da Khalil ya amsa kiran Ubangiji don haka addu'a kawai zaki masa." "Ya mutu Abba me yasa ya mutu ba tare da ya bari burinmu ya cika ba? To Ni yanzu wa zan aura? shi kadai na ke so."

Sam Abba ya kasa jure halin da Zainab ke ciki, don haka sai hawaye yake haka sauran jama'ar dake dakin ziciyoyinsu ya tsinke tausayi da tsoron Allah ya kara shigar su, allurar bacci Nurse suka mata, ko kafin da ta yi bacci sai da ta ci gaba da maganganun ta, duk wanda ya ga halin da Zainab ke ciki indai mai imani ne to sai ya tausaya mata. Time ɗin da ta kara farkawa da sauki domin babu wannan sambatu sai kuka kawai, a kwana na shida ana gobe bakwai aka bata sallama domin Alhamdulillah da taimakon addu'a aka samu ta koma daidai, amma sunan IK ya ki fita daga bakinta ko da yaushe cikin tagumi da tunani sai salloli da addu'oi duk akan IK,  duk ta fita hayyacinta bata kaunar magana da kowa ko da kuwa Umma ce.

             *CIKIN KANO*

Alhamdulillah sauki ya farahanawa samuwa a wajen Alhaji, don ya fara gane mutane sai dai maganarsa bata wuce Zainab, domin sosai yake samun kula daga wajen Dr Asmad, tsakaninji  Mummy da Daddy gaisuwa ce, shima sau daya ya ke amsa mata komai za a yi Fatima yake sanyawa, dan zaman da suka yi sosai Fatima ta ga kamar kubban  canji a wajen Mummy amma Daddy ko kadan bai kula da wani canji ba sai ma karin haushin ta da yake ji a zuciyarsa.

Zaune suke a dakin Alhaji na shan farfesun kayan cikin da Aunty Ameena ta yi masa Daddy ya dube su tare da gyaran murya ya ce "idan an sallami Alhaji Rano zamu wuce domin na dan huta da naso zuwa sipein ne ina huta amma tunda muna nan Gara mu tafi Rano." "Yawwa Daddy daga nan ma zan je gaisuwa wani dan Ball dake Rano ya rasu satin sama, na ji mutuwar mutumin zan je in yi ta'aziyya." "Ke Fatima ba dai IK ne ya rasu ba?" Alhaji ya yi tambayar yana aje plet." "Eh, yaya wallahi shi ne." "Allah sarki Allah ya yi masa rahama." Sosai Alhaji ya ji mutuwar IK.

      *BANGAREN ZAINAB*
    
Kullum umma cikin yi mata nusiha take abinci ma sai ta matsa mata take ci, ko Fawzan bata kaunar ya raɓe ta domin a ganinta ta gama samun farin ciki. Bayan an share bakwai suka koma cikin gidan da IK ya Gina a nan ranon, Zainab ce zaune ta buga uban tagumi sanye da k'aton hijabi sosai ta yi nisa a cikin tunaninta har bata san time da umma ta fito ba, Umma dake tsaye ta zubawa Zainab ido ta girgiza kai sannan ta kasara wajen kujeran da take zaune hannunta dauke da plet ɗin abinci, zama ta yi da sauri Zainab ta saki ajiyar zuciya tana faɗin "Umma Sannu da fitowa." "Yawwa Zainab anata sana'ar ne?" "A'a Umma." "Hmmmm Zainab sam ba ki jin magana na ce ki cire wannan tunanin a ranki ki yi masa addu'a na tabbata da zai dawo duniya yaga yadda kike masa kuka  ba zai taba jin dadi ba." Hawayen da take ma'kalewa ne suka samu nasara saukowa kuncinta.

      *RANO*✍

BURINA COMPLETEWhere stories live. Discover now