Complete

3.6K 129 10
                                    

_*® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S P.M.L*_ 💭💭💭

💞💞💞                    💞💞💞
                       *BURINA*
💞💞💞                     💞💞💞

   
                          ©
  *ZULAYHEART RANO*💞

*Dedicated to AYSHA ALIYU GARKUWA*

*Godiya mai tarin yawa ga masoya wannan littafin, ba zan taba mantawa da ku ba har abada domin kun nuna matukar soyayyar ku ga wannan labarin, musamman yan ZAMA NA AMANA 2, BURINA FAN'S GROUP, UMMYN YUSRAH HAUSA NOVEL'S, LAIFIN WA? & SANGARTA*

WANNAN PAGE DIN FOR YOU HASSAN ATK AND HUSAIN ATK

                        3⃣2⃣

                         *LAST*
Sosai Alhaji ya ji dadin kasancewa da Fawzan, musamman yadda Yaron yake kiriniya hakan ya tabbatar masa da cikin koshin lafiya yake, babu ma wajen bacci da Fawzan ya ki kwanciya sai a jikin Alhaji, aiko dole Alhaji ya shigar shi suka yi baccin su hankali kwance, da gari ya waye Alhaji da kansa ya yi wa Fawzan brosh, har Fawzan ɗin yana cewa "morning Dad?" Don ya saba gaisar da Umma da Mommansa idan sun tashi, murmushi Alhaji ya yi ya amsa da "I'm fine My boy." Bayan sun gama gaisuwar ne s suka nufi falo inda Mummy take, da gudu Fawzan ya karasa wajen Mummy Yana faɗin "good morning." "Morning how are?" Cike da farin ciki Mummy ta yi tambayar. "I'm fine." Ya Bata amsa yana zama a dining, a nutse suka kammala yin break ɗin sannan Mummy ta ba Alhaji umarnin ya kai Fawzan wajen Mommansa, duk tana jin Yaron har cikin zuciyarta bata son rabuwa da shi amma ya zama dole a maida shi wajen Mommansa ko dan kar wata matsalar ta kuma samuwa. "To Mummy amma sai anjima." Alhaji ya ba Mummy amsa da suka koma bedroom, bayan sun koma ne Fawzan ke ce wa "Dad Yaushe zaka kaini wajen Mommana?" "Sai anjima My boy, kana son ganin Momman ka?" Gyada kai Fawzan ya yi alamar"eh." "To ka kwanta zuwa anjima sai mu tafi." Bacci suka koma ba su tashi ba sai karfe ɗaya wanka suka yi suka shirya sosai suka yi kyau kowa ya gamsu yasan uba ne da ɗa musamman tsantsan kamar su, a falo suka yada zango sai da suka yi dinner kafin suka fita, wajen shakatawa daban daban Alhaji ya kai Fawzan har Alhaji ya manta ma zai kai Fawzan wajen Zainab, har sai bayan la'asar ya tuna don haka suna isar da sallah suka nufi gidan su Zainab.

                   *BANGAREN ZAINAB*

Ta sanya rai zai dawo da shi washegari amma har aka yi azahar babu alamar Alhaji zai zo gidan, har wani zazzaɓi ta ji yana niyyar kamata ga shi ta lura Umma ta dau zafi yau da safe da kyar ta amsa mata gaisuwar ta, jiki a sanyaye bayan ta fito wanka doguwar riga kawai ta sura ta nufi falo inda Umma ke zaune a falo, ɗan nesa da Umma ta zauna tare da daura kanta a jikin kujerar ta wani marairaice kamar dai zata yi kuka, Umma dai bata ce komai ba hasalima sai ɗaukar remote control ta yi tana kara vol din TV.
     Zuwa can ta ce "ke kam lafiya?" Hawayen da take ma'kalewa suka sauko kan fuskarta ta ce "Umma Fawzan fa har yanzu Abbansa bai dawo da shi ba." "Fawzan! Au dama duk wannan yanayin da kika shiga ta dalilin Fawzan ne? Shi da kika ce masa tsiya? Ko ba haka kika cewa mahaifinsa ya dauki tsiyarsa ba? Ai ya tafi da shi don ya nuna maki ba tsaya ba ne shi, kuma ko kadan Alhaji bai bani haushi ba domin Ni ce ma na sanya shi ya tafi da Yaron, tun da ke kin zama isassa baki jin maganar kowa sai abin da ranki ya raya maki, Ke Zainab ki rufawa kanki asiri ki dawo cikin nutsuwar ki, wato duk shawarar da na baki ba ki dauka ko?"
     "Ki yi hakuri Umma in sha Allah ba zan kuma bata maki rai ba." "Kullum maganar ki kenan amma kunwnki ba ji yake ba." Sosai Umma ta yi wa Zainab faɗa har jikinta ya yi sanyi bata jin zata kuma saɓawa Umma, ganin time na la'asar ya sawo jiki har wasu masallatan sun kira sallah, sai Umma ta shige bedroom ta bar Zainab a falon ita daya. Kamar daga sama sai jin Fawzan ta yi a jikinta, buɗe ido ta yi cike da mamaki tana faɗin "Daddy Abba Kai ne?" "Eh Momma." Fawzan ya bata amsa. "Kai da waye?" "Dad ne ya kawo ni ya ce yana gaida ki." "Ina Dad din?" "Ya tafi Mummy tana ce tana gaida ki." A maimakon Zainab ta ji dadin ganin Fawzan ba tare da abbansa ba sai ta ji damuwa ya kamata, ko ba komai taso ta kuma ganin Alhaji ko da ba zai ce mata komai ba. Jiki a mace ta ja hannun Fawzan zuwa bedroom Yaron yana ta bata labarin inda Dad ɗinsa ya kai shi cike da farin ciki.
     Wasa-wasa Alhaji ya dauke kai da yi wa Zainab magana, baya shigowa gidan sai ya tabbatar tana makaranta kuma har ya gama hira da Umma ya dauki  Fawzan su je yawo ba ya tambayar Zainab, sai dai idan ta dawo Fawzan ya faɗa mata Da dinsa ya dauke shi sun je yawo, ko kuma ta ga shigowar Fawzan da tarkace idan ta tambaya sai ya ce mata da Dad suka fita, sosai abin ke mata ciwo don har ga Allah yanzu ta sauka ta amincewa zuciyarta zata koma gidan Alhaji da aure a karo na biyu. Kamar kullum yau dai Zee a farfajiyar gida ta zauna, domin wajen ya kasance akwai ni'ima musamman da yake yamma ce sakaliya, farin glass ne manne a idanunta hannun rike da littafi tana karantawa, jikinta sanye yake da riga da siket na atamfa wanda suka matukar amshi jikinta.
     Kamshin turaren ta da nashi ne suka hadu suka bada wata daddaɗar kamshi mai cike da ni'ima da sanya kasala, a hankali ta ɗago kanta fes ta sauke idonta akan na shi, sun bala'in burgeta musamman shigar da suka yi, saurin mayar da kai kasa ta yi tana ci gaba da karatun duk da gaba daya bata fahimtar komai, hasalima ta manta a layin da take. Muryar Fawzan ne ya ratsa mata kunnuwa inda yake faɗin "Momma gani Ni da Dad ɗina." "Na ganku ina maku sannu da zuwa." Ta yi maganar kanta a kasa. "Sannu da hutawa Momman Fawzan Barka da yammaci." Cikin muryar sa ta tsayayyen namiji ya yi maganar.
"Yawwa Abban Fawzan." Ta amsa a takaice. Murmushi ya yi kawai ya shige falon Umma. Fawzan kuwa ya zauna sai surutu yake yi wa Zainab.
    Shiri kawai Zainab ke yi domin yau Rano za su je saboda gobe za a bude makaranta da masallacin da aka gina na mirgayi Khalil, karfe uku na yamma suka isa Rano a gidan su suka sauka sai da suka huta sannan suka nufi gidan Abba, mamaki sosai Zainab ta yi ganin yadda mutane yan'uwanta suka cika gidan ana ta harkoki kamar ana yin biki, suna ganin Zainab suka fara sowa suna ihu ga amarya sosai kanta ya daure, haka nan ta daure ta ci gaba da fara'a har ta shiga dakin Abba, a kusa da shi ta zauna don tuni Umma ta shige dakin bayan sun gaisa ta kula Abba na cikin farin ciki sai murmushi yake yi ta gyara zama tana faɗin "yau Abbana na farin ciki rabon da na ganshi a cikin irin wannan farin ciki har na manta." "Haka yake Zainab ina cikin farin ciki mara misaltuwa domin kuwa zan cika BURINA na auras da Zainab a karo na biyu." Zaro ido ta yi baki har yana rawa ta ce "Abba auras da ni?" .
     Washegari aka bude masallaci tare da daura aure, wanda jama'a da dama suka samu damar halartar daurin auren, farin cikin da Alhaji ya shiga a ranar baya misaltuwa domin shi tun da yake bai taba tsintar kansa a ciki ba sai yau, a bangaren Zainab kuwa kadaran kada han duk da ta yi farin ciki a zuciyarta amma a fili sai ta nuna wa Alhaji bata ji dadi ba. Ranar da aka daura auren Alhaji ya bukaci ta tare, ba don ran Zainab ya so ba tabi Alhaji zuwa Abuja sai da su Abba da Umma suka sanya baki, jirgi suka bi zuwa Abuja don haka karfe biyar a garin Abuja ta yi masu ta samu kyakkyawar tarba daga yan'uwan Alhaji wanda ta yi matukar burge Zainab, tana zaune ita da Fatima suna hira Alhaji ya kira wayarta yana faɗa mata ta shirya ga mai yi mata kwalliya zuwa don za a yi mata kwalliyar zuwa dinner, mtsww ta Saki tsaki ta ce "wai mai yi min kwalliya zata zo sai ka ce wata sabuwar amarya." "Lah ji Sis da wani magana, au ke da kina nufin ke ba sabuwar amarya ba ce? To Yaseen kin fi sabuwar amarya a wajen mu, Please tashi ki shiga wanka, cikin mintinan da basu fi arba'in ba har an kammala mata kwalliya ta yi matukar kyau sosai, karfe takwas aka tafi dinner Allah yasa Fawzan a wajen Umma aka barshi, shi yasa hankali kwance aka yi komai, an ci an sha haka an cashe kuma an yi barin kudi abokan Alhaji sun yi matukar k'ok'ari, karfe sha daya aka tashi kai tsaye Alhaji gidan da Daddy ya Gina masa ya wuce da matarsa don wannan karon ba gida daya zasu zauna da Daddy ba.
     Suna shiga gida Zainab wanka ta soma yi sannan ta yi alwala ta gabatar da salla ko kayan jikinta bata tsaya canzawa ba ta yi kwanciyar ta ɗin ta gaji sosai, can cikin bacci ta fara jin motsin mutum a jikinta aiko da sauri ta tashi ta re da fara masifa "Ni fa wallahi wannan karon ba za a yi min mulkin mallaka ba, sai mutum na bacci don shiga hakki sai a fara takurawa mutum." Tashi Alhaji ya yi ba tare da ya ce komai ba sai girgiza kai ya yi ya bar mata dakin don shi farin ciki yake tun da ga shi ga burinsa Zainab gida daya. Tana ganin ya bar dakin ta gyara kwanciya ta ci gaba da baccinta, da safe Alhaji da kansa ya tashe ta sannan ya wuce masallaci, haka suka ci gaba da zama Alhaji na tattalin Zainab ya nuna mata ba jikinta yake so ba a wannan karon, zallar soyayya kawai suke wa juna sosai ta tabbatar da Alhaji sonta yake tsakani ga Allah, satin su biyu da tarewa amma irin kyaun da suka yi abin gwanin sha'awa, yau dai Allah ya sa Zainab zata shiga hannun Alhaji domin yau din gida ya wuni bai ko fita ko ina ba yana gida hatta magarib a gida ya yi ta, bayan ya idar da issha ya umurce ta da ta kai masa abinci dakin kwanansa, don bai ci abinci ba ya bari sai ya yi issha, Zainab bata nufi dakin ba sai da ta yi wanka ta shirya cikin rigar baccin ta mai matukar daukar hankali bata daura komai ba a kai domin tasan tana yin shigar da ta fi haka daukar hankali amma Alhaji bai taba nuna ya damu ba, shi yasa yau ma ta kai masa har daki ta aje zata koma bedroom ɗinta ya yi gyaran murya tare da fadin
      "Je ki yi alwala." "Ina da alwala ta bashi amsa ok zauna ki jira na kammala cin abinci sai mu yi sallah." Bata mu sa ta zauna har ya kammala ta kwashe kayan ta kai kicin sannan ta koma dakin bayan ta dako hijjab da zani, sallah suka yi raka'a biyu addu'a sosai Alhaji ya yi masu har Zainab tana mamakin ashe Alhaji yana da sa ni a ilimin Islama amma yake mugunta, bayan sun idar ta mike da niyyar barin dakin Alhaji ya yi saurin rungumota jikinsa kan ta yi wani yunkurin har ya game bakinsa da nata ya fara bata muhimman sakonninsa wanda suka yi matukar tasiri ga Zainab. Tun bata maida masa martani har ta fara sosai suka dage don ganin sun faranta wa junansu don sun shiga duniyar ma'aurata, a wannan rana Alhaji ya shaida mata suna suka tara domin kuwa ni'imar da Zainab take da shi ba ko wacce mace ke da irinsa ba, har kuka sai da Alhaji ya yi bayan komai ya kafa ya rungume ta jikinsa yana kwarara mata addu'oi da albarka. Soyayya suke yi irin mai tsafta kuma abin so ga kowa, burinsu shi ne su faranta wa juna. Gaskiya kam ana shan soyayya don yanzu zuwa kofar gida wahala yake wa Alhaji shagwaɓar Zainab kadai zata sanya ya kasa fita sun yi kyau gwanin sha'awa fatarsu sai wani sheki take ga zallar hutu da fatar jikinsu ke nunawa.

A gurguje

       *Bayan wata biyu*
Sosai hankalin Zainab da Alhaji ya kwanta soyayya dai babu kama hannun yaro domin burinsu shi ne su faranta wa juna, tuni aka dawo da Fawzan haka kuma an daura auren Umma da Abba, shirin bikin Fatima ake da Usman ɗin Rano wanda suka hadu abin Zainab ikon Allah kuma suka daidaita. Sallama ya yi tare da shigewa falon, turus ya yi ganin Zainab kwance da alama bacci take, girgiza kai ya yi yana mamakin baccin da ta ke yi a yan kwanakin nan, har ya kusa zuwa inda take ya soma jiyo kauri a kici ai da sauri ya nufi kicin ɗin, gas ta fara kashewa ya sauke tukunyar da ta yi bakinkirin kasa, falo ya koma har a lokacin Zainab tana bacci zama ya yi tare da jawota jikinsa a hankali ya soma shafa fuskarta, buɗe ido ta yi tana faɗin "lah Abban Fawzan ka shigo?" "Eh na shigo kina bacci Momman Fawzan wannan baccin an ya na lafiya lau?" "Lafiya lau fa wallahi bacci ne idan ya kamani sai na yi ta..." Bata gama dore maganarta ba ta mik'e da sauri. Rikota Alhaji ya yi yana faɗin "ina za ki je?" "Abu na daura a kicin." "Ai sai dai ki yi hakuri domin ya kone, Allah ma ya kiyaye ne da ya kawo ni gidan, don Allah a bar daura girki tun abin ya zama haka zan rika shigowa da shi." Lumshe ido ta yi bata re da ta ce komai ba ta gyara kwanciya a jikin sa bacci ya kuma gaba da ita. Haka ya yi ta zama har ta farka tana farkawa ta ci abinci shi ma ba da yawa ba ya umurce ta da ta shirya su je asbiti, aiko suna zuwa bayan gwaje-gwaje da likita ya yi ya tabbatar da tana dauke da juna biyu.
     Farin ciki sosai suka yi tun suna asbiti suka fara sanar da mutane Daddy ya yi farin ciki haka su Umma, Mummy Kam a ranar ta baro Kano don duba Zainab, har Daddy da kansa ya zo don duba Zainab anan ne Zainab take rokonsa da ya mayar da Mummy. Murmushi Daddy ya yi ya ce zai duba, sannan ya yi masu sallama ya tafi, ba a jima ba Mummy ta iso ita ta ci gaba da kula da Zainab sosai Zee ta gamsu da soyayyar Mummy a gareta don ko motsi ta yi sai Mummy ta tambayeta me ke mata ciwo, a haka har ciki ya yi kwari yawan baccin nan ya ragu sai shegen cin abinci, tuni Daddy da Mummy suka daidaita har an mayar da auren, godiya sosai Mummy ta yi wa Zainab domin har ga Allah ta gaji da zaman gida sannan ya bi duk hanyar da zata bi don Daddy ya maidata Amma fir ya ki sai ta dalilin Zainab ga shi sun koma matsayin na ma'aurata, kwanci tashi har Allah yasa ta shiga watan haihuwa inda Allah ya sa ta sauka lafiya kuma ta haifa katon lafiyayyen danta namiji, kar ku so kuga farin ciki a wajen Zainab ranar suna Yaro ya ci sunan  *Ibrahim Khalil* , wato an mayar da sunan IK suna kiransa da Khalil, Alhaji da kansa ya zabawa ɗan sa sunan IK domin ya samu labarin Alhairin sa daga bakin Zainab, kuma har ga Allah ya so Allah ya ba IK damar cika burinsa amma da yake Zainab ba matarsa ba ce sai ga shi ya mutu ranar daura auren su.
      Cike da ZAINAB ke zaune tana shayar da Khalil Alhaji ne suka shigo shi da Fawzan, "sannu da k'ok'ari Momman Fawzan ko dai ta Khalil za a ce?" Murmushi ta yi ta ce "na duka dai amma a ce Momman Khalil BURINA ya fi daɗi." "An ki wayon sai dai na Fawzan don ba a sauyawa tuwo suna." Dariya suka yi gaba daya cikin farin ciki don hankalin su kwance "Allah ya jikan Ibrahim Khalil ya raya mana wannan Allah yasa ya yi halinsa." Amin Zainab ta amsa cikin jin dadi. Duk wanda ya ga wannan family sai ya matuk'ar burge shi, domin yadda suke gudanar da rayuwa cikin farin ciki da soyayyar juna. Muna Allah ya kara mana son mazon Allah s.a.w amin

*TAMMAT ALHAMDULILLAH*

Nan shi ne karshen wannan littafi Mai suna a sama ina godiya ga Allah da ya bani ikon rubutawa lafiya kuma na gama lafiya, Alhairin dake ciki Allah ya sada Mu da ita kuskuren da ke ciki Allah ya yafe mana, sai mun hadu a littafiina na gaba mai suna *KYAKYAWAR ALAK'A* Ni ce taku har kullum Zulayheart Rano, Momman Fawzan, Yar mutan Rano.

Chegaste ao fim dos capítulos publicados.

⏰ Última atualização: Jan 08, 2019 ⏰

Adiciona esta história à tua Biblioteca para receberes notificações de novos capítulos!

BURINA COMPLETEOnde as histórias ganham vida. Descobre agora