Page 14

1.9K 92 4
                                    

💞💞💞                    💞💞💞
                       *BURINA*
💞💞💞                     💞💞💞

   
                          ©
                        *Z&R*💞

*Dedicated to AYSHA ALIYU GARKUWA*

                        1⃣4⃣

Mummy ne zaune ita da Alhaji a falo suna hiransu mai dadi, gyara zama Alhaji ya yi cikin yanayin damuwa ya ce "Mummy wallahi ina tsoron kar hakkin yarinyar can ya kmamu." "Wani irin hakki?" Mummy ta yi saurin katse shi. "Mummy akan cikin dake jikinta, ko babu komai cikin jinina ne bai kamata mu walak'anta shi ba kuma..." Kasa k'arasa maganar ya yi saboda wata uwar harara da Mummy ta banka masa ta ce "Ina jinka ubana, ni zaka zauna kana jawowa hadisi? Lallai ma Alhaji anya ma dai baka fara son yarinyar can ba?" Bata jira amsar shi ba ta ci gaba "idan ma sonta kake sai dai ka mutu matukar ka kuma mata kallonta da sunan tausayi ko soyayya sai na saɓa maka."
      "Allah ya baki hak'uri Mummy." Tsaki kawai ta ja ta bar masa falon don ya bata mata rai. Girgiza kai Alhaji ya yi cikin takaici har ga Allah yanzu yana mugun tausayawa Zainab, sai dai dole ya bi umurnin Mummy, tun ranar bai kuma mata maganar Zainab ba haka bai kuma zuwa wajen Zainab ɗin ba.

Bangaren zainab ma tun bayan da haka ya hadasu da Mummy, babu wanda ya kuma zuwa mata akan maganar cikin, abu daya ta sani shi ne kila Mummy tana jira har ta haihu ne kafin ta zatar da hukunci kamar yadda ta fada, sai dai tana addu'a akan kada Allah ya ba Mummy ikon cutar da ita.
   Kamar yadda Mummy ta bata umarnin sanya hijab aiko haka aka yi, kullum cikin babban hijab, bangaren aiki ma babu wani sauki yin sa take ga ciwon baya da mara wanda suke addabar ta, komai cikin dauriya take babu wanda ya yasan da maganar cikin har zuwa yanzu, har Fatima bata san da shi ba duk da dai Mummy ta hanata shiga bangaren Zainab, amma aboye tana shiga sai dai basa dadewa, a haka har cikinta ya shiga watan haihuwa, takaicin ta daya bata saya komai ba dan gane da haihuwar ta rasa ya zata yi, kuma tana da kuɗi a hannunta sai dai babu wanda zata ba ya saya mata, shi yasa ta hak'ura ta fauwalawa Allah komai, yau ranar ta kama ranar juma'a ce tun asuba Zainab ke fama da ciwo amma a haka ta isa falon Mummy ta fara gyarawa kamar yadda ta saba, tana yi tana cije leɓe don ita kadai tasan yanayin da take ciki, da kyar ta iya kammala komai ta nufi bangaren ta, duk wannan abu da ake Mummy tana kula da ita kuma tasan haihuwa ce tazo, sai dai bata jin tana da imanin da zata tausaya mata cikin sauri ta kira layin Alhaji ta bashi umarni ya zo yanzu.
   Zainab kuwa a falo kafarta ta cije ta kasa motsi "Ya rabbi." Ta furta cikin wata irin murya. Gumi ke karyo mata ta dukkan gaɓoɓinta, cikin wannan hali da take addu'a kawai take Allah ya sassauta mata wannan azaba domin bata jin zata iya rayuwa, domin ji take mutuwa zata yi Allah dai ta ci gaba da ambato har ciwon ya ɗan lafa kaɗan, jikinta ne ya bata akwai wani cikin falon a razane ta ɗago kai, fes ta sauke su kan Fatima dake tsaye idonta na hawaye don ganin halin da Zainab ke ciki, murmushin karfin hali ta yi ta ce "Lafiya kuwa sis?" "Babu lafiya." Fatima ta bata amsa tana nufowa inda take.
   "Me ya sameki?" Zainab ta yi tambayar tana mamaki, duk da a halin ciwo take." "Abin da yasa ki shiga wannan halin nuna shi yasa ni." Kafin Zainab ta yi wata magana har Fatima ta ci gaba "Sis me yake damunki?" Lumshe ido ta yi cikin sabon ciwon da ya taso mata da kyar ta ce "Sis nakuda nake yi." Zaro ido Fatima ta yi ta ce "ban gane ba nakuda dama kina da ciki ne?" A hankali Zainab ta warware wa Fatima komai, gaba daya kuka suke. Cikin kuka ta ce "Amma Sis shi ne baki sanarwa da Daddy ba?" "Mummy ta hanani kuma ina tsoro." Kallo Zainab take cikin tausayawa ta ce Wannan wacce irin mugunta ne? An ya Mummy da Ya Alhaji suna da Imani kuwa?" "To uwar iyayi aike kina da imani ko? Tashi ki bar min nan tun banyi kasa kasa dake ba munafuka kawai, idan har naji wannan maganar wajen wani kin ji na rantse sai ranki ya ɓaci." Cikin zafi Mummy ke maganar. Jiki a sanyaye ta fita daga dakin zuciyarta fal tausayin Zainab.

Shi kam Alhaji bai ko tsaya jin mai Mummy ke fadawa Fatima ba, wajen Zainab ya isa hankali tashe musamman yadda yaga tana ta zufa da juyi. "Mummy please ki taimaka akaita asbiti." "Asbiti? Wa zai kaita asbiti?" "Mu zamu kaita Mummy kaɗa yar mutane ta mutu, Please and please Mummy." Cikin hawaye Alhaji ke rokon Mummy Wacce ko kallonsa bata yi ba har sai da ta ji ya yi shiru ta ce "Ka gama? To ai ba kira na yi ba don ka tausaya mata ba, kiranka na yi don ka rubuta mata takaddan saki." A firgice Alhaji ke kallon Mummy bakinsa har yana rawa ya ce "Saki wani irin saki Mummy?" "Sakin aure." "No! Bani iyawa Mummy ba zan saketa a wannan halin da take ba..."  "Kai! MUMMY ta daka masa tsawa ta ce "Wannan umurni ne bada shawara ba, don haka yanzu ba sai anjima ba." "Please Mum..." Marin da ta watsa masa ne ya sanya shi kasa k'arasa maganar. "Wallahi Abdullahi zan tsine maka matukar bakai abin da nasa ka ba." Zuwa lokacin tuni Zainab ta nemi ciwon da take ta rasa don ta daina tsoron Mummy ta koma mamaki, Muryar Alhaji ta ji yana magana cikin kuka da rawan baki ya furta *ZAINAB NI ABDULLAHI NA BAKI SAKI DAYA BISA UMURNIN MAHAIFIYATA* yana gama fadar haka ya bar falo idonsa yana tsiyayar da hawaye kamar dai ba namiji ba.
       Wani irin karfi ne ya zo wa Zainab har ta tashi ta tsaya da kafafunta, hijab din jikinta ta gyara bata ko waiwayi bedroom ba ta soma tafiya, ko kadan hawaye basu da niyyar fita daga idonta don wani tashin hankalin ya fi gaban hawaye. A haka ta fita get sai dai tana zuwa get din kamar an dawo da ciwon sabo, duk da haka ta daure tana tafiya idan ciwon ya motsa sai ta tsaya tafiya mai nisa ta yi don ko hango get din gidan su Alhaji bata yi, haka ta ci gaba da tafi duk wanda ya ganta sai ya tausaya mata a haka har ta kusa isa babban titi, da kyar ta kai a niyyarta ta tsallaka amma ina abin ya gagara don ta fita a hayyacinta, wani mai mota ne yazo wucewa daga gani sauri yake musamman yadda yake falla gudu a motar sam bai kula da wata halitta ba har sai da ya zo daf da ita wata wawiyar birki ya ja Allah ya taimaka bai sameta ba, don ya bigi wata mota ce dake  gabansa sai dai babu wani abu da ya samu motar, fita ya yi da niyyar zuwa ya ba mai motar hakuri idonsa ya sauka kanta har abada ba zai taba manta kamaninta ba, ko da wani irin canzawa ta yi, da sauri ya nufeta tabbas ita ɗin ce jikinsa ya dawo ta lokacin har ta fita hayyacinta idonta lumshewa suke *ZEE* ya furta da karfi. Jin muryar sa yasa ta buɗe ido ta kalleshi ta buɗe baki da niyyar yi masa magana  amma ina sai ma numfashinta ya soma daukewa, da sauri ya sureta sai cikin mota.

Ku yi hakuri don Allah wallahi da rashin typing akan lokaci, akwai aiyuka da yawa kuma jiki da jini dole wata ran mutum ya huta. Ina sonku fisibilillahi😍

*RANO*✍

BURINA COMPLETEWhere stories live. Discover now