Page 3

2.9K 157 1
                                    

💞💞💞              💞💞💞
                    *BURINA*
💞💞💞                    💞💞💞

                     ©
                 *Z&R*💞

*Dedicated to AYSHA ALIYU GARKUWA*

Wannan gaisuwa ce ga masu bibiyar littafin *BURINA* sosai nake godiya Allah ya barmu tare ina yinku irin sosai ɗin nan😍😍

              0⃣3⃣

Washe gari tunda karfe shida suka ɗauki hanya, ko break sai a mota suka sanya, Alhaji tunda ya ji fadan da Daddy ya yi masa, ai bai  fita sallar asuba ba sai da ya yi wanka ya shirya, bayan sun isar da sallah  suka kama hanya.

Tafiya sosai suka yi karfe goma da rabi suka sauka birnin Rano, kai tsaye family hause nasu suka nufa inda anan ake bikin, Alhaji karami da Daddy break suka fara kafin time ɗin ɗaurin auren, Mummy Fatima da Ammar kuwa tun a hanya suka yi.

Karfe sha daya aka daura auren, shi Alhaji dama da kyar ya tsaya a wajen, yana ganin an gama sai ya koma gida, bangaren Alhaji Abubakar ya shiga wato yayan Daddy, canne babu jama'a da yawa, bai kwanta ba sai zaman da ya yi yana kallo.

Ya Al'ameen ma yazo bikin shi da matarsa, ita dama Aunty Ameena can suka sameta tunda nan take zaune, suna ta hira Aunty Khadija ta ce

"Mummy wai ina Alhaji karami ne?" Matar Ya Al'ameen.

"Wannan miskilin kike tambaya?  Kema kinsa ba zaki gansa anan ba, don ba k'aunar jama'a yake ba." Aunty Ameen ta bata amsa.

"A'a karkusa wa Babana ido, yau Daddyn ku ya sa shi yin tafiyar asabu, don haka a barnin shi ya huta." Mummy ta faɗa tana daukar yarinyar  Aunty Ameena.

Dariya suka saki, Aunty Ameena ta ce

"Allah Mummy me like kara shagwaɓa yaron nan, sam bai san ya girma ba, kuma yaci a ce ya sama maki uwa zuwa yanzu."

"Bai isa aure ba, a barshi har zuwa time da zai kai auren,  jiya Daddyn ku ya gama maganar.

"Yawwa wallahi na ji dadin maganar Daddy domin nasan zai matsa har ayi. Hira suka ci gaba da yi abinsu cikin kwanciyar hankali.

Karfe huɗu Alhaji ya tashi, wanka ya yi ya canza kaya yaso tafiya gida, amma Daddy ya hana shi tafiya sam yau ɗaya har ya gaji da garin, fita ya yi ya shiga cikin gidan da kyar Mummy ta matsa masa ya ci abinci sannan ya mike

"Sai ina kuma Baban Mummy?

"Zan ɗan fita ne Mummy na gaji da zama."

"A dawo lafiya." Ta faɗa cikin sakin fuska.

"Allah yasa Mummyna." Ya amsa yana murmushi, sannan ya fita.

Motar da suka zo da ita ya dauka ya shiga gari, ya yi yawo sosai inda ya tsaya a filin makaranta don yaga suna buga ball, can nesa da mutane ya yi parking ya fito a  saman motar ya zauna yana kallonsu, domin Allah ya yi shi baya son shiga jama'a, yana wajen har karfe shida, sosai wasan ta ɗauki hankalinsa, kuma ya taba ma masu buga wasan.

Malam Suleiman ne da abokinsa Alhaji Ahmad wato Daddyn Alhaji karami, hira suke yi a kofar gidan Malam Suleiman irin ta abokan.

Allah ya yi Alhaji Ahmad da son jama'a, bai manta abokansa na garin ba, duk inda yazo sai ya je ya gaisa da su, yau ma haka ya kawowa Malam Suleiman ziyara

Zainab ce sanye cikin kayan makarantar su tazo wucewa, ganin Malam Suleiman yasa ta tsuguna tana gaida shi, domin wannan al'adar ta ce, cikin saki fuska ya amsa har yana tambayarta ya babanta, ita kuma ta amsa masa

"Yana lafiya lau." Daga haka ta wuce

Sosai Daddy ya yaba da hankalinta, har ya ji yana ma Alhaji kwaɗayi samunta Matsayin mata, don ya tabbata zai yi dace da mata ta kwarai.

Bai yi kwauron baki wajen tambayar Malam Suleiman ba

"Kai wannan yarinyar tana da nutsuwa."

"Ai yarinyar nan Zainab kam Alhamdulillah! Nutsuwa wajenta ba kaɗan ba."

"Yar wacece?"

"Yar gidan Malam Ali ce, tun tana karama Allah ya amshi ran mahaifiyarta.

"Ikon Allah, wannan Yar gidan Ali ce gaskiya ta girma babu laifi, da ba'ai mata miji ba da na yiwa Alhaji karami kamu don irin nutsuwarsu ɗaya.

"Bana jin an yi mata miji, amma zan tambayar maka zuwa anjima."

"To mai zai hana mu tafi  yanzu  don da zafi-zafi ake dukan karfe, gobe zan koma Abuja.

"Mu je kawai ." Malam Suleiman ya faɗa yana tashi tsaye, Aiko take suka nufi gidan Malam Ali, sun yi sa'a yana gida,   koda ya ji bukatunsu hankalinsa ya tashi, amma girman Malam Suleiman yasa shi amincewa

(Tofa! Babban magana wai dan sanda yaga gawar soja, anya an yi wa IK adalci?)

*****
Khalil ne tare da Babansa Malam Sa'idu, suke tattaunawa, zuwa can yasa hannu a aljihu ya ciro wasu kudi yana faɗin

"Yawwa Baba dama kuɗi ne na samu, shi ne nace mai zai hana akai kuɗin gaisuwa gidan su Zainab?"

Murmushi Baba ya yi irin tasu ta manya,

"Khalil banki taka ba, amma abin dubawa a nan shi ne, idan aka kai kuɗin gaisuwa sai yaushe za'a kai sadaki, kasan Ni dai ba wani karfi ne da ni ba, kuma bani da hanyar samun wasu kuɗi, to bama wannan ba, kasan dai ko dakin da zaka zauna babu a gidan nan." Malam Sa'idu ya yi maganar yana kallon idon IK, domin bai lura da kuɗin da ya ciro ba.

Sosa keya ya yi ya ce

"Dama ai kuɗin gaisuwar kawai za'a kai, shima wani yayan abokina ya bani, ya yi min alkawarin gobe za'a tafi damu Abuja domin a yi mana gwajin kwallon, idan Allah yasa na haye, satin sama zamu tafi Ingila ka ga ma kuɗin." Ya yi maganar yana mik'a masa.

Amsa Malam Sa'idu ya yi yana juya kuɗin tare da mamakin yawansu

"Dubu ashirin da biyar ne, sai kuyi amfani da dubu goma sha biyar, sai akai dubu goma kuɗin gaisuwar."

"Lallai wannan mutumin yana da kirki sosai, Allah ya saka masa da Alhairi kai kuma Ubangiji ya baka nasara, in sha Allah Khalil zaka yi nasara a kan wannan burinaka, domin kai yaro ne na gari mai kyautatawa iyayensa Allah ya maka albarka."

"Amin." Ya amsa cike da farin ciki, sosai yake jin dadin yadda iyayensa suka ba shi goyon bayan akan yadda yake buga ball. Malam Sa'idu ya tsinka masa tunaninsa.

"Amshi wannan sai ka yi amfani da su, domin bai kamata ka zauna baka da ko kwabo ba." Malam Sa'idu ya yi maganar yana mik'a masa dubu biyar.

"A'a Baba ka barsu kawai."

"Amsa dai."

Hannu yasa ya amsa don baya son musu da mahaifinsa, cikin farin ciki ya bar mahaifinsa, kai tsaye gidansu Zee ya wuce domin burinsa ya bata wannan daddaɗar albishir...

     *RANO* ✍🏻

BURINA COMPLETEWhere stories live. Discover now