Page 13

2K 104 0
                                    

💞💞💞                    💞💞💞
                       *BURINA*
💞💞💞                     💞💞💞

                          ©
                        *Z&R*💞

*Dedicated to AYSHA ALIYU GARKUWA*
                    
*Na gode sosai da addu'oin ku, anyi biki lafiya kuma an gama lafiya, tuni amarya ta tare gidanta na gode kwarai*😘😘

*Wannan sadaukarwa ne ga dukkan masoya wannan buk ɗin, ina jin dadin yadda kuke nuna soyayyar ku a gareshi😍*

_*Garkuwa Uwar ɗakin barebari, ga gaisuwa da fatan Alhairi a gareki ba sai na faɗa maki son da RANO TA HANNUN HAGGU KE YIN KI BA, SOYAYYA CE IRIN WACCE BATA FADUWA, Allah dai ya bar kauna*_

              1⃣3⃣

"Ciki Zainab!" Alhaji ya yi maganar cike da mamaki yana kai hannunsa ga cikinta wanda ya fito. Ko kafin Zainab ta yi wani yunkurin sai jin saukar zazzafan mari ta yi wanda ya yi sanadin daukewar numfashinta na mintina uku, a kausashe ta ji muryar Alhaji yana faɗin
   "Ban san baki da mutunci ba sai yau, wato ke cikin ne kinsan kina dashi amma kika ki sanar min har sai yanzu? To bari ki ji ke ɗin nan baki isa kirabani da Mummyna ba tun wuri kisan yadda zaki yi da cikinki, domin bana kaunarsa." A zafafe ya gama maganar yana hankade ta.
    Wani irin kuka Zainab ta fashe da shi, domin cikin iri-iren tashin hankalin da ta gani babu wanda ya kai wannan firgita ta, bata taɓa tunanin irin wannan hukuncin daga Alhaji ba don tana da yakinin yasan cikinsa ne ba zai taɓa gudunsa ba, amma ga shi da bakinsa ya futar mata kalma mafi muni akan cikin, tabbas tasan wannan nafila ne akan wanda Mummy zata yi mata matuk'ar tasan da shi sai ya salwanta, wani sabon kuka ta fashe da shi, ikon Allah kawai ya kaita bedroom ɗinta akan gado ta zube tana ci gaba da kukanta.

Shi kam Alhaji toilet ya shiga ransa a matukar ɓace, da farin ciki ya dawo garin amma wannan abin da ya gani ya masifar tashin hankalinsa, a gaggauce ya gama wankan shiryawa ya yi cikin kananun kaya ya nufi bangaren Mummy, Babu kowa a falon don haka sai ya wuce bedroom ɗinta, sallama ya kamar baya son yin maganar. MUMMY fake zaune a bakin gado da waya a hannunta ga dukkan alamu waya ta gama amsawa ta dubi Alhaji cikin kulawa bayan ta amsa sallamar sa ta ce
    "Babana lafiya na ganka a wannan yanayin? Bayan yanzu babu jimawa ka fita da zallar farin ciki?" Mummy ta dire maganar tana ci gaba da kallonsa.
    Shiru Alhaji ya yi yana tunanin ta yadda zai fara faɗawa Mummy maganar, da yasan zata tashi hankalinta, sam baya k'aunar abin da zai bata ran Mummyn sa, sai kawai ya kuma kasa da kai yana jan yatsun hannunsa, shirun ya yi yawa a kalla ya yi minti goma bai ce komai ba, ran Mummy ya baci sosai don haka sai ta ce "Tashi ka bani waje tunda baka yi min magana." Ta yi maganar tana nuna masa hanyar fita daga dakin.
    A jiyar zuciya ya sauke idonsa tam da kwalla ya bude baki da kyar ya ce
   "Mummy Zainab fa ciki ne da ita..." Da rawar murya yake maganar ko kafin ya gama har Mummy ta sauke masa wani lafiyayyen mari. Ta daura da fadin
   "What? Ciki ta ya haka ta faru? Mummy ta yi maganar cikin firgici da tashin hankali. Alhaji da ya ji shigar marin da Mummy ta yi masa don rabon da wani ya taba lafiyarsa har ya manta, sai yau da Mummy ta yi masa shi yasa ya firgita, gyara zama ya yi ya ce
     "Eh! MUMMY ni ne na shiga wani yanayi sai na tara da ita, amma ki yi hakuri wallahi na kasa kare kaina ne kuma bazan kuma irin wannan sakacin ba Please Mummy." Alhaji ya gama maganar da alamar yana nadamar abin. Take tausayin ɗan nata ya darsu a zuciyarta, ta ji sam bata kyauta masa ba da ta mareshi, tabbas tasan Alhaji yana matukar yi mata biyayya babu mamaki wannan shaidaniyar ce ta ribace shi har hakata faru, (hmmmm Allah Sarki wato ba ma Alhaji keda laifi ba, lallai Hajiya Asma'u son kanki ya yi yawa, Allah ya sa ki gane gaskiya.)

"Ki yi hakuri Mummy."  Ya yi maganar murya a sanyaye.
   "Na hak'ura, sai dai kamar yadda kace baka k'aunar cikin nima bana sonsa abin da za'a yi tashi mu je bangaren naku don na yiwa tufka hanci, bana son kowa yasan da cikin." Mummy ta kai karshen maganar tana mik'ewa.
   Kai tsaye bedroom suka nufa don basu ganta a falo ba, fuskar Mummy daure kamar wacce bata san wani abu shi dariya ba, hararar da ta watsawa Zainab shi ya yi sanadin da cikinta ya wani ya mutsa da sauri ta dafe cikin tana furta "wash! Mtsww! ta ja tsaki ta ce cikin masifa
     "Wato ciki gare ki shi ne kika ɓoye shi don kar mu gani ko? To yau ba sai gobe ba zan sanya likita ya zubar min da shi, domin ban shirya hada jini da ke ba." Tana maganar ne tana latsa waya, cewa Dr ɗin ta yi tana jiransa yanzun nan. Daga haka ta katse wayar.
     "Ke wakika sanarwa kina da ciki a gidan nan?" Tana dafe da cikin hawaye masu zafi suna fita daga idonta ta girgiza kai alamar babu kowa. "Gud." Mummy ta yi maganar cikin farin ciki domin zasu gama aikinsu babu wanda ya sani, babu dadewa Dr ya iso Alhaji ya yi masa jagora har falo, Mummy suka fito Zainab tana biye a bayanta. Gaisar da Mummy Dr ya yi, bayan ta gama amsawa ta faɗa masa abin da take so a yi. Da mamaki Dr ya ce "Hajiya zubar da ciki? Me yasa za'a zubar da shi?" Harara ta jefa masa ta ce "Kaga bafa tambaya na ce ka yi min ba don haka ka kula, gata nan bana son cikin ya kuma kwana." To Dr ya amsa yana mai kallon Zainab wacce ta kuma tsurewa tana mai karanta duk wani addu'a da ta sani, a nutse yake kallonta daga bisani kuma ya ce
   "Malama watan cikin jikinki nawa?" Domin dai Dr baya son zubar mata da cikinta. Murya na rawa ta ce "Watan sa bakwai." "Nima kallon da nake ma cikin kenan domin ga shi ya fito ras, zubar da shi zai iya janyo babban matsala." "Ban gane matsala ba?" Mummy ta yi saurin katse shi.
    "Eh! Tabbas wajen cire shi ana iya rasa su gaba daya, don haka nake baku shawara abar mata cikinta ta haifa." Mtsww! "An ya kuwa Dr kasan aikinka? Ta ya zaka ce ciki ba zai ciru ba ana iya rasa su duka... "To wani shegen ya ce ma muna da buk'atar rayuwar ta? Idan zaka min aiki ka yi ko nawa kake so zan baka." Mummy ta yi saurin katse shi "No! Hajiya wannan aikin ba zan iya shi ba sai dai ku nemi wani." Yana gama fadar haka ya fice, zuciyarsa cike da tsoro yana mamakin halin irin na Hajiya Asma'u. Sororo Mummy ta bishi da ido, shi dama Alhaji kwanciya ya yi bai wani san yadda suka yi ba, don bacci ya fara daukarsa a kasalance ya ce "MUMMY ki bi komai a hankali." Daga haka ya koma baccinsa. Zainab kuwa sansanyar ajiyar zuciya ta sauke tana hamdala ga Allah da ya kare ta daga sharrin Mummy.
    "Ni Dr ya walak'anta zan dau mataki akan sa zan nuna masa bani da mutunci?" Sai kuma ta koma kan Zainab "To bari ki ji wallahi matukar kika bari wani yasan da cikin nan wallahi sai kin gane kuranki ciki kuwa har da Fatima ki rufawa kanki asiri karki bari asan da shi, daga yanzu zuwa lokacin da zan san yadda zan yi dake." Fuuu ta fita daga daki tana uban huci

Shiru Zainab ta yi amma hawaye basu daina zuba daga idonta ba a haka ta ja kafarta zuwa bedroom tana ci gaba da addu'a akan Allah ya kare ta daga sharrin Mummy.

     *RANO*✍

BURINA COMPLETEWhere stories live. Discover now