page 6

34 4 0
                                    

Friday,

8:00pm

Wushe-wushe night.

Compound din gidan General mahfuz ya cika ya tumbatsa da jamaa kala kala tun daga maza da mata, yara da manya.  Hasken fitulu ya dalle ko ina da ko ina na da tsakar gidan duk girmansa , ya hade ya gama haduwa cikin decorations na wushe wushe din Hanan M.Jajere. 
       Amarya hanan tare da mijinta kamal sun shigo tare da Rakiyar kannenta da cousins dinta,shima angon tare da rakiyar Abokansa yayin da kidan Gangaa Kura daya ke tashi ta cikin speakers din,  Dangin mahaifiyarta suna dauke da wani tray dan gabatar da Aladarsu ta wushe wushe din, sun fara komai gwanin ban shaawa har akazo gabar da aka bukaci mahaifiyar amarya dan ta shafa mata wani abu mai kama da lalle, MC ta bukaci hajiya Gaji ta taso dan ta gabatar da wannan aladar amma Gaji ta nuna kunya da kara tace ta wakilta Umma zulai tayi hakan, MC ta cigaba da kiran Umma Zulai ta cikin mike amma babu ita babu labarin ya.

       Muna zaune akan chairs dake zagaye da wani round table nida ikram, munirah da wata cousin dinsu ikram Mai suna Yasmin, munyi kyau sosai cikin kaya na Aladar da ake sawa a ranar wushe wushe, pictures muke tayi da wayar yasmin gwanin ban shaawa , munata shaawar waya dan kaidar Abba ce baa riqe waya agidan sai angama secondary school,

"Omg, Afy I can't wait to have my own phonneee"

Fadin ikram bayan munyi wani hoto mai dan karen kyau, karban wayar nayi ina dubawa ina kallon Kai na kamar bani na, ganin yanda nayi kyau bayan kwalli da lipgloss kadai na shafa ina ga gobe munyi makeup Din dinner,

"Nima wlhy Iky, dubi kowa da wayarsa anan bandamu"

Na fada ina pouting lips dina cikin shagwaba. Kafin mu kara cewa komai Anty Gumsu tazo ta wajen ikram tace

" ikram maza kuje ku kira mana Umma Zulai tazo ta dan Allah, da tana zaune anan tashi tayi"

Ikram ta miqe sannna tace wa munirah,

"Muje please"

"Tab wlh bazani ba, ina shiga sai an samu wanda zai aikeka yin wani abun, kuje da Afy."

Munira ta fada tana gujewa shiga part dinsu dan dama bawai a saran mahaifiyarta take shigewa shaanin bikin ba, ikram ta dubeni da ido tun kafin tayi magana ma na miqe dan rakata sashen da nafi shekara ban sa kafata acikinsa ba,  aiken Abba ko yakumbo ne kadai yake kaini wajen ta, muna cikin tafiya muna ratsawa ta cikin mutane saiga Rais yazo,

"Yauwa ikram kizo inji ya hanan , tace kizo yanzu fa "

Rais ya fada hannunsa rike da kaya niki niki na souvenirs ,yana fada ya juya cikin Sauri da alama jiransa akeyi,  ikram ta juyo Tamin kallo mai cike da gajiya,

"Bakomai jeki kiran ya hanan Din, bari ni na kira umman"

Na fadawa iky yayin da hannuna ya murda handle din falon umman, na turo kofar na shiga bakina dauke da siririyar sallama da ba lallai anji ba, babu kowa a falon sai tarin plates da robobin lemo,  na taka na dan shiga kadan inajin gabana yana faduwa,  bude baki nayi zan yi sallama da karfi naji an fito daga kofar corridor....gabana ya tsananta bugu sosai inajin bacin rai with the sight of her, sanye take da atamfar ankon irin namu amma sam ban ganta a filin taron ba,

"Afifah"?

Ruman ta furta da mamakin ganin ta, ta dade rabon ta da yarinyar....ta kara girma sosai.

"Ruman"

Na bata amsa itama, ban san dalili ba amma sai muka tsinci kanmu da kallon kallon, kowaccen mu da abunda ke kai kawo a zuciyarta game da yar uwarta, amma whats the nuisance feeling?

"Ya akayi?"

Muryar Umma zulai ta ratsa kunnuwanmu ta dawo damu dga tunanin da muka tafi, juyowa nayi gareta na fada mata sakon daya kawoni na fice, harara Umma zulai ta bi afifa dashi kamar ta bita ta shaqo kanta.

AFIFAHजहाँ कहानियाँ रहती हैं। अभी खोजें