page 23

34 7 0
                                    

You wrap your name tight around my ribs and keep me safe.I was born for you.
                                         ~Alire

Washegari ranar Asabar da hantsi tawagar gidan mai martaba sukazo dan tafiya da Amaryarsu zuwa masaukin da masarautar yobe ta tanadar musu dan tsare Gimbiya har zuwa lokacin da zaa kaita dakinta,  Munirah tasha kuka sosai ita da Ikram lokacin da akazo tafiya da ita a cikin wata luntsumemiyar mota, nice na zama mai basu hakuri da lallashi sabida an tabbatar mana da duk lokacin da mukeso muna iya zuwa kai mata ziyara, wata Kanwa a wajen Yakumbo mai suna kaka Danejo tazo daga Jajere a matsayin wanda zata zauna tare da munirah daga bangaren dangin ta, Wannan zabin Umma Zulai ba taso shi ba sam dan har ta zabo wata daga cikin yan uwanta a kano amma yakumbo tace sam bata yarda ba, kaka danejo ce zataje.
         A daren ranar duk da ba tare muke kwana ba amma nida ikram da Rais duk jikinmu a sanyaye yake ainun ,tunda muka taso koda yaushe muna tare koda ziyars zaaje wani gidan toh tare ake zuwa, yau gashi auren ba zata ya rabamu da Munirah, we weren't mentally ready for the separation ba kamar nida ikram ba munsan ga lokacin barin mu gidan kuma akwai sauran lokaci mai dan tsawo da zamuyi preparing minds dinmu.
         Kwana biyu tsakani da tafiyar munirah mukaje tambayar Abba akan munaso muje can Amma sai Abba yaki, yayi wuri da yawa su fara ziryan nan kuma dama can shi ba mai son fita bane, Hakuri ya basu yace ba yanzu ba sai an kwana biyu ,ya kuma shawarce mu da mu karbi reality, dan rabuwar dole ce watarana gamu baki daya, toh da aka ki bari muje sai abun ya dawo kan waya, ko yaushe muna video call da voice call musamman ita munirah da bata aikin sisi balle na kwabo, har gara mu muna tashi muyi ayyukan gabanmu ga school da zamu koma wannan satin. Haka zamuzo mu tarar da missed calls dinta rututu a waya sai ta samu daya daga cikinmu zata ji dadi .
         A video call din da muke da munirah ba karamin dadi nakeji ba ganin irin daular da take ciki a masaukinta, Ga hadimai dake shigowa duk bayan yan mintuna suna tambayar ta ko akwai abunda takeso,  kamar yanzu ina kan gado muna waya da ita naji muryar wata mata ta shigo ta ce

" Ranki ya dade ,zamu iya Fara wa?"

Munira ta bata amsa da

" Ki jirani daga parlor zan kiraki"

"Angama ranki ya dade"

Matar ta amsa,

" Afy kullum sai anzo an dirje min jiki da wasu abubuwa masu kamshi, kuma ba shi kadai ba sai ace sai na zauna kan wani abu kamar rushi yayita gasa min mazaunai"

Munirah ta fada cikin kagara kamar zatayi kuka, dariya na kyalkyale da ita sannan nace

" Amarya kinsha kamshi, ke dalla gyara ki akeyi"

" wallahi mura nakeyi ma sabida karfin turaruka, ke baki ma sani ba sai kaka danejo ta damo wasu abubuwa marasa dadi nake shiga uku ma, anjima kafin na kwanta zakiga tazo tasani agaba....yanzu tsaya ma dai, wai yaushe zakuzo?"

Munira ta fada bayan ta tashi daga kwancen da take akan katon gadon tana kokarim zuge zip dinta danta daura towel kafin masu gyaran jikin su shigo,

" Abba ne ya hana mu zuwa Munee, amma Monday zamu koma school ko daga nan sai muce baba Musa ya kawo mu "

Na bata amsa dan taji dadi duk da nasan baba musa bazai taba kaimu wani waje ba tare da izinin Abba ba, tundaga lokacin da abunda ya faru dani ko ruwa aka aiki baba musa ya siyo kaffa kaffa yake dasu. Munirah taji rashin dadi ainun sosai data tuna ita yanzu school din ta yasha ruwa kenan,

" yanzu ni da school saidai a labari kenan Afifah"?

" ko daya, ki gwada mishi maganar wata rana zai iya maida ke.....wait munee, yana zuwa?"

Na bata amsa, Munirah ta jinjina kai dan bataga alamar mutanen zasu bari ta shiga school ba, yanda ake mata kamar yau aka haifeta.

" ranar da mukazo naji muryarshi, amma bai shigo dakin da nake ba,toh tun ranar ma ban sake jinshi ba....but he do send a message ta waya lokaci zuwa lokaci"

AFIFAHUnde poveștirile trăiesc. Descoperă acum