page 21

29 5 0
                                    

****

" munee, ke da iky kunfison Always ko?"

Na fada a lokacin ina ciro pads daga jikin carbinets din store din, shirun danaji ne yasa ni waigawa na dan dubi Munirah dake gefena, sam bata ji ni ba hankalinta yana wani wajen ,saida na dan tabota sannan tace

" na'am ,me kika ce?"

" Cewa nayi kunfison Always ko? "
Na kara maimaita mata,

" Yeah, shi....amma kadan ma zaki dauka "

Munira ta bata amsa still hankalinta bawai yana kan shopping din da muke bane, na cirar musu Always din nikuma na dau molped sabida nafi sonshi, bai cika karar leda ba unlike Always, idan ina tafiya ko chanja pad a toilet sai naji kamar kowa yanajin sound din.....very uncomfortable!
         Cigaba da shopping dinmu mukayi kalakala kamar yadda muka saba duk karshen wata idan Abba ya bamu kudi, wani sain Ikram da ni muke zuwa, wani sain nida munirah wani sain ma su kadai suke zuwa ko da yaya sajidah. Muna list dinmu na " things -to -buy" na duk abubuwan bukatar mu na yau da kullum, duk wani abu da diya mace zata bukata tun daga kan toiletries zuwa ga kayan sawa abba ne ya ke bamu kudin saya ,  daidai da kayan zaki na kwadayin mata acikin kudin muke sayo isassu yanda zai ishemu, koda ya kare muna da damar sake zuwa tuntubarshi ya sake bamu batare da gajiyawa ba.
        Hakan na daga cikin dalilin dayasa muka kasance yan gata sosai kuma babu wani burga ko kudi da saurayi zaizo mana dashi ya rinjaye mu ko sa mana kwadayin Abun hannunshi, Allah yasani daga ni har Iky da muke da samari we don't feel entitled to thier money ko kadan, tunanin wai sune zasu dinga bamu kudin kashewa ko siyayya bai taba zo mana rai ba......dalili shine Mahaifinmu jajirtacce ne kuma ya tsaya akanmu yanda baa tunani.
        Ko katin waya da Yaya Aliyu yake loda min a wayata da yan kyauttukan da ba a rasa ba ji nakeyi kamar na aikata sabo idan ya ce min mai delivery yana waje na fita na karbi sako, dan babu yanda na iya ne amma I don't feel is right hakan, wani sain har fushi yakeyi Idan nace he doesnt have to do that, Yaya Aliyu sai yace he has been doing things for us tun muna yara kuma yanayi ne sabida mu kannensa ne badan yana soyayya dani ba.
          Bracelet din da Yaya Massa ya bani na nunawa Yakumbo a ranar daya bani kuma tace na ajiye a cikin akwati, bamu san wata iri bace ko adadin kudinta amma yanda take sheqi daga gani duwatsun masu daraja ne, na bude drawer ta nasa acan kasan kaya sabida nasan dole sai na mayar mishi da abunshi wata rana , a raina ko kankani banajin zan iya barin Yaya Aliyu na auri Massa, duk da fushin dana keyi dashi a ranar da zai tafi amma tuni muka shirya bayan yasha kirana da Messages kala kala yana bani hakuri, na hakura kuma na manta komai tunda na gano harda lefi na aciki tunda ni nakai kaina har dakin training dinsa.
      
        Toh A mota bayan mun fito daga shopping din mun loda kayan mun shiga baba musa ya tashi motar muka bar harabar store din, ina Lura da Munirah yanda ta zama wata shiru shiru kwana biyu, kwana biyun nan ma bana ganinta ko dazu da zamu fito ma sai dana kirata a waya sannan ta fito, she's looking so disturbed and bothered.
       Dole akwai abunda yake damunta, Munirah tana da zurfin ciki haka take tun Muna kananu ba kamar ikram ba, ikram bata da boye damuwa sam dan if she shared it with some one shine ma zata fi jin sauki a ranta. Bansani ba watakila soyayya Munirah ta fara shiyasa take shiga damuwa kwana biyun nan, zanso nasan matsalarta amma im 90% sure bazata fada ba. Hannuna na dora akan nata lokacin da baba musa ya shiga da motar cikin gida yayi parking a lot. Ba tare data kalleni ba itama ta Dora daya hannun nata akan nawa ta danyi tapping dinshi tace,

" I'm alright afy, karki damu"

Ta fada dan tasan Afifah ta gane tana cikin damuwa kuma tambayr da zata mata kenan,

" no you are not! Ya akayi kikasan tambayarki zanyi If you are okay or not? Kinsan you are not alright din kenan"

Na bata amsa lokacin muna zaune acikin motar muna sorting out kayyakin kowa, na dibarwa Ikram da Yaya Hanan nata tunda Abba ya Kara kudi yace duk abunda zamu saya mu saya da ita tunda tana gidan, munira tana daukar musu nasu itada sajeeda ,nima na dauki abubuwna dana siya da na Yakumbo,

AFIFAHWhere stories live. Discover now