page 16

31 3 0
                                    

10am,Friday

" Yanzu tsakani da Allah innata bazaki je lallen nan ba? "

Yakumbo dake zaune akan sallaya ta idar da sallar walha da misalin karfe 10 na safe ta fadi tana kallon Afifah dake kallon maimaicin wani film hankalinta kwance tana shan oats acikin wani bowl,

" yakumbo nifa ba wani lallen da zanyi, gidan radio nan ma zan tashi na tafi na ma makara"

Na fada ina shan oats dina, tun jiya yakumbo take mita akan sai naje nayi lalle sabida zuwan da naji sunayi na Massa a yau, tun kwana biyu da suka wuce aketa shirye shirye a bangaren yakumbo duk dan sabida zuwan yarima Massa, ko kadan ban dora akai ba balle ya dameni shiyasa ban ma fadawa Yaya Aliyu ba dake ta shirye shiryen zuwa gida shi ma. I feel there's no need to tell him sabida a soyayyar yaya Aliyu babu gudu babu ja da baya, ina jiran Massa yazo na fada mishi ni inada wanda nakeso yayi hakuri.
         Shiryen shiryen abinci da abunsha kala kala yakumbo dasu baba Audi suke tayi sabida babban bakon, yakumbo tasani agaba sai naje lalle ko kuma akira min mai lallen tazo gida tayi min duk naqiya, nayi sati biyu da fara zuwa gidan radio inda nakeyin Attachment dina kuma ina matukar son wajen dan ina koyon aiki sosai, yau jumaa Ina zuwa wajen kuma shirin tafiya nakeyi abuna na toshe kunnuwana daga mitar yakumbo.
          Ina tsaye adakin ina kokarin daura niqabi na najiyo muryar ikram tun daga kofa tana kwala min kira,

"Ranki ya dade Gimbiya Afy, "

" a'ahh me Zan gani haka? Wai fita zakiyi? Nifa zuwa nayi naji me zamu shiryawa Prince ta bangaren mu....yakumbo kinga fita zatayi wai"

Yakumbo tayi wuf tashigo dakin suka hada baki da Iky sukai ta fada akan ina shirin wulaqanta bako, bakon da kaf garin yobe da zagaye babu yashi.  Ko ci kanku ban ce musu ba nacigaba da shiri na na suri bag back dita na rataya

" Yakumbo sai na dawo, yau bazamu dade ma ana saukowa masallaci zan taho, Daga nan sai muga dame yarimanku yazo dashi ko?"

Na furta ina dariyar yanda su iky suketa tada jijiyoyin wuya, ban kai ga fita ba sai shigowar yaya Hanan mukaji mukai mata sannu da zuwa muka gaisheta ta amsa babu yabo Babu fallasa, ta wuce wajen yakumbo suka gaisa itama, yakumbo tace

" Ashe kina tafe Aisha, toh yaya maigidan?"

Yakumbo ta tambaya cikin kulawa, taga alamun kamar da sauki acikin alamarin hanan din dan da kanta taje har gidansu wajen mahaifiyarshi Hajiya Rahi akan rashin kyautawar kamal din da ake rade radin yanayi duk da ita hanan da bakinta bata taba kawo kararsa ba.

"Ai kwana ma zanyi yakumbo, ya tafi Abuja dazu"

Hanan ta fada da jin dadi a muryarta, ita kanta tayi mamakin furucin kamal jiya da dare wai ta shirya zuwa gida tayi weekends sabida zai tafi Abuja, ko a mafarki bata taba mafarkin zai barta zuwa gida kwana ba dan zaiyi tafiya, duba da yasha zuwa garuruwa ya tafi ya barta agidan ita daya agidan. Bayan ya ajiyeta ya kuma bata dan kudi a hannunta koda zata bukaci wani abun, ta tuna yanda ya janyo ya jikinsa ya matse gam tare da fadin.

" idan na dawo ranar Monday da kaina zanzo na daukeki, kar kice zaki koma kiyi wani girki okay?"

Bankai ga fita ba saida yakumbo ta sanarwa yaya hanan akan nadage sai na fita bayan inada muhimmin bako, duk a kokarinsu na faranta ran yakumbo suka biye Mata aka dora min laifi, nikuma har ga Allah ban sa ba yin musu da yakumbo akan abubuwa ba amma wannan karon naji duk duniya banida bukata da ta wuce na fita naje gidan radio, kamar wani maganadisu yana ja na, nayi musu sallama na fita wajen sarkin mota wato baba musa ya kaini har kofar gidan radiyon, kamar ya sani a hanya yayi ta man hirar yaya Aliyu wai shima sunyi waya dashi yace zai dawo yau ko gobe, nayi farinciki a raina sosai inajin surprise yaya Aliyu yake son yayi min shiyasa yaki sanar Dani ranar dawowarshi.

AFIFAHWhere stories live. Discover now