page 22

34 5 0
                                    

A wannan daren Munirah a dakin yakumbo tayi bacci, baccin ya dauketa ne jim kadan bayan munyi magana da ita, dalili sabida ta samu ta fitar da abunda ke ranta. Naji lokacin da mai aikin Umma Zulai tazo wai ana kiran Munirah, amsar da yakumbo ta bata tasani murmusawa.

" kije kice tazo da zanin goyo ta dauketa"

A wannan daren na tashi karfe 3:30 nayi salloli da Adduar istikhara da duk wasu adduoi danake bukatar yiwa kowa, Ina zaune akan sallaya ina kallon yar uwata munira dake baccinta hankali kwance, Na daga hannu na roki Allah nace,

" Ya Allah, kai kadai kasan sirrin abunda ke cikin zuciyata a yanzu, ya Allah idan akwai alkairi tsakaninsu ka darsa kauna a zuqatansu"

Ko da muka tashi da safe Munirah was so energetic fiye da yanda take a kwanakin baya, muna breakfast tana ta walwala nikuma inata binta da ido..she's so cute! Ban taba jin shaawar Dark skin ba sai irinta munirah. Wata fata baka amma ba can ainun ba mai sheqi.....irin kalar fatar mutanen Ethiopia ko kasar Eritrea!

Inata juya tea dina inaso na mata maganar amma nakasa, na kalleta lokacin tasa plantain din a bakinta tana tauna tace

" laaa Afy yaune bikin Siyama ta ajinmu a poly, zaki rakani tunda gidansu abayan gidanmu yake? Dan Allah kice eh "

" munee, Zaki auri Massa?"

Na fada inajin tunda nazo duniya ban tambayar abu mai wahala kamar wannan ba. Naga lokacin da manyan idanunta suka bude da mamakin abunda na furta,

" you must be crazy Allah"

Munira ta fada,

" No, just think about it! Nasan bazai ki ba Allah. Kuma wallahi Munee kaf yobe da kewaye ba macen da zata kaiki saar miji...not even close!"

Na kuma fada, duk wannan abun munayi ne a hankali yanda ba wanda zaiji, only God knows how excited I feel about the idea of Massa da munirah....ban taba jin inaso abu ya tabbata ba kamar wannan. Munirah tayi fushi ta tashi ta fice batare da ta karasa cin abincin ba, tana tafiya tana jinjina hauka irin na Afifah , yama zaayi hakan ta kasance? Yarima Massa ba ita yace yanaso ba dan me zaace ita yanzu?
        Sai taji dama bata gayawa Afy abunda ke damunta ba tunda har take shirin sacrificing saurayinta for her, koda ta isa sashensu sai da tasha fada wajen ummansu akan ta kwana wajen yakumbo, bata kulata ba ta cigaba da harkokinta har ta shiga wanka. Wani abun tsoro daya sameta shine fuskar Yarima Massa dake ta kaikawo a kirjinta, Abunda ta jima da binnewa a ranta shine yakeson dawowa,
Zama tayi akan kujerar dake bandakin tana goge kwalla. Irin wahala da Azabar da tasha akan cire soyayyar Massa a ranta ita da Allah kadai suka sani, tasha wahala tasha wuya akan son maso wani!

        One sided love ko makiyinta bata mai fata yayi shiga wannan halin, ita kadai ta mutu ta dawo akan son Massa ba tare da kowa yasani ba, tun ranar da sukaje gidansu zasu tafi umrah ta soma sonshi , it was a nice and cute feeling at first amma abun ya zama kamar ciwo da tsananin azaba sabida son yakice shi aranta a ranar da manema auren Afifah sukazo nemawa Massan Aurenta, Ranar taci kuka ta godewa Allah kuma ta kudiri aniyar dena son Massan ko ta halin kaka.....abu na karshe da zataso tayi a duniya shine son namijin da sisters dinta sukeso, there's no way zata so wanda keson Afifah , gara mata mutuwarta da hakan ya faru balle ace har wani ya gane ma.
        Munirah ta tsunduma Addua da sadaka duk dan Allah yasa ta dena son Massan, Allah kuma ya fito mata da nata mijin itada sajeeda su huta da tsangwama da gorin da uwar da ta haifesu take musu, sometimes mantawa ma takeyi ko shekara 20 batayi ba amma gorin da Ummansu take mata kamar ta shekara 40 ne ba aure, she somehow became depressed duk dan akan tunanin maso wani da kuma pressure din Ummansu but she didn't stop praying , har Allah ya taimaketa ta manta da Tunanin Massa kuma ta dena jin sonshi.

Meyasa yanzu karanbanin Afifah Ke son dawo mata da tsohon ciwo sabo? Meyasa take neman tono mata abunda ta dade da binnewa kamar yadda ake binne mamaci? Tayi wankanta ta fito tana ta kokawa da abubuwa a kirjinta, ya zame mata dole ta hada kayanta ta koma gidan yayarsu Anty bilki, she should get Away from Afifah and her rubbish for sometime coz ita kadai ta San wahalar datasha akan Massa, idan ta tafi gidan Anty bilki zata dan manta idan ta shiga cikin Nieces and nephews dinta sabida gidan Anty Bilkin sunada yawa kuma anashan shafta.

AFIFAHWhere stories live. Discover now