page 3

35 4 0
                                    

No 6,
General M.jajere street
Federal Lowcost, GRA
Yobe state.

8:20pm

Bude kofar nayi bakina dauke da siririyar sallama na shiga falon fuskata dauke da murmushin ganin Abba, amsa sallamar yayi da ganina ya ajiye Newspaper din hannunshi,  cire takalma na nayi daga gefe na fara taka katoton Italian Carpet din dake shimfide a falon ya rufe ko ina da ko ina duk girman falon, parlor ne katon gaske mai cin saitin kujeru guda 2 dakuma dining area da bookshelves kato kamar library,  duk da sanyin gari daya fara sakamakon shiga watan December da akayi yau amma Abba bai kashe AC dinsa ba.
        Ina isa gabanshi na tsugunna na gaisheshi cikin girmamawar da duk wata diya takewa mahaifinta,  tambayar shi nayi yau inda ya shiga dan ban ganshi ba tun bayan dawowarmu daga lesson karfe 5 na yamma,

" naje wani meeting ne AFIFAH,ban jima da shigowa gidan ba"

General mahfuz ya furta yana duban diyarshi da kulawa cikin so da qauna,

"Yaya makarantar toh? Dafatan kuna maida hankali sosai,  yaushe ne zaku yi jamb din? "

" Lafiya lau Abbanmu, jamb din next month abba, waec ma haka"

Na fadawa Abban ina tsoron ya cigaba da tambayoyi akan jamb dinnan dan Allah yasani mu tuni mun jingina zancen nan agefe,  shagalin mu kawai mukesha agidan ga kuma bikin ya hanan da zaayi, maganar bikin ne yasa ni zuwa wajen Abban kamar yadda muka tsaro dasu iky azo a tambayi Abba kudin makeup, Ikram da sajida suna waje a bakin part din Abba suna jirana,

Kara lankwasa kafafuwana nayi na dubeshi na sauke murya na shagwabe nace,

"Abba bikin yaya Hanan, Abba munaso muyi makeup"

Murmushi yayi a zuci yace anzo wajen, dan yasan wannan zuwan daren da magana a bakin Afifa,duk da ita din ba Daga baya ba wajen zuwa dubashi idan taga shiru baije sashen mahaifiyarshi ba,  daace su ikram ne daga sunzo yasan toh tambayar kudi ne sun maida shi kamar ATM dinsu, 
Kallon kyakkyawar farar fuskarta yayi yace cikin raha

"Mene ne shi hakan? Kayan sawa ne? "

"Aa Abba kwalliya ce, ranar dinner zaayi mana fa"

Na bashi amsa ina ta zuba addua a zuciyata dan nasan su iky suna waje suma suna aiko da tasu adduar,

" Allah ya kaimu ranar,  amma ku dauko mai kwalliyar tazo nan tayi muku ko?"

Ya fada yana jin babu wani abu da ya'yanshi zasu nema awajenshi su rasa matukar bai sabawa sharia ba, yana kaunarsu equally tamkar numfashinsa....yana ganin yanda farinciki ya cika fuskar Afifa kamar ya musu wani albishir tana ta mishi godiya ta tashi da sauri dan ta sanarwa su Ikram, Abba yayi dariya dan tuni dama suna waje suna jiranta....yagane duk wani takunsu da suke a tunaninsu dabara sukeyi.

Na zura takalmana da sauri dan na je na sanarwa su iky yanda mukayi nasara, na murda handle din kofar kenan mukayi kicibis da Umma Zulai, tana sanye da wani katoton hijabi taci kwalliya sai zuba kamshi takeyi kamar me,
         Gabana ya fadi da ganin matar danake mugun tsoro da fargaba, wata halitta da tin budar idona agidan wani abu na mutuntawa ko rahama bai taba shiga tsakanina da ita ba, harara ta ke ta zabga min kamar idonta zai fado na matsa gefe ta shige tana jin tsanar yarinyar kamar zai halaka ta, ta tsani yarinyar nan ta tsani existence dinta since from day one!

Taso ta na falon dan taji mai suka tattauna da Abban su munirah amma ta makara,Allah kadai yasan wani munafurcin yakumbo ta aiko ta suka tsara mishi ,kuma tasan duk bazai wuce akan auren hanan ba dan kowa agidan dashi suke kafa hujja suna tatsarshi kamar saniya, kwafa tayi hassadar auren nacin ranta tare da fatan a fasa auren sai taga da me Gaji da ita hanan din zasu cigaba da musu fifika.  Da faraarta ta karasa wajen mijinta tana Mai wani sihirtaccen murmushi,
     Abba shikuma   So da kaunar matarshi yaji yana ratsa ko ina kamar yau ya soma ganinta, a rayuwa bashi da burin daya wuce yaga zulai akusa dashi ko yaushe sai yaji kamar anyi mai gafara, tsugunawa tayi har kasa ta gaisheshi sannan ta gabatar mishi da abincin dare, yanaci tana janshi da hirarraki masu dadi da sanyaya zuciyar maigida sai ka rantse yau kwananta ne, mafi yawan hirar ta yakumbo ce duk acikin salon kissar ta dan nuna mishi irin kular da take bata wanda a zahiri karya ce ziryan, rabanta da sashin yakumbon ma anfi kwana 7, Bayan Abba ya gama cin abincin ya nutsa Umma Zulai tayi gyaran murya tayi sannan tace

" yanzu da zan shigo naga yan matan naka a kofa Suna ta murna, hala kudi aka tambayeka"

Dariya Abba yayi irinta manya sannan ya goge bakinshi da tissue yace

" au su Afifa wai, kwalliya zasuyi da bikin hanan shine akazo akayi billing dina"

"Oh Allah, kaji min yaran nan,da baka biyesu ba ranka ya dade ..."

Ta bashi amsa tana dariya itama amma ranta haushi ne fal,saarsu daya harda Munira aciki da wallahi baza suyi kwalliyar ba,

"Ko me sukeso zanyi musu zulaiha, "

Abba ya bata amsa,  jinjina Kai tayi tana yanke shawarar ya zama dole itama diyarta tazo gidan ayi shagalin da ita Dan already tasa anyi mata dinkunan fitar bikin dama,

" hakane Abbansu, Allah de ya raya mana Su yayi musu Albarka, RUMAN ma zatazo wani satin....bata dai tsayarda ranar ba"

Umma zulai ta fada tana fatan yace zai bada kudin mota abawa Ruman din, ilai ko sai gashi ya hankada throw pillows ya ciro kudi ya ajiye mata agefe yace a aika mata da kudin mota , ta dauki kudin tana jin dadin alamarin,  ya zama tilas ga Abba ya kula da diyar da ta haifa agidan tsohon mijinta tunda a banza ma yace yaji yagani zai kula da diyar tsintuwa!

Bayan mun gama tsallen murnar mu anan katon compound din gidan tare da ikram, mungama hasko irin kyan da zamuyi ranar dinner dinnan, sanyi ne ya dameni nayi shirin tafiya sashen mu, mukayi sallama dasu nayi gaba ikram ta kwala min kira

" Afy kinyi maths assignment din Mr Bola? Kinga na manta banyi ba wallahi"

"Nayi kuma gaskiya bazaki kwafi nawa na, waya hana kiyi?"

Na bata amsa ina jinjina shiririta irinta ikram, rokona ta dinga yi akan Dan Allah na bata ta kwafa gobe a mota kafin mu isa school,

"Naji, amma zaki wanke min uniform gobe"

"Naji nayi biyayya Afy love,har guga ma"

Mukayi dariya tare dayiwa juna saida safe na wuce sashin mu nida yakumbo, da isata na tarar da tasu kungiyar cike a falon anata kallo ana shan fura , yakumbo ce da masu aikin gidan na kwana wato baba Audi sai sabirah, sai kuma wani yaro jikan baba Audi da yake gidan yana yan kananun aikace aikace,  hade rai nayi tamau inajin haushin wannan kallon daren da suke zuwa,kuma dama zasuyi kallon kadai da sauki amma sai an hada da hira da bin baasi akan duk wani scene da zaa nuno sai anyi sharhi akansa,

" uwata, zaki sha furar ne na zuba miki?

Yakumbo ta fada dan hade ran da Afifa tayi ba karamin tayar mata da hankali yayi ba,

" ko wanka zakiyi zaki fi jin dadin jikin?"

Ta kuma tambaya, sudai su baba Audi babu baka sai kunne dan inda sabo sun saba da ganin tabarar Afifa dakuma irin tarairayar da yakumbo take mata abun sai ka riqe baki,  haka Afifa ta tsallakesu ta wuce can wajen yakumbo ta kwanta ajikinta tare da rungumeta tsam tanajin duminta, 

" ni bacci nakeji yakumbo, muje mu kwanta"

Na fada dan son ganin wannan taron na su sabirah ya watse, abarni nida yakumbo na mu sakata mu wala, aiko ko rufe baki banyi ba yakumbo ta ce maza maza su tashi su san inda dare yayi musu zata rufe dakinta Afifah najin bacci,
         bayan sun fita na rufe mana kofa sannan muka nufi daki dan kwanciya bacci dama already kayan baccin ne ajikina tun dazu kafin naje wajen su ikram,  kwanciya nayi ajikin yakumbo inajin duminta , dumin uwa, dumin mahaifiya danake sha tun daga ranar da nayi wayo na tsinci Kaina agidan, ranar da bazan iya tunawa ba sam dan inada shekaru 2 kacal kamar yadda yakumbo tace min,  banida uwa a duniya sama da yakumbo sannan banida uba aduniya sama da General mahfuz jajere.
        Idona na lumshe ina hasashen kamannin mahaifiyata kamar yanda nasaba a kullum amma empty! Bansan ta ba, bansan sunanta ba......Saidai imaginations na brain amma I don't have a single picture of her in my memory, a kullum saide nayi hasashen kyakkyawar buzuwar mace mai Kama dani.

Shin mene ne ainihin sunana? Wace ce ni? Suwaye dangina? Wadannan wasu tambayoyine da ashekarata ta 18 banida amsar Su kuma banida mai banisu, inajin kuma har na mutu bazan san su ba, abunda Abba ya fada min kuma shima iya abunda yasani shine sunan mahaifina Youssoufa, sunan garin mu DIFFA dake a jamhuriyar Niger!

AFIFAHWhere stories live. Discover now