page 9

33 5 0
                                    

Sir kashim road,
Damaturu

1:10Am

Tana kwance akan doguwar kujerar dake falon ta lulluba da bargon data fito dashi daga daki, sata irinta bacci dakuma tsalawar da dare yayi shi yasa baccin ya dauke ta badan tana cikin kwanciyar hankalin dazatayi bacci ba, Tv falon a kashe take sai fanka dake gudu, shiru baa jin komai sai karar deep freezer dake bangaren dining area, ga kulolin Abinci da kuma plates data jera tun karfe 7pm na dare.

Karar bude gate dakuma haushin karensu ita tasa Hanan ta tashi i
firgigit, tanaji ya shigo da motar ya koma ya kulle gate sannan ta miqe ta nufi kofar ta murza key ta bude mai,

"Kamal, sai yanzu kamal? Ina kake tsayawa kwana biyu sai dayan dare zaka dawo gidan nan?"

Hanan ta fada cikin muryarta mai matukar sanyi kamar zatayi kuka,  tashin hankali karara a muryarta da fuskarta dan ita bata ganewa halin da kamal din yake bijirowa dashi kwana biyun nan, yau satinsu 3 da aure , sati 3 suna shan soyayya da amarci kamar babu gobe, sati uku ana darzar amarci dan ko fita masallaci bayayi, a wanann lokacin rashin fitarshi masallaci bawani abu take daukarshi ba tunda sunayi agida, shima itace zata lura lokaci yana kurewa ta ankarar dashi sai ya tashi suyi tare.
      A wannan lokacin ganin hakan takeyi duk a cikin soyayya dan ta Saba jin anacewa Angwaye ko fita basayi, a sati na biyu ne ya fara fita yayo dan cefene da siyayyan provision da duk abubuwan bukata bayan an dena kawo musu daga gidan iyayen kamal, mahaifin kamal shine tsohon mataimakin gwamnan da suka sauka wancan tenure.Hanan tayi tunanin zasu fita su je gaishe gaishen iyayenta da nashi amma ko kofar gate dinnan bata taba wucewa ba, babu inda take zuwa saidai ita ta danyi baki sama sama shima yawanci daga nata dangin ne banda nashi....a yanda ta lura dasu tun kafin auren mugayen yan raini ne ,wulaqanci da ji da kai a hakan ma wai dan nata uban ba talaka bane.
        Halin rashin sallah akan lokaci, yawon dare har ma Dana rana, raini, ,waya da yan Mata, fada da masifa babu gaira babu dalili sune kadan daga cikin sabbin halayen da kamal din ya bijiro dasu a satin su na 3 bayan aure, a kullum tana bashi uzuri tare da ba kanta laifi ko itace take mishi laifi sai ta zage damtse ta gyara amma ta lura sam hakan ba daga wajenta bane dan ko mai zatayiwa kamal din baya gani kuma baya appreciating.....she's been holding back coz she believe its too early ta fara suspecting matsala a aurenta but truly there is a problem! Amma menene matsalar? Daga ina matsalar take? Ina wannan soyayyar dake tsakaninta da kamal? Ina burika da alkawarruka da sukayiwa juna? Shikenan komai ya kare a sati 2? Dama haka auren yake?

      Tun ranar kai amarya bata kuma sa mahaifiyarta da mahaifinta a idonta ba saidai tayi waya ta gaishesu, ranar datayiwa ummansu complain akan kamal yaki bari tazo gida har fada umman tayi mata sosai ta kuma bata laifi ma na kan cewa mai yasa zata matsa saita zo gida , har tana mata misali da cewa su ada sai bayan wata shida da aure sannan yarinya take fara fita, Abbansu ma beign the busy person he is dan shi mostly ba zama a yoben yake ba toh bai taba maida rashin zuwanta gida wani abu ba, sau da dama saidai tayi musu text message shi da Yaya Aliyu da sauran yayyanta, Babbar yayarsu bilki ce ma take fushi akan rashin zuwan hanan din gidanta su gaisheta,
       Ita harga Allah kullen kamal agareta bai wani daga mata hankali sosai sabida inde rashin fita ne sun riga sun saba da hakan already tun tasowarsu, basa fita sam koda sun fitan ma ko yaushe azagaye suke da securities sojoji. Yawon daren da kamal yakeyi da rashin sanin addini shi yafi komai daga mata hankali a yan kwanakin nan, zuciyarta  cike take da fargaba kala kala kuma ta kasa samun karfin guiwar yi mishi bore akan fitar Daren,
        ako wace fitowar Rana tana farkawa with the hope that kamal zai dawo gida da wuri yau amma karfe biyun dare ko dayan daren nan dole sai ya kai.....haka zai dawo mata kamar makekke amma kuma ba maye yake tuburan ba, tare da warin wani abu shi ba taba ba shi ba gawayi ba, Abincin data girka ya zama waste dan ko kallonshi bazaiyi ba......kamar ma bata da wani amfani a rayuwar kamal saidai ya dawo cikin dare ya kwanta da ita ya moreta san ranshi dan a wannan fagen baya wasa kuma baya daga kafa Sam, kamar yanzu Bayan ya shigo tamishi tambayoyin nan bai amsa ta ba yana tsaye yana dan tangadi a cikin falon yanata lalubar aljihu wai mukullin mota yake nema,

AFIFAHWhere stories live. Discover now