page 36

57 5 2
                                    

I have died everyday waiting for you.....Darling don't be afraid, I have loved you for a thousand years.....and I will love you for a thousand more!
                                         ~Perry


7 days later.

5:00pm.

Kano.

Shigarsu cikin garin kanon ta wajen mariri ita ta sanya Simon dake tuqi ya Tsagaita gudun motar, tun da suka taso daga Yoben da misalin karfe 12 na rana Hilux din ke falfala uban gudu akan tituna tamkar zata tashi sama har yanzun da suka shigo gari, Aliyu da Simon ne kadai a tinted hilux baqa wuluk sai sheki takeyi.
         Hold up suka tarar a maririn da yake neman bata musu lokaci , kamar yanda akasan sojoji basa iya jurar go slow sai sun fito sunga meke faruwa kuma su nemi da a basu hanya da gaggawa su wuce,  tun dazu Simon yaso ya fita amma Aliyu ya hanashi ,ganin abun na neman wuce gona da iri yasa ya umurci Simon din daya fita ya duba, da sauri Simon ya fita ya isa ga yan karotan Kuma cikin dakikun da suka gaza 10 sai gashi an tsayar da daya hannun an basu suka wuce.
           Rana akeyi sosai a garin kanon , ranar ta fito ta tsala kai kace ba yammaci bane bayan laasar, ranar da yake tunanin jiya sun tarar a yobe ashe ba komai bace compared to ta kanon dabon, hakan na nuni da cewa damuna gab take da farawa. Duk da AC din dakeyi a motar bai hana yaji hannayenshi nata tsattsafo da gumi ba, gumin da hannunsa keyi bashida da alaka da zafin gari sam saidai irin dumbin tunanin da ke dankare a ransa, har yanzu baisani ba idan akan turbar daidai yake ba, har yanzu baisani ba idan zuwa kanon wajenta shawara ce mai kyau, har yanzu baisani ba idan abunda yake shirin yi daidai ne.....abunda yasani kawai shine bashida zabi.
          Jiya Asabar suka taso daga birnin tarayyar gaba dayansu da misalin karfe 7 na safe,jirginsu kuma ya sauka a Maiduguri, daganan Su Imrana da suka taho a day before suka daukesu a wannan hilux din zuwa Yoben, yaso su tsaya ta Shehuri su ga Muneera sai Afy tace ai duk suna yoben ita da ikram. Lokacin da sukaje gida sun tarar a hada wani kwarya kwaryan walima, abundai kamar family gathering duk jikokin gidan da wasu daga cikin cousins sun hallara, walimar da aka shirya tayi dadi sosai kuma anyi zumunci duk da Abba bayanan ya tafi Kasar india shida Umma Zulai zuwa medical Checkup amma a satin da zai shigo zasu dawo.
          Washegarin ranar da suka zo yobe ya tsara cewa dama zaije kano, saida ya gama baccin sa tas ya tashi ya shirya yar jakarsa da dik abubuwan da zai bukata sannan ya nufi sashen ummansa wajen karfe sha daya saura, yana shiga ya iske Afifa da ummansa harma da ikram da Hanan suna karyawa, Kinan yana hannun Umma Gaji ta gama mishi wanka tana kokarin goya kyakkyawan jikan nata, Afy tana ganin ya shigo ta gaisheshi cikin jin nauyin ummansa, tanaso ta zubo mishi abincin amma tana jin kunyar Umman , Umma gaji da kanta ta dubi Afy tace

" tashi ki zubawa mijinki abinci mana"

Sannan ta tashi ta hado masa dik abubuwan da tasan yanaso ta kawo mishi, kadan yaci yanayi yana duban agogo, ganin ya gama yasa tazo ta kwashe tray din gabanshi Takai kitchen, dawowarta kenan taji Aliyun yana fadi wa ummansa cewa zaije kano yanzu,

" Kano Kuma Haidar? Lafiya amma?"

Umma Gaji ta tambaya,

" Lafiya lau Umma, zani wani aiki ne"

Ya bata amsa shima yana ta kokarin karya hada ido da matarsa, aduniya bai taba jin nauyinta irin na yan kwanakin nan, yayi musu sallama bayan ya ajiye musu wasu yan kudi koda zasu bukata sanann ya fice, Afy ta bishi da kallo dik da tana son ta tashi ta rakashi koda zuwa wajen mota ne, amma sai taji batada karfin guiwa tunda bata san zaiyi tafiya ba ma, tsakaninta da mijinta babu tsananta binciken na sai taji abunda yake ciki ko mai zaiyi ako yaushe ba, amma tafiya zuwa wata kasa ko wani garin baya boye mata sam.....meyasa takejin kamar akwai abunda yake boye matan yanzu?

"Alhaji Allah ya saukeku lafiya, Allah ya rabaku da karfe lafiya" Alhaji asiya kwai"

Maganganun wasu yara masu bara da kuma tallah shi ya dawo dashi hayyacinsa daga tunanin daya tafi, sai a sannan ya lura suna gab da Kabuga inda zasu dauki hanya zuwa dorayin, Dashboard ya bude ya dauko dubu 3 sabbi fil ya sauke glass a hankali ya mikawa yaran sannan suka wuce, Yamma ta farayi sosai lokacin kuma inda Allah ya taimakeshi shine dama tun dazu d azahar ta riskesu a wani kauye ya tsaya ya gabatar da Sallar azahar da Laasar a hade tunda yasan laasar din zata riskeshi a hanya. A hankali motarsu ta cigaba da kurdawa tana bin hanyoyin da zai sadashi ga inda ya nufa.

AFIFAHDonde viven las historias. Descúbrelo ahora