Shimfida.

140 4 0
                                    

Assalam Alaykum.

Dafatan na sameku Lafiya? Alhamdulillah.

Ina mai sake gabatar muku da Alkalamin rubutu na a Karo na biyu, Littafi Mai suna

AFIFAH!
Labari ne na tsantar Soyayya, sanyanyar qauna, kiyayya, makirci, nadama , War of love....etc
kunsan yanayin rubutuna,kudai ku biyoni muje zuwa.

Ga kadan daga cikin labarin Afifa da Aliyu haidar

"Da zuciyarki da bindigar nan sune rayuwata,gara na kasheki da hannuna akan ki rayu da soyayyar wani"

Ya fada tare da saita bindigar adaidai saitin zuciyarta.

***************

2003

Diffa Town

Niger republic.

" Salamu Alaikum, gahwara dai! Mallam Youssoufa!! Gafararmu dai"

Muryar wani bafade dake ta kwala sallama sanye cikin kayansu na fadawa, daga gani hankalinsa a tashe yake yanata dube dube hannunsa rike da wata touch light, akalar rakuminsa na hannunsa ya kosa ya fadi sakon daya sa aka tasoshi tun safe.

Sai a sannan ya fara jiyo motsin bude kofar sannan malam Youssoufa ya fito sanye da babbar riga da rawaninsa irin na buzaye, Farin ba'abzine mai kyau da yalwar gemu sosai, Gaisawa sukayi da dan sakon a gurguce sannan dan sakon ya fadi sakonsa ya tafi, Malam Youssoufa ya koma cikin gidan jiki a sanyaye, ya tura kofar karamin falon ya shiga ya mayar ya rufe ta gam bayan ya tabbatar da duk wata sakata ta shiga, Aransa yana Allah wadai da wannan yanayi na rashin zaman lafiya d suka tsinci kansu dashi a diffa a cikin yan watannin nan.

" malam, waye ne a kofar?

Matarshi yarinya yar shekara 25 ta tambaya itama da damuwa a fuskarta, autarta yar shekara 2 na kan cinyarta tana kokarin sake mata wasu kayan dan kwanciya bacci, malam youssoufa bai ce mata komai ba har saida ya zauna sukaci gaba da shan shayinsu shida yayansa maza guda 3, babban yaran acikinsu baifi shekara 12 ba.

Saida yaran suka tafi daki dan kwanciya bacci bayan Shattou ta tofe musu jiki da adduoi, ta kuma juyowa ga mijinta da tambayar da tayi mishi da farko dazun, malam Youssoufa ya dubeta da damuwa a fuskarsa sannan yace,

"Bari kedai shatou, abun babu dadinji....sako ne daga yayana Issa akan yana bukatar komawarmu can cikin gari (Diffa) ya aiko sako akan mu tahi dan kubuta da rayukanmu da diyoyinmu, lamarin tsaron kara lalacewa yake, wai sun aiko sako zasu shigo nan yankin "

Shattou gabanta ya yanke ya fadi a take, ta kadu da jin hakan kuma a lokaci guda tayi farin ciki da sakon, gara su tattara su koma wajen mai martaba sarkin diffa kuma babban wa ga mijinta, daman malam dinne ya dage akan zamansa anan kauyen sabida taimakawa dayake da koyarwa a makarantar firamare, Malam youssoufa yanason koyarwa, shine yafi mai komai dadi a rayuwa,

" mu tahi kawai malam, hijira ta zama wajibbi hwa yanzu, Iyalin Abdulkadiri ma sun tahi agadez jiya, mu taimaka mu kubutar da diyoyin nan malam"!

Ta fada fatan ta malam din ya yarda da bukatarta, kyakkyawar diyarta dake jikinta mai Kama da ita da mahaifinta, kamar ta jinin abzinawa ya hadu ya bada wani sirkin kyau ga diyoyinsu, malam youssoufa yayi shiru ya dilmiya kogin tunani, da gaskiar shattou ya zama dole su ceci diyoyinsu, ya dubeta yace,

" bakomi shattou, jibi idan Allah ya kai rai sai mu wuce cikin gari, amma Allah da kun barni bawani abu da zai hwaru...."

"Miyasa sai jibbi malam, mu wuce a goben kawai"

AFIFAHWhere stories live. Discover now