page 11

27 3 0
                                    

Bornu emirate,
Shehuri

Maiduguri.

1:00pm,

Da misalin karfe 1 na rana muka iso fadar shehun borno ,amma kafin shigar mu ainihin cikin gidan iyalansa saida muka shafe tsawon minti 30 sannan muka iso masaukinmu bisa jagorancin wani bafade da jakadiya, mun sami tarba ta mutunci sosai dan ba karamin zumunci ne a tsakanin Abbanmu da mai martaba Ahmadu bukar ba,ga Kuma kasancewar Ummansu Ikram itama haifaffiya kuma cikakkiyar yar Borno. Kafin kace me an cika parlon da kayan ciye ciye da abunsha ganin idonmu, abinci kala kala na gida dana waje kamar munzo wani muhimmin shaani, mukaci mukasha sanann kowa ya samu waje dan hutawa, masu baccin rana irinsu ikram da munira sukayi bacci abunsu, nida yakumbo kuma mun de kwanta ne kawai amma bamuyi bacci ba, hira mukeyi da yakumbo tana ta bani tarihin abokantakar Abba da shehun borno Ina saurarenta har Anty bilki ta shigo dakinmu riqe da jaririnta dan wata 8 a hannu tace,

" wai wadannan bacci sukayi, so nake kuje mota ku duba min ko aciki na bar daya wayata, duk na duba ban ganta ba "

Tashi zaune nayi na janyo mayafi na peach na yafa akai da niyyar zuwa na duba mata duk da bansan takamaiman  hanyar da zata fitar Dani wajen ba, kafin mu shigo mun wuce ta corridors kala kala,

" Anty bari naje ni kadai basai an tashe su ba"

Na fadi hakan kenan sai ga wata kuyanga ta shigo ajiye mana wani katon tray, Anty Bilki ta hadani da ita muka fita ta kaini wajen da zai sadani da parking lot din bangaren, baba musa ya bude min katuwar sienna din na shiga na duba Mata wayar, kuma akayi saa naga wayar a kasan .
          A hanyar komawa ta ciki ne na bata na rasa hanyar da zata komar Dani masaukin mu, akwai wata hanya da tayi left da right wanda daya daga cikinsu ne zai kaini masaukin mu,  na rikice kuma Allah baisa na ci Karo da kowa ba balle ya fitar dani,kuma dabarar kiran yakumbo da wayar Anty bilki dake hannuna sam bata zo min, banida zabin daya wuce nayi trusting guts dina kawai nayi left, a wannan lokacin nayi tunanin hanyar daidai nabi dan tsarin ginin bashida banbanci da wancan, katuwar kofar falon mai kama da irin tamu nagani a gabana, banbancin wannann da wancan shine tamu akwai shoes dinmu da yawa a bakin kofar wannan kuma babu komai sai door mat mai laushi na silk.
            Domin na kara tabbatarwa kaina na bude kofar na saka fararen kafafuwana aciki, idona yayi tozali da wani hadadden falo Mai matukar kyau da tsaruwa , duk kyan masarautar dakuma haduwar masaukin mu sai naga shi ba komai bane compared to this.....so Royal!
Sanyin AC splits karara ya kankare falon dawani hadaddan oudy kamshi, I wanted to melt right away, zuciyata tana ingiza ni akan na rufe na fita dan tabbas nan kila falon mai martaba ne na shigo, yayin da wata zuciyar ke kara sani jin shaawar ganin mammallakin wannan waje, shigo da jikina nayi gaba daya amma ban yarda na rufe kofar ba koda incase Zan ci Karo dawani abun tsoratarwa ,

" Assalam Alaykum"

Na tsinci muryata da fada a hankali duk da im sure babu kowa, babu motsin kowa. A take kuma na fara jiyo motsin kofa daga can cikin wani corridor ta gefen dining area mai dauke da set of royal tables and consoles, tafiyar ta cigaba da kusantowa at the same time wani kamshi yana gauraye ilahirin falon, wata murya ke magana cikin wani hadadden turanci cikin fada fada,

" She's probably just exhausted,nothing more"

Muryarshi ta fada kuma babu zato babu tsammani idonsa ya sauka akan wata kyakkyawar halitta da tun dayake bai taba ganin beauty in its human form ba, she looks so unreal....Who's this princess? Wani abu mai kama da faduwar gaba yaji ya sameshi, kallon kallon sukeyi, ita nata idon na mishi kallon firgici da tsoro ,nashi kuma yana mata kallon wace ce ita? Har ta kai Aneesah nata magana ta cikin wayar cikin nadaddiyar harshen ta mai fidda American Accent.

" Will call you back"

Ya fada ba tare da jiran amsarta ba ya kashe wayarsa ya mayar cikin aljihun wandon kaftan dinsa yana neman karin bayani, ya kafe Afifah da ido yana neman karin bayani Daga gareta,
          Hannu na naji yayi gumi sosai har Nokia anty Bilki na shirin faduwa daga hannuna, kara damke handle din kofar nayi Ina son fita Amma kamar an dasa kafufuwana awajen,

AFIFAHWhere stories live. Discover now