Page 38

89 8 0
                                    

9:06pm.

Cikin hadadden bathroom din nashi mai kalar black and gold Aliyu ne tsaye karkashin shower dake zubar da Ruwan sanyi mai sanyaya jiki, duk da kasancewar garin ya sanyaya matuka dan yau yini akayi ana ruwa agarin na Abuja. Idonshi a rufe yana jin dadin saukar ruwan a fatarsa mai santsi, ciwon Kai yake fama dashi wanda rashin isassan hutu da bacci ya wanzar masa dashi.
Towel white color ya janyo ya nade iya kugunsa dashi ya fito dakin yana jinjina wa Afy yanda bata taba gajiya da tabbatar da tsaftar wajen kwanansa da na toilet dinsa ba, ko ranar daya dawo daga daurin aurensa ya tarar da dakin a share tsaf harda sabon zanin gado, duk da yafi tunanin Saaima ta aiko tazo tayi, ire ire wadannan su kesa ya ji kaunarta da ganin girmanta na daduwa a zuciyarsa, ya sani ya bata ranta amma bai taba dawowa yaga babu abinci mai rai da Lafiya akan dining table dinsa, shikam idan ya musguna mata Allah zai barshi ne?
Yana tsaye agaban mirrow dinsa ya gama feshe jikinsa da deodorant na maza "Nivea" , taje gashin kansa yayi sannan ya shafa lipbalm din nivea a lebunansa kananu kuma masu taushi kamar auduga, faffadan kafadunsa da murdadden damtsen sa da suka gaji da Gym yake duba , shi kansa halittarsa na kayatar dashi yanda ubangijinsa ya kera shi a tsaye Kuma dakakke irin zubin namijin duniya.....ya dade rabon da yaji mace a jikinsa kuma tabbas kafadunsa da kirjinsa sunyi kewar runguma cikin dumin mace. Wardrobe dinsu mai girma da tsayi ya bude yana kallon yanda rabi da kwatan kayan ciki duk na Afy ne, murmushi yayi yana mamakin yanda tayi dominating duk wasu maadanar da yake ajiye kayansa , a cewarta wai yanasa kayanta su dinga kamshinsa.
Wata Farar Moroccon jallabiya mai kyau ta maza ya dauko ya saka , Hularsa Zanna bukar ya ciro itama ya daidaita zamanta akansa sannan ya kara feshe jikinsa da turaren " Tom ford" ya fita a dakin bayan ya kashe fitilun ya jawo kofar, Da sassarfa yake sauka kan stairs din yana murmushin ganin Picture frames dinsu manya manya dake manne a bangon stairs din, hotunan manya da kananu masu dan karen kyau shida ita dakuma wanda suka dauka ranar suna tare da Yusuf Kinan. Warmers dake kan dining table da plates ya kalla kuma a take cikinsa ya murda mai alamun yunwa, tun safe rabonsa da abinci kuma yasan ya kamata yasa wani abu a cikinsa but his stomach can wait, Abu mafi muhimmanci a wajensa shine dubo halin da iyalinsa ke ciki.

"Iyali?"

Ya tambaya kansa da kansa a zuciyarsa yanajin zuciyar tana takurewa da jin irin gagarumin girman daya hau kansa a yau din, a yau din daya zamana Mijin dake da hakkin kula da matan aure guda biyu a karkashinsa, Iyali biyu da ke zamansa, zaman ikonsa, zaman rayuwar da ya tsara musu, zaman rayuwar da duk ake jira ya ja ragamarta, Wani sain har yau sai yanajin tamkar yaron da zai ruga ga Abbansa ko Ummansa ya shige jikinsu dan ya samu protection amma yau shi Aliyu at the age of 34 shi keda hakkin kula da Mata biyu da yaro daya. Ya sani yana cikin wani siradi mai wuya wanda maza that are into polygamy basa ganewa ko maida hankali akai, amma shi ya sani, a ankare yake da duk halin da makomar lahirarsa ke ciki.

" zaka iya Ali! Zaka iya! Kai namijin duniya ne!"

Ya fadawa kansa kafin ya fita a bangarensa ya nufi Bangaren AFIFAH JAJERE hannunsa rike da ledar da ya siyo mata chocolates, abunda ya faru shine bayan dawowarsa saida ya raba chocolates din gida biyu yasa wa RUMAN nata a leda daya, badan komai ba saidan yanda zuciyarsa ta dinga tsikararsa akan baiyu adalci ba daya siyowa Afy ita kadai, saida ya raba sannann hankalinsa ya kwanta yana jinjina wahala da maza sukesha akan conscience din polygamy.....it feels so Absurd! Saaima kadai ya tarar a falon nata tana zaune kan carpet tana waya, tana jin shigowarshi ta boye wayar tare da Fara gaisheshi, amsata kawai yayi ya wuce sama inda yafi tunanin zai sameta.

" kada ki yarda ki zubda hawayenki akan wata Rumana Afy, me akayi akayi ta? Kaddara dai ta riga fata amma ki nuna mata har yanzu batasan mai duniya take ciki ba, Ki mike ki karbo mijinki da gidanki, ko amafarki karki sakar mata komai kinji?"

Muryar muneera dazu kafin tafiyarsu ke min amsa kuwwa a kunnena, na share hawayen da suka gangaromin da tissue din hannuna inajin yanda idanuwan suka min nauyi sabida kukan da nasha tun dazu da naji shigowar motar data kawo su UmmuRuman gidana. Tunanina ya kara tuno min maganganun Yakumbo data fada min dazu da safiya.

AFIFAHWhere stories live. Discover now