Page 37

49 6 0
                                    

Tafiya ce mikakkiya ta awa 6 cur a hanya kafin isowar tawagar yan kawo Amarya UmmuRuman gidan mijinta dake garin Abuja, Mutum 4 ne acikin bus din idan harda driver da Salisu dake gaban mota zai kasance mutane 6 ne acikinta.  Motar kafin shigowarsu garin na Abuja shiru kakeji dan duk sun yi laushi jikinsu yayi Laasar kasancewar duk jamaar motar babu wanda ya taba kwatanta tafiya mai nisa irin haka idan ka cire direban da Kuma shi salisu dake ta hira abunsu, Sauran matan da duk sun gaji kowacce tana ta kallon hanya babu mai cewa Uffan, lokaci zuwa lokaci ne ma Inna duduwa wata yayar mahaifinsu ke dan amsa waya tana fadin cewa sun dai kusa isa, bayan ita babu mai cewa komai Musamman UMMU RUMAN da tsawa da kuma rugigi kai kace irin na hadiri ne kadai ke tashi acikin kanta da kuma zuciyarta, har yanzu da motar ke zuba uban gudu tana dosar wani waje da ubangiji ya kaddara cewa nan ne zai kasance sabuwar duniyarta, har yanzu ji takeyi tamkar zata farka da ga wani mafarki da ta kwanta yinsa tun ranar data ga Aliyu a kofar gidansu.
         Komai yazo ya faru ne tamkar kiftawa da bismilla, tamkar anyi ruwa andauke har qaddara ta hade rayuwarta data mutumin da duk duniya babu wanda takeso sama dashi....fiye ma da yanda takeson kanta a tunaninta. Kafin kwakwalwarta ta gama fahimtar mai ke faruwa sai tsintar kanta tayi a gaban mahaifinta a safiyar yau din kafin su taho, tana sanye da wata Sabuwar Atamfa riga da skirt da mayafinta da ajiya su yaya hafiza sukaje shagon wani sanannen mai dinki anan dorayi suka sayo ready made kaya kala 10 kasancewar mai dinkin ya saba siyar da dinkakkun kaya har da mayafan dazasu shiga dasu, Idan ba dan shi Aliyu yayi tunanin bawa Hafizar kudin naira 100k a safiyar jiyan da batasan mai zata saka ba ma.
          Kuka takeyi a durkushe gaban malam Ashiru dazun hannunta cikin na Inna duduwa, kukan da harga Allah ita kanta batasan maanarshi ba, tunda dai ta laluba zuciyarta taga babu abunda zatayi kewa anan gidansu din, babu wani da take takaicin rabuwa dashi kuma ko makaho ya shafa yasan rayuwarta dake gaba zatafi wanda take ciki ayanzu haske ninkin ba ninki, a takaice de kuka kawai take na tsananin murna da farin ciki, kuka irin na godewa Allah na saar data taka, kwanaki 10 baya ko duk duniya zata taru ta fada mata cewa wai yau zata amsa sunan MATAR ALIYU bazata taba yarda dasu ba amma sai gashi din, sai gashi har komai din ya faru, sai gashi har burin nata ya cika.

" Ni a matsayina na mahaifinki babu wani dogon bayani da nake da bukatar fadi maki Umma, tunda tun tashinki a duniya cikin wannan gidan tare dake ake duk wani fadi tashin Talauci da rayuwa, Wannan bawan Allah ya gama miki komai, yayi miki abunda ko ni ban miki ba....kibi Allah kibi mijinki Rumana, ki zauna lafiya dashi da iyalinsa, kada naji kada nagani Rumana, wallahi kikayi saken da ya koroki banida gurin ajiyarki, duk yayana mata bani da dakin ajiyarsu yayin zawarci billahillazi kunji na fadi muku!'

Malam Ashiru ya fada yana nunasu kaf dinsu da hannu musamman Hafiza da kullum tana ziryar gida, bini bini saita hado kaya tace tazo kwana. Iya abunda yake ganin zai iya fadi mata kenan, ai sudin ba yaran hutu bane, daidai gwargwado yasan cewa labarin zafin talauci saidai ita rumanan ta bawa wani labari ma, shi baiga dalilin da zai sa ya tsaya yana mata waazi akan lalle sai tabi miji ba, anashi ganin wannan yaran da basu san mai ake nufi da rayuwa ba ake fadimawa.
               Gyara zama tayi ajikin kujerar, kanta na jingine da windon tana kallon yanda ruwa yake zuba a hankali yana jika windon da tituna, damuna ta fara sauka a Abujan amma a kano ruwan bai fara saukowa ba tukun saidai zafi kullum. A hankali a hankali ta fuskanci tabbas sun shigo Abuja, wani gari da take mai kallon Madina tun suna kanana, ta dan waigo ta dubi yaya Hafiza dake gefenta tanata baccinta wuyanta a langwabe, Abuja wani gari ne da tasan cewa ba wajen zuwansu bane a da, ko a labari babu wani dan uwansu da sikaji labarin yana zaune a Abuja, tun tashinta yasa take wa garin kallon babban alamari, akwai wani lokaci da aka taba bikin wata a layinsu akace an kaita Abuja sukai ta jinjina lamarin har ita rumanan tace

AFIFAHWhere stories live. Discover now