Page 35

46 5 0
                                    

He's the eyes of my Hurricane; the calm Im drawn to amidst the chaos of my home.
                                          ~Lauren.

National defense HQ
Abuja

7:16pm

Hadadde kuma kayataccen Office mai cike da tarin kyau , tsari, haduwa Gami da kwarjini tamkar mamallakinsa. Office din mai dauke da painting irin kalar su ta sojoji wato Army green da tambarinsu na Camouflage, hotunan shugaban kasa da sauran manyan manyan hafsoshin gwamnatin ke manne a bangon office din. Zagayayyen wooden table mai kyau sai sheki yakeyi ga tarin takardu a baje akan taburin da kuma system dake a kunne ya gamayin zoom meeting ta cikinta mintuna kadan da suka wuce, tag dinsa mai dauke da sunan " COL. JAJERE ALIYU M." sai wani karamin photo frame mai kyau sosai, hotonsa ne da Matarshi AFIFAH da kuma dansu YUSUF KINAN ,hoton sun dauke shi ranar sunan kinan din kuma ya kayatar matuka dan duk wanda ya shigo office din sai idonsa ya kai kansa harma mutane su dauka suna complimenting iyalan nasa.
             Yana zaune akan kujerar table din yana rocking kujerar a hankali,idonsa a rufe ruf kamar mai bacci yayin da Sanyin AC ke sirarowa ta kowani bangare na office din, a zahirin gaskia ba bacci yakeyi ba kawai he's having his time, irin wannan lokaci dayake samu yayi tunani kuma yayi digesting abubuwa dayawa tundaga kan ayyikan office da kuma alamarin iyali dana dangi gaba daya. Dagowa yayi a hankali ya dubi agogon fatarsa yaga lokaci, ya kamata ya tafi gida dan ya dade sosai a office din yau ,mafi yawancin maaikatan duk sun tafi sai daidaiku da suka rage kowa yana kokarin karasa ayyukan gabansa.
Tattara takardun dake gabansa ya farayi tare da kashe system din, yana cikin hakan wayar telecom dake gefe ta fara ringing Kuma yana nuni da cewa Secretary dinsa ne ke Kira, kamar bazai dauka ba saidai ya sa hannu ya dauka ,

" Evening sir! You have a visitor sir"

Isaac ya furta yana dan jin tsoro aransa dan tabbas yasan fada zaisha bana wasa ba, kwana biyun nan zuciyar ogan nashi a kusa take kuma abu kadan zai balbale mutum, amma bazai iya hambarar da cin Hancin da aka kawo masa ba indai ya samu ya sama mata ganin Colonel din,

" I'm done for the day Isaac, make it tomorrow noon"

Aliyu ya fada yana jin haushin koma waye yazo yanzun babu appointment, yarasa meyasa wasu basu da tunani sam, abun mamaki saiga kiran Isaac ya kuma shigowa, wannan karan ya dauka dan yayi masa kaca kaca amma sai Isaac yayi caraf ya amshe da fadin

" its Captain Ellie....Shhh...She said its really urgent sir!"

Isaac ya fada yana dubanta, yana ajiye wayar yasa hannu ya janyo envelope dinda ke gabansa mai dauke da Dollars aciki ya janyota gabansa yana farin cikin nasarar dayaci,  indai karban cin hanci ne dan yayiwa mutane iso wajen Aliyun wannann ya kware akai kuma shine side business dinsa....nuni yayi mata ga stairs din ita kuma ta tashi tana murmushi ta dauki katuwar Flower bouquet din da kudinta ya haura naira dubu dari, ta juya tana taku daidai kuma mazaunanta na rausaya ta cikin damammen London V trousers dinta, Wandon daga kasa yayi fela sai saman kuma har zuwa cikinta, rigar jikinta mai yanayi da Bra amma long sleeve, Nonuwanta kamar zasu fito sabida yanda yar ficiciyar rigar tayi musu kadan.
          Wig dinta mai mugun kyau da tsada original human hair wanda kudinsa shima ya haura dubu dari uku, takalminta mai uban tsini kamad Allura tana takawa dashi cikin kwarewa akan stairs din har zuwa saman inda jerin gwanon ofisoshin suke.
           Captain Ellie jimoh, Navy Officer ce  yar shekaru 29, Christian, Inyamura kuma yar asalin garin Enugu, Captain Ellie is a successful young lady datayi saar samun successful career at a very Young age, tana da babban matsayi a Rundunarsu ta sojojin ruwan Nigeria kuma senior officer ce da rabin rayuwarta acikin ruwa takeyi kamar yarda akasan sojojin ruwan sunayi. Wata 2 da suka wuce ta fito Daga cikin ruwa dan halartar wani gagarumin taro da zaayi da duk wasu forces na kasar kuma ananne zata gabatar da report ga jamian sojojin na kasa bisa wani muhimmin abu, awannan daren da sukayi meeting anan ne ta kyalla ido taga Aliyu kuma zuciyarta tace dawa Allah ya hadata inba shima, kafin kace kobo ta tsunduma so da kaunar Aliyu,a tashin farko ta gabatar mishi da tayin kaunarta amma Aliyu yasa kafa ya hambarar da wannan tayin, Alal hakika shine irin soyayyar da Addini da Alada bai aminci dashi ba shi takeso suyi, babu abunda yadameta da Addininsa da Kuma aladarsa, tasha tarin mamaki da har mace kamarta namiji ya kalla yace baya bukata abune dabai taba faruwa ba a tarihin rayuwarta.
           Maimakon Ellie taji haushin Aliyu bisa rejecting dinta da yayi saima wutar kaunarsa da sonsa daya karu a rayuwarta, haka tayita shige da fice a office dinsa , waya da text messages kullum a rana saita bar mishi babu adadi, acikin messages din zai zabi na aiki aciki yayi reply sauran kuma ya bar mata abunta, a lokacin har ta koma bakin aikinta acan Lagos har aiki ya dan cin manta sannan ta dena damunsa, Last message dinda ta aiko masa shekaranjiya dayake nuni da cewa ta fito daga aiki ta kuma shigo garin Abujan, ta sanarwa Aliyu cewa yaune birthday dinta kuma tayi musu reserving table a Hilton hotel .
          Aliyu yaga message din jiya da daddare lokacin yana zaune a wajen yakumbo dauke da kinan , message din na shigowa ya gogeshi batare da bata lokaci ba, toh ita captain Ellie tasan cewa Aliyu ba zuwa zaiyi ba hakan yasa ta shirya kawai sannan ta biya ta siyan mai flowers ,ta gwammaci ita tazo har inda yake ta kawo mai a gift a ranar birthday dinta maimakom shi ya zo ya taya ta Murna.
          Ya gama tattara duk wasu takardunshi ya maidasu mazauninsu, ya miqe ya isa ga hanger din dayake rataye rigarshi ta saman ya dauka ya saka, Wani drawer ya bude mai dauke da jerin Bindigunsa kala kala kuma samfuri iri iri, yana nan tsaye Yaji knocking kadan kuma tun kafin ya bada izinin shigowa ta bude kofar ta shigo,  idonsa ya sauka akanta cikin irin shigar da bai taba ganinta dashi a zahiri ba saidai uniform dinta,  takalminta mai tsini tasa ta rufe kofar sannan ta fara takowa a hankali har izuwa gabansa jikinta yana wani irin rangaji tamkar reshen bishiya.....

AFIFAHWhere stories live. Discover now