page 4

35 3 0
                                    

Major General Mahfuz bako Jajere( Rtd) dan asalin garin jajere ne dake a birnin yoben Nigeria,  matansa 3 da yaya 9.
Matarshi ta farko hajiya babba yayanta 3, Anty bilki, Daddy Rufai,Daddy salman.
Matarshi ta 2 Umma Gaji da yayanta 4- Aliyu Haidar, Hanan,ikram sai auta Rais, Matar General ta 3 itace Umma zulai mai yaya 2- Sajida da Munirah.

        Mahaifinsa malam bako jajere shine maigarin jajere na wancan lokaci kafin Allah yayi masa rasuwa, malam bako jajere ya rasu ya bar Mata biyu da ya'ya shidda.
       Yakumbo Bilkisu Yar asalin yobe ce itama, itace matar malam bako ta farko kuma uwar yayanshi guda 4 maza 3 mace 1, mahfuz shine na 3. Daya matarshi iya mai madara itace matarshi ta biyu kuma ta haifa mishi yaya 2 duk mata, Allah yayiwa iya mai madara rasuwa tun da dadewa yayanta mata kuma duk sunyi aure harda jikoki. Malam bako kafin rasuwarsa dattijo ne na kwarai mai mutunci da dattaku, mutum ne mai rufin asiri bamai tarin dukiya ba , ya tarbiyantar da ya'yanshi tarbiya mai nagarta kuma kan matanshi da yayanshi duk a hade yake har ya bar duniya baa taba jin kansu ba,  malam bako yayanshi maza kadai yasa a karatun zamani matan kuma a iya na arabiyya suke tsayawa sai yayi musu aure daga sun tasa. 
         Mahfuz shine karami acikin mazan kuma sai Allah ya qadarta tafiyarsa aikin soja tun bayan ya gama makarantar gaba da secondary ya sanadin wani aminin mal bako dake zaune a jihar kaduna garin gwamna, lokacin da mahfuz zai tafi ansha kuka tsakaninsa da yakumbo da sauran yan uwansa amma malam ya dage akan tafiyarshi, a wancan lokaci gwamnati tana ta rokon mutanen kasa da su dinga saka yaransu makarantar horon sojoji sabida karancinsu daake fama dashi ga kuma bukatarsu nata tasowa a kasar, malam bako badan yanaso ya salwantar da dansa ba amma kasancewarshi shugaba kuma jagoran garinsu yasa shi farawa da gidansa wala allah sauran mutane zasu fi aminta dasu kai yaransu suma.
           Haka mahfuz ya hada jakarsa yayi sallama dasu tun yana dan shekara goma 17, tun da ya tafi sai da yayi shekara 1 bai zo gida ba saidai wasika akai akai, wani lokacin zaa dauki watanni babu wasikar ma,sai hankalin yakumbo ya tashi tai ta kuka tana ganin an kashe mata danta a fagen daga. sannu sannu bata hana zuwa saidai a dade baa je ba, mahfuz tin daga scratch ya fara karatun soji har Allah ya bashi saa da Albarkar aiki ya Kai wani matsayi da bazaa kirashi karamin soja ba.
         Awani dawowa dayayi gida ya tarar an aura mishi Yar uwarshi abokiyar wasanshi Mai suna manniratu, auren jeka ga dakinka akayi musu shida mannira tunda basu suka daidaita kansu ba, Mahfuz ya karbi abun ya kuma godewa iyayensa, bayan hutunsa ya kare ya dauki matarshi suka wuce barikin sojoji dake garin ikko, anan barikin suka haifi Bilkisu mai sunan Yakumbo, ko shekara batayi ba ya kara samun transfer zuwa wani barikin sojoji dake plateau anan kuma aka haifi Rufai da salman, adan tsakankanin lokacin nan Allah ya budewa mahfuz sosai arziki da dukiya ya wadata ga karin girma yanata samu Daga gwamnati, anan ne yayi shawarar samun matsuguni na dindindin anan garin yobe sabida tarbiyyan yaranshi da makarantarsu.
          General Mahfuz ya sayi katafaren gidanshi a unguwar lowcost GRA din garin yobe, unguwace ta masu hannu da shuni da kuma kusoshin gwamnati, Gida ne katoton gaske mai matukar girma da mutum sai yaji tsoro idan ya shiga musamman da daddare sabida dogayen bishiyu da waje mai Kama da daji, a hankali a hankali ya dinga sare bishiyun yana tada gini da sassa kala kala,Babban abun shaawa da gidan shine har round about akwai mai fesar da ruwa gwanin ban shaawa.
           General mahfuz ya kara auren Aisha (Gaji) bayan shekaru 8 da aurensa na fari, Gaji itace zaa ce akanta yayi auran so maana matar daya aura tanaso yana so,  Aisha (Gaji) yar asalin garin borno ce,  babarbariya mai kyau kuma yar gidan mutunci da tarbiya,sunyi soyayya sosai har ta kaisu da aure babu bata lokaci aka kawota nan yobe gidan daya ajiye mannira amma sassan Gaji daban , bayan aurenta da wata 9 cif cif ta haifo santalelen danta  ALIYU HAIDAR, saida Aliyu yayi shekara 6 babu qani sannan aka haifi Aisha( hanan) .
        Akwai kishi sosai tsakanin hajiya Babba(mannira) da Gaji amma hakan bai sa su yin mummunan kishin da zai tayar wa mijinsu hankali ba, girmamawace a tsakaninsu da mutunta juna Dan hajiya babba ta girmewa Gaji kuma yaranta sune manyan gida ,bugu da kari zaman Yakumbo uwar mijinsu a tare dasu shiya kara wanzar da zaman lafiya agidan mahfuz tunda shi ba mazauni bane, baya nan baya can a hakan ma dan ya taka babban mukami a fagen aikinsu shiyasa zirga zirgar ta ragu.
         Anana ananan bayan wasu shekaru Wani dawowa da Mahfuz yayi bayan ya shafe watanni kusan 4 baya garin yazo musu da labarin auren dayayo a kano,aure ne da ko yakumbo da yayyansa manya babu wanda yasan dashi sai labarinshi da sukaji, yana dawowa kamar baa hayyacinsa ba ya fara gyaran wani sashen gidan dake a rufe, haka ya hau barnatar da kudi babu ji babu gani kamar wanda zaiyi auren Fari, sati daya bayan dawowarshi sai ga tawagar amarya zulaiha ita da yan uwanta daga kano, dangin da suka rakota marasa mutunci da kamun kai sukai ta rashin mutunci da habaice habaice da tonon fada har saida yakumbo ta taka musu burki sannan suka shiga taitayinsu dan yakumbo ba kanwar lasa bace kuma a tsaye take akan danta da iyalansa.
        Da zuwan Umma zulai kamar yadda yaran gidan suke kiranta abubuwa da dama suka sauya agidan, farin ciki da annushuwa yayi musu kaura, zaman Lafiya da akeyi daidai gwargwado ya fara zama tarihi sanadiyar munafurci da tuggu irin na zulai, mace ce makira kuma yar bariki da ta kware aduk wani salon tuggu,  zaman Lafiya sam baya wanzuwa aduk inda take,   da fari kafin su ganota haka take addabar su da munafurci tana hadasu fada da mijinsu dakuma yakumbo.  Bayan an auro zulai da shekara daya ta haifi yarta sajida, sajida tana da shekara uku suka kara haihuwa tare da Gaji tsirarsu sati 3 kawai, zulai ta haifi Munirah (sunan hajiya babba akasa) Gaji kuma ta haifi hafsatul Ikram.
        A wannan shekarar dai kuma Allah yayiwa hajiya Babba rasuwa sanadiyar hatsarin mota, anji mutuwar hajiya babba dan macece Mara matsala sam harkar gabanta kawai takeyi sai kuma lamarin yaranta,tuni dama diyarta ta bilkisu tayi aure har ma danta, kannenta maza suma duk sun girma suna shekararsu ta farko a jamia, anyi rashi kuma ansha alhini kafin lokaci ya tafi da komai aka manta aka cigaba da gurza rayuwar kishi tsakanin Gaji da zulai.   
         Zulai mace ce makira mai bin bokaye da yan tsibbu Wanda a sanadin hakane dubun ta tacika har aurenta na fari ya mutu ta baro diya awancan gidan ta auri Mahfuz, mace ce Mai wayon tsiya da ta riga ta kafa gwamnatinta a wajen General Mahfuz da kyawawan dabiu na bogi da yasashi yake ganin babu mace mai hakuri da ladabi irin ta, irin haka ne yasa ko kararta Gaji ta kawo baya yarda kuma baya zurfafa bincike a karshe ma saidai laifin ya dawo kan Gajin, a hankali a hankali tun Kafin aje ko ina duk wannan soyayyar da qaunar dake tsakaninsa da Gaji ta dinga bajewa tana bin iska ta dawo bata da katabus agidan sai zaman yaya kawai da takeyi.

AFIFAHWhere stories live. Discover now