page 13

22 3 0
                                    

Yau watanmu hudu cif da fara zuwa "yobe state polytechnic " inda nake yin Diploma in Mass communication, Ikram da Munirah na karantar science laboratory technology, tabbas rayuwa ta chanja sannan abubuwa da dama sun faru a tsakanin wadannan watannin.
       Shigarmu makaranta tasa na kara gogewa da rayuwa na Kara koyan zamantakewa da different set of people, na gane cewa rayuwa bata tsaya a iya fence din gidanmu ba da compound din secondary school din mu, Da fari mun fara zuwa polytechnic baa San ranmu ba sabida ba nan muka so zuwa ba, duk mu ukun Alhikmah university illorin muka so tafiya amma Abba yayi tsalle ya dire akan cewa bazai taba bari muyi nisa da gida ba, Ranmu baiso ba Abba yasa aka kawo mishi admission letters guda 3 har gida kamar yadda ya samowa yaya hanan.
          Ikram da munira sunso yin bore akan fasa yin karatun gaba daya anasu ganin munfi karfin mushiga polytechnic, na lallaba su tare da nuna musu cewa karatu karatu ne kuma muna da damar zurfafa karatun mu bayan munyi diploma din,  ganin nasaki jikina inata harkokin school yasa suma suka saki jiki muka fara babu yabo babu fallasa,
         Abba bai fasa treating dinmu kamar yara ba dan kaimu makarantar akeyi har venue sannan motar ta jiramu mu tashi adawo damu gida, saida mukayi semester daya a haka , a dawowa 2nd semester ne lokutan tashinmu ya banbanta nida su iky, sanadiyar hakane Abba ya yarje mana akan mu dinga dawowa gida da kanmu. Ina matukar kaunar course of study dina na jarida coz it has always been my dream and passion tun Ina yarinya, Ina son aikin jarida Ina burin na zama yar jarida sananniya, bansani ba ko hakan ya hada da zama da tsohuwa kamar yakumbo, kowa yasan mostly tsofaffi ke jin radio, duk wasu shirye shiryen radio da gidan TV na haddace su nasan lokutan su da masu gabatarwa.
Sau tari nasha fadawa yakumbo cewa nifa agidan radio nakeson nayi aiki,  su ikram su kyalkyale da dariya yayin da yakumbo zatayi min addua da fatan nasara, Abba kuma sai ya Kara da cewa

" har a BBC London zakiyi aikin jarida kinji diyata"

Shiyasa ranar da Abba ya damka min admission letter dita naga mass communication abun bai bani mamaki ba dan Abba mutum ne dayake zama da yaransa tun suna kananu, yasan komai about their dreams ,yasan komai gameda hangen nesan su da irin nasu tunanin. Abba is actually my best friend on this planet!
          Sauran abubuwan da suka faru abubuwa ne masu matukar muhimmanci agareni fiye da komai, shin mai zaifi soyayya da kaunar dake tsakanina da yaya Aliyu? Me zai Danne wannan farin cikin da annushuwan da muka tsinci kanmu aciki nida shi? Soyayya tsakaninmu ta yi nisa ko kuma nace ta fara ne jim kadan bayan dawowarmu daga umrah, kamar yadda ya bamu kudi mu sayi waya acan haka na damka kudin ahannun daddy Rufai, daddy rufai ya sai mana waya sabuwar IPhone x duka mu ukun. Bayan dawowarmu muka cigaba da zana waec amma hankalina da tunani yana ga yaya Aliyu, tunaninshi ya zame min abokin rayuwa babu dare babu rana, na zama mutum mai shiru shiru na fara kebence kaina daga wajen su ikram , letter daya barmin acikin jakata ta kasance kamar wata addua agareni duk dare kafin na kwnta saina dauko na karanta sannann na ajiyeta a kirjina ina mai tuna kyakkyawar fuskar yaya Aliyu.
         Kafin kace me na rame na fada sabida tunaninsa da haushin halin daya sani a ciki, yaya Aliyu ya kwadaita min soyayyarshi sannan ya tafi ya barni babu shi , ko labarin zuwanshi babu Sam dan dama irin haka sai a bakin ikram nake samu, sau da dama nasha attempting karban numbersa daga wajen ikram duk da ban taba jin itama tace sunyi dashi ba , Ego da jan aji irin nawa ya hana na sami numbershi ko a wayar yakumbo duk da itama ba yawan kiranta yake ba, bansani ba ko hakan nada nasaba da aikinsa.  Tambayoyi kala kala nasha Daga wajen ikram da yakumbo amma amsar dai guda daya ce,

" babu komai fa, exams fever nakeyi"

Tayaya ikram takeso na kalleta nace mata ciwon son yayanta nakeyi? Tayaya yakumbo takeso na dubi idonta nace kaunar Yaya Aliyu ke neman halakarni? Tayaya Zan Iya fadawa Abba cewa soyayya na fara? Ana cikin wannan yanayin ne dangin Faruk  masu neman auren Ikram sukazo tambaya wajen Abba dasu Daddy Rufai, alokacin kowa agida yana sane da soyayyar dake tsakanin Faruk da ikram din, Abba ya amsa musu tambayar su yakuma bawa Faruk din izinin cigaba da nemanta har zuwa lokacin da zaice su fito domin asaka musu Rana.
Soyayyar ikram da yaya faruk ba  karamin burgeni takeyi ba, a halin danake ciki gani nake babu mai saa kamar ikram din.
         Yakumbo kullum sai tayi fada sosai akan yanayin danasa kaina aciki, akwai wani dare da ta shigo daki ta tarar dani rungume da wasikar yaya Aliyu idona yana tsiyayar da hawaye, ina ganinta nayi saurin goge hawaye na na boye takardar a karkashin pillow dan ban tsammaci shigowarta ba a lokacin, zama tayi a kusa dani ta tayar dani zaune , hannun ta tasa ta share min hawaye na sannan tace,

AFIFAHWhere stories live. Discover now