page 5

34 4 0
                                    

Daga wannan ranar rainon Afifah da tarbiyyarta kacokan ya dawo hannun yakumbo Bilki tare da taimakon Yar tayin raino da aka dauko mata mai suna mama Rabi, kullum tana sashin yakumbo bata fita ko nan da can sai a hankali data gane akwai saaninta ikram da munira da kuma Rais dake bin ikram sai suka hada kansu suke zuwa wasa sashen yakumbo ko kuma suyi wasa anan compound dinsu,  haka yaran suka taso su 4 abunsu gwanin ban shaawa amma Afifah ta fita daban dasu dan ita fara ce sosai kuma da anganta anga zubin buzaye.
        Lokacin da suka isa shiga makaranta sunada shekara 5 anan ma saida akayi sabon case da Umma zulai har ta jawa kanta General Mahfuz ya dankara mata saki guda ta bar gidan na tsawon wata 4 kafin ta dawo da taimakon Allah da taimakon kawunnenta data dinga sawa suna zuwa suna bashi hakuri wasu kuma su biyo ta wajen yakumbo, tabbas ta dandana kudarta bayan komawarta gida dan fakirai ne iyayenta basu da Komai sai tulin yaya gurbatattu da basu san shansu ba basu shan cinsu na, wahala tayi wahala agida saide kudin kashewa ya gagareta sakamakon satar da kannenta ke mata         

          nadama ta lullubeta ta fahimci cewa tabbas batada gatan daya wuce gidan General din, batayi kasa a guiwa ba ta fara aike tana bada hakuri har ta samu ya mayarda da ita bayan ya kafa Mata gargadi akan Afifa da shiga shaanin yarinyar da bata tsare mata komai ba, yarinyar dako fahimtar a Ina take bata gamayi ba amma Zulai ta tsaneta ta tsani gilmawarta agidan, ga kuma wani aminci dasukeyi da yarta munira da ikram shima baya mata dadi tayi iya yinta ta raba amma takasa,zumunci ne da Allah ya hada da kanshi, sajida ce kawai take mara mata baya akan cusgunawa Afifa shima sai in babu wanda yake gani,dan akan Afifa yakumbo tana iya fito na fito da koma waye.
          Abun da ya jawo sakin da Abbansu yayi mata shine lokacin da yaran suka isa shiga makaranta General Mahfuz ya sa Afifa tana amfani da sunan shi kamar yadda yaransa sukeyi, lokacin da Zulai ta fahimci hakan ba karamin tayar da tarzoma tayi ba kan cewa tabbas Afifa diyar shi ce dan akan wani dalilin zaisa tayi amfani da sunanshi tunda yana ikirarin yasan mahaifinta, rigima da balai ya balle tayita mai tijara ,
           karin abunda ya kuma hargitsa zulai shine "Will" ( wasiyya) da ya rubuta ya bawa lauyoyinsa kan cewa ga wasu kebantattun kadara daya ware ya kuma mallakawa Afifa idan baya raye,wannan kadarori basa cikin na magada ya barwa Afifa halak malak, toh anan ne fa gobarar bala I da masifa ta kuma tashi har saida yayi mata saki daya sannan ya sami nutsuwa agidan.
         Sauran jamaar gidan kamar yayan hajiya babba da hajiya Gaji sam basu da matsala da Afifa, sun dauketa matsayin ya', kanwa kuma yar uwa dan gudun sabawa mahaifinsu da kuma girmama decision dinshi, babu yabo babu fallasa iyalan dakin Gaji suke muamalantar Afifa dan su bata tsare musu komai ba, Hanan ce bata shiga shaanin yaran dan ko kannenta da suke uwa daya Ikram da rais ba shiga harkarsu take ba balle kuma Afifa da take jinta babu dangin iya babu na baba,   ta bangaren  Aliyu kuwa ya rungume su duka a matsayin kannenshi wanda asali da zaa bude zuciyarshi yafi tausayin Afifa,har yanzu wannan ranar da aka zo da ita ta kasa bacewa daga tunaninsa sam.
         duk da karancin shekarun sa baya daukar raini kuma baya shiga shaanin yaran ballanta su raina shi, he is always there for them as a brother and a protector but they dont mess with him, haka suka dinga tasowa shekaru nata tafiya suna kara girma har suka kammala primary school zaa shiga JSS1, alokacin shikuma aliyu ya tafi NDA Kaduna bayan kammala babbar secondary dinsa, tafiyar sa NDA ita ta kara datse shakuwar da yayi da kannenshi ta kuma kara fito da ainihin discipline ,zafin rai da cin zali dake a ranshi koda yake nature ne na mafi yawancin masu suna ALI musamman kuma Shi da Allah ya nufeshi da zama soja.
       Wahala da azabar dayake sha a makarantar horon sojoji ta kaduna ita ta kara chanja Aliyu ya koma wani daban bashi ba, duk yanda yake kaunar zama soja all his life saida takai ya karaya har yana rokon mahaifinshi akan ya taimaka mishi ya dawo dashi gida ya hakura da zama soja amma Abbansu yaki yakuma cigaba da karfafa mishi guiwa akan yayi hakuri watarana wahalar mai wucewa ce, Duk wani hutu da zaizo gida har ya koma su Afifa suna yinshi ne cikin wahala da takura har sai yakoma zasu cigaba da sararawa,  duk ranar da akace yazo kuwa Afifa bazaa kara ganin shawaginta agidan ba kullum tana wajen yakumbo abunta, daga School sai islamiyar da ake zuwa duk dare ayi musu.

AFIFAHWhere stories live. Discover now