🌷Shafi na 50🌷

Start from the beginning
                                    

Shiru Alh Muaz ya danyi a hankali ya furta “Allah ya bashi lafiya,”

“Ameen,” suka amsa a tare.

Sai bayan kusan awa guda sannan Alh Muaz ya tashi zai koma gida domin dare yayi sosai sannan babu wajen kwana a asibitin. Binsa waje Alamin yayi domin ya dan taka masa. 

Suna fita Jasmine ta dauko wayarta ta kira Marianna. Muryarta a kasale ta ce “Hi,”

Hamma Marianna tayi tace  “Why are you calling this early? I just woke up,”

Kai tsaye Jasmine tace “What is happening Anna, I read a very bad news earlier today, what happened to Matt?”

Shiru Marianna tayi har sai da ta kira sunanta “Anna,” sannan tace “Jas,why are you asking such a bizarre question? Matt is fine,”

“But I read something about…” kafin Jasmine ta karasa maganar Anna tace “Go and sleep I know it’s still night there, stop over thinking you of all people should know how those tabloids build up lies,”

Shiru Jasmine tayi hankalinta ya dan kwanta “Okay, but we will talk later when I wake up,”

“Sure,” kawai Marianna tace ta katse wayar.

Har Jasmine ta ajiye wayarta a gefe sai kuma ta fara vibrating, sunan Diane da ta gani (Cousin din Matthew ta bangaren mahaifiyarsa, kuma kawarta ce sosai) ne yasa ta dan bata rai dan tasan lafiya lau Diane bazata kirata ba tafi yi mata text ko suyi chatting indai ba wani abu bane mai matukar mahimmanci Diane bata kiran mutum, a hankali ta amsa wayar “Hello,”

Kafin Jasmine ta rufe bakinta Diane ta fara zayyano magana “Jeez, Jas which part of the world are you in? I have been trying to reach you but you’re no available,”

Shiru Jasmine tayi tana jinta bayan ta dire maganar Jasmine tace “First of all slow down, second I am in Germany and i think it’s network problem,”

“Yeah, I know you heard the news so I want to know how you are doing?”

Jasmine ji tayi zuciyarta tace daram, kar dai abunda ta karanta gaskiya ne, da sauri tace “What news Diane?”

“About Matt, no one told you?”

“Yes, please tell me,”

Tsayawa Diane ta danyi tana tunanin yadda zata fadawa Jasmine abunda ya faru ba tare da ta tayar mata da hankali ba, “He tried to commit suicide,” zubur Jasmine tayi ta mike tsaye “What,” ta faɗa tare da dora hannu akan kirjinta.

Da sauri Diane tace “But he didn’t succeed, he is in the hospital, they get to him on time he didn’t die,”

Wani dogon nunfashi Jasmine ta saki wanda bata san ta rike ba “Where is he now? How is he?” tayi saurin tambayar Diane.

“He is uncouncious but the doctors said he will survive,” shiru Diane tayi
“What is it?” Jasmine ta tambayeta dan tasan shirun nata bana lafiya bane  “His Suicide note, he said something about his undying love for you, what happen between you two Jas?”

Komawa Jasmine tayi ta zauna “Diane,” ta furta a hankali “He proposed and I rejected because I don’t feel the same way anymore,” hawaye ne suka fara gangarowa akan kumatunta tana danasani tare da nadamar yadda ta bullowa lamarin “I broke up with him and I am married Diane, I married someone else,”

Da karfi Diane tace “What the fuck!!!” mamaki ne ya hana ta magana dan ko kadan bata taba tsamanin Jasmine zata auri wani wanda ba Matthews. “How did all that happen? When? How did I not know of this?” ta baibaye Jasmine da tambayoyi.
“It’s a long story,” Jasmine ta bata amsa. “I will explain whenever we meet,”

“Wow, did you know that Matt has converted. He changed his religion a day after you left because he thought that was the only thing stopping you from marrying him,” Shiru Diane ta dan yi sannan ta cigaba da cewa "It was a big issue with the family but they let him be as long as he doesn't let the public know about it."

Hannu jasmine ta dora akan bakinta tana jinjina maganar da Diane ta faɗa mata,  Matt ya musulunta. Ko kadan bata taba tunanin zai iya chanja addininsa akanta ba. Addinin da ya gada awajen iyyaye da kakaninsa duk ahanlinsu shi suke bi.

Kasa magana Jasmine tayi, Diane tace “I guess he didn’t tell you about his sickness,”

Da sauri Jasmine tace “What’s wrong with him,”

Murmushin takaici Diane tayi tace “I can’t tell you I promised him that I won’t tell you,”

Lumshe idanunta Jasmine tayi amma hakan bai hana hawaye zuba daga cikin idanunta ba, cikin murya kuka tace “Diane, I can’t come right away but promise me that you will be informing me about everything that happen to him before I come,”

Kafin Diane ta bata amsa cardiac monitor din da aka sawa Alh Yunus ne ya fara kara, cikin hanzari Jasmine ta jefar da wayarta a kasa ba tare da ta kashe ba ta nufi inda Alh Yunus yake kwance Cardiac monitor din ta kalla taga heart rate dinsa ya ragu sosai, gashi nunfashinsa ya fara daukewa,  kirjinsa kwata kwata baya dagawa yana komawa kamar yadda yake yi da.
.
Wani red button na emergency da ke gefen gadon ta danna sannan ta nufi kofar dakin da gudu suka ci karo da Alamin “What happen Jasmine,” tambayarta yake amma ba tashi take ba ture shi tayi ta zura kanta hallway din “Medical Emergency!” ta faɗa da karfi tana kokarin hana kanta yin kuka.

Komawa tayi da gudu inda Alh Yunus yake kwance, gabaki daya ta birkici ga karar da Cardiac machine din yake yi, kirjinsa ta fara dannawa tana kokarin ta taimaka masa yayi nunfashi, da gudu likitocin suka karaso cikin dakin, da kyar wata nurse ta janye Jasmine daga wajen ta fita daga dakin.

Hawaye ne kawai ke zuba akan fuskarta, ta kasa ko da daga kanta ne bare ta mike tsaye tunda ta tsuguna a inda take. Alamin ne ya tsuguna a gabanta yace “Jasmine,” a hankali ta dago jajayen idanunta ta kalleshi, tausayi ta bashi sosai ganin yadda idanunta ya dan kumburar, kwayar idonunta tayi green sosai kamar ganye, hannunta ya rike “He will be fine, In’sha Allah zai samu sauki,” yana gama magana likitocin suka fito daga dakin mikewa su suka yi atare.

Jasmine tana kallon fuskar doctor Stephen ta fara girgiza kanta, sauran likitocin kuwa duk sunkuyar da kansu sukayi “I am sorry, we lost him,” wadannan kalomin suna fitowa daga bakin Dr Stephen Jasmine taji kamar an buga mata guduma akanta. Alamin kuwa kasa motsawa yayi chak ya kame a inda yake, ji yayi kamar mafarki yake tamkar a wata duniyar ta da ban yake wanda da ya farka daga bacci zai ga duk a mafarki ne, karar faduwar Jasmine da yaji ne ya dawo masa da hankalinsa jikinsa ya nufi inda ta fadi.

Jasmine Baturiyya ceWhere stories live. Discover now