🌷Shafi na 47🌷

Comenzar desde el principio
                                    

Saboda gajiya da tayi da yanayin zamanta yasa Jasmine ta gyra zamanta ta jingina ajikinsa sannan tace "Tana gidan mu, I got her a new nanny bana son ina yawo da ita, she is a baby jinkinta bai yi kwari ba,"

Murmushi Alamin yayi ya gyra mata gashinta da ya zubo gefen fuskarata yana jin dadin sakin jikinta da tayi da shi, a hankali yace "That's very thoughtful, yanzu me zamu fara ci?"

"Ka zaba, what do you want?"

"Duk abunda zaki ci,"

Murmushi kawai jasmine tayi ta dauki fork da yar wuka ta yanko sausage ta kawo masa daidai bakinsa, a haka ta rika bashi abinci yana ci itama tana ci, suna dan taba hira tare da tsokanar juna.

Kwankwasa kofar suite dinsu da aka yi ne yasa Jasmine juyawa ta kalleshi tace "Are we expecting someone?" kokarin mikewa tayi Alamin ya riketa yace "Just ignore it love,"

"Indan emergency ne fa,"

"Ba shi bane,"

Murmushi kawai tayi ta mike zata je ta bude kofar shima yayi saurin mikewa ya riko "Ki tsaya a nan, lemme open the door,"

Alamin yana bude kofar yaga Nadia a tsaye, fuskarsa cike da mamaki yace "Nadia?"

"Yaya Alamin ina kwana," ta gaishe murya a makale cike da yanga har da dan durgusawa.

Shiru Alamin yayi ya matsa mata ta shigo sannan ya rufe kofar. Tsayawa yayi yana jiran tayi magana. "Uhmm.. Yaya Alamin daman magana na zo muyi,"

Tsayuwarsa ya gyra yace "Okay, ina jin ki,"

Cikin suite din ta kalla ta bude bakinta zata yi magana ta hango Jasmine ta fito daga dinning area, a take taji kamar an chaka mata mashi a cikin zuciyarta dan gabaki daya shirinta rugujewa yayi ya narke tamkar gishirin da aka kwarawa ruwa, har sai da fuskarta ta nuna ranta ya baci duk da tayi saurin rufe bacin ran da murmushi amma sai da Alamin ya gani. Ita a zatonta Jasmine ta na dakin Marianna dan taga anan ta sauka, sam bata yi zaton zata sameta a nan ba.

A hankali Jasmine ta karaso wajen tana kallon kayan jikin Nadia. Da kyar ta iya rike dariyarta, tana juyawa kuwa suka hada ido da Alamin ta gane shima dariyar yake rikewa. Mamaki ne ya kamata ganin Nadia tayi irin shigarta, hatta irin tattarar da take yi da gashin kanta shi Nadia tayi da Brazillian wig din da ke kanta, gashi tasha makeup sosai, tayi kyau ba wai bata yi kyau ba sai dai kwaliyar tayi saffiya da yawa sannan kana kallon shigar indai ka san Jasmine to kasan ita ta kwaikwaya.
Murmushi Jasmine ta sakar mata sannan tace "Yanzu ko muke breakfast, please join us,"

Murmushin yake Nadia tayi sannan tace "Ina kwana bamu gaisa ba,"

"Lafiya, muje," Jasmine ta nuna mata hanya tare da yin gaba Alamin yana biye da ita a baya. Kujerar da ke kallon ta Alamin Nadia ta Jawo ta zauna. Jasmine ta janyo kujera zata zauna Alamin ya janyota ta fado kan cinyarsa, daidai kunnenta ya kai bakinsa ya rada mata magana cikin harshen Spanish. Murmushi kawai Jasmine tayi ta saki jikinta,  hannu Alamin yasa ya gutsuro Sausage ya kawowa Jasmine bakinta ta karba, kumatunta ya sumbata sannan shima ya kai wani bakinsa.

Zumbur Nadia tayi ta mike dan ji take kamar ta kurma ihu a wajen saboda tsabar takaici da bakin ciki, wato a gaban idanunta zasu yi wannan barikin ko kunyar babu, to kara baza su yi mata ba.

Da sauri Alamin yace "Aa ina zaki kuma baki fada min abunda ya kawo ki ba, ki zauna mana,"

Komawa Nadia tayi ta zauna tana kallo Jasmine ta dago kofin hot Chocolate dinta ta kai wa Alamin bakinsa ya sha sannan itama ta sha. Runtse idanunta tayi tana bawa zuciyarta hakuri kar tayi abunda zai sa ta barar da garinta gaba daya. "Daman, na zo ne akan maganar komawa ta gida," Nadia ta faɗa a hankali tana kokarin haɗa karyar da zata faɗa dan ba abunda ya kawota ba kenan.

Jasmine Baturiyya ceDonde viven las historias. Descúbrelo ahora