🌷Shafi na 39🌷

Start from the beginning
                                    

Wasu hawayen ne suka sake zubowa fuskar Jasmine tace "Yet she called me a mistake," dagowa Jasmine tayi daga kan kafadarsa ta kalleshi tace "Does that means I am a bastard?" Da sauri Alamin ya dora hannunsa akan lebenta yace "Shh, stop saying that Love, you're not and even if you are that doesn't make you any less of who you're, and neither will my love for you lessen or your mother's love for you," shiru Alamin ya danyi sannan ya cigaba da cewa "Tana sonki Jasmine, she was suprised just like you idan kika bata lokacin a hankali zaki fahimci komai."

Lumshe idanunta Jasmine tayi ta budesu akan fuskar Alamin a hankali tace "Thank you," komawa tayi zata kwanta Alamin ya janyota "Ina baza ki kwanta ki cigaba da wannan kukan ba?"

Shiru Jasmine tayi bata ce masa komai ba sannan bata ma yi kokarin kwace hannuta daga cikin nasa ba kamar yadda ta saba ko mosti bata yi ba kawai idanu ta zubawa masa. Girgiza kansa Alamin yayi yace "Inaah, I cannot let you wallow in this self pity party Sweetheart, ki tashi ki shirya zamu fita,"

Zame hannuta Jasmine tayi ta jingina a jikin gadonta sannan tace "Ni babu inda zani, kawai ka kyale ni."

"I have already done that, na baki yafi 2hours kinyi kukan yanzu ki tashi ki shirya ko ni na shirya ki da kaine," Matsowa Alamin yayi kusa da ita kamar zai daga ta, da sauri Jasmine ta kauce tana harararsa, tsakiyar gadon ta koma tace "Ni babu idan zani ka kyale ni,"

Murmushi Alamin yayi ya mike kamar zai fita, sakin jikinta Jasmine tayi ta zauna dan a zatonta Alamin fita zai yi, bata yi aune ba sai ji tayi ya kamota, kokarin kwacewa ta fara tana fusge fusge amma yaki cikata "Alamin dan Allah ka kyale," Jasmine ta faɗa a marairaice. Shiru yayi mata ya daga ta chak sai bathroom din dakinta. Ajiyeta yayi ya kunna ruwa a bath sannan ya juya yace "Na taya ki cire kayan ne ko zaki yi da kanki,"

Harararsa tayi tace "Naji zan yi da kaina," fitowa daga bandakin Alamin yayi ya shiga cikin closet dinta ya dauko mata kayan da zata saka. Leko kanta Jasmine ta farayi bayan ta gama wankan tace "Can you get out Please, zan fito."

Yar karamar dariya Alamin yayi yace "You're quite funny love, Wai meye difference din towel din da ke jikinki da wayannan short skirts din da kike sakawa,"

Tabe baki Jasmine tayi tace "The difference is you here, ni dai ka fita,"
Girgiza kansa kawai Alamin yayi ya tashi ya fita. Kayan da ya dauko mata ta kalla ta tabe baki sannan ta shige cikin closet dinta ta dauko wanda take son ta saka. Silky white button up shirt da coffee color wando ta dauko sai wani dan karamin mayafi da zata yafa. Takalmi kuwa yau bata dauko heels din da ta saba sakawa ba, farin canvas na kamfanin Nike ta dauko.
Turare kawai ta fashe jikinta sannan ta fito. Alamin na zaune akan kujera a falo ta fito har inda yake ta tako tace "Na shirya, Wai ina zamu?"

Dagowa Alamin yayi ya kalleta yace "A haka zamu?"

Kayan jikinta ta kalla tace "Rigar nan ta kusa kaiwa gwiwata fa and na rufe gashina, ni bazan chanja kaya ba sai dai na fasa zuwa,"

Murmushi kawai Alamin yayi yace "It's fine, muje a hakan." Dan ya fuskanci rigima take ji.

Kasa suka sauka suka fita waje, wata bakar G-Wagon ce ta tsaya gabansu Alamin ya budewa Jasmine gidan baya ta shiga sannan shima ya shigo ya zauna a kusa da ita. Juyawa Jasmine tayi ta kalleshi dan duk sanda zasu fita da kansa yake tuka su. Murmushi kawai Alamin yayi mata bai ce komai ba har suka isa idan zasu. Alamin ne ya fara fita sannan Jasmine ta biyo banyansa tana karewa wajen kallo. Cikin Gusto Restaurant suka shiga suka zauna aka kawo masu menu suka zabi irin abincin da suke so, sannan suka zauna jira. Dagowa Jasmine tayi ta ga Alamin yana kallonta, "What?" Ta tambayeshi fuskarta babu fara'a.
Dariya Alamin yayi ganin har yanzu bata sauko ba, "You look Beautiful without makeup," ya bata amsa. 

Jasmine Baturiyya ceWhere stories live. Discover now