🌷Shafi na 39🌷

Start from the beginning
                                    

Shiru Anty Kaulat tayi bata ba ta amsa ba hakan yasa Jasmine ta sake maimaita tambayarta da dan karfi. Dago idanunta Anty Kaulat tayi ta kalli Jasmine tace "Just be because I didn't raise doesn't mean zaki iya daga min murya, I am still your mother,"

Girgiza kanta Jasmine ta fara yi tana dariyar takaici tace "Really? All this while I thought you don't know where I was or worst you're dead ashe gani na ne kawai ba kya son yi," Anty Kaulat ta bude bakinta zata yi magana Jasmine ta rigata da cewa "Ba sai kince komai ba Mami, na san ba kya sona, I am a mistake right, daman bai kamata na zo ba, I will leave right away." Da sauri Jasmine ta juya ta yi hanyar sauka kasa tana ji mahaifiyarta tana kiranta taki juyawa.


Alamin yana zaune a falon kasa tare da kannenta, ya ga ta sauko da gudu ta fita daga falon. Mikewa yayi da sauri ya bita da yaga bata tsaya ba ta yi hanyar fita daga gidan, da gudu ya bita ya riko hannuta, kokarin kwacewa tayi amma yaki cikata, a hankali ya juyo da ita yaga tana kuka janyota jikinsa yayi ya rugumeta bai ce mata komai ta ringa kuka a jikinsa har kukan nata ya dan tsagaita, sannan yaja hannunta ya kaita har idan motarsu take ya bude mata kofa ta shiga sannan shima ya shiga. 

Alamin yana yin parking a cikin gida Jasmine ta bude kofar motar ta fita tun kafin ya kashe motar, da sauri ta nufi bangarensu ta shige dakinta ta rufe da mukulli, a jikin kofar dakin ta sulale a kasa tana kuka kamar ranta zai fita.

Tunda tasan mahaifiyarta na raye bata da burin da ya wuce ta ganta a zahiri sai dai bata taba yin tunanin dalilin da yasa ta tafi ta barta ba ko dalilin da yasa bata taɓa nemanta ba. Bata taba kokwanton soyayyar da ke tsakanin Uwa da Ɗa ba sai yau, dan ta gani da idonta mahaifiyarta bata sonta.

Alamin yana shigowa ya zo bakin kofar dakin Jasmine yana bugawa yafi minti goma ya magana a bakin kofar nan taki bude masa haka ya hakura ya koma dakinsa ya zauna dan kasa fita ko ina yayi. Laptop dinsa ya dauko ya bude ya fara dube mails din da aka turo masa. Shi kansa yasan yana sake da aikinsa yanzu ba kamar da ba, gashi ya tarawa kansa bashin aiki mai yawa dan yafi kwana biyu bai je office dinsa ba. Yana duba emails dinne yaga ashe yana da Appointment gobe a Abuja ga tafiyar da zai yi Japan duk a goben, gaba daya sati nan ma bai kamata yayi shi a Nigeria ba dan ranar Wednesday shi da Jamal zasu hadu a dubai akan wani sabon kasuwanci da zasu bude a a chan UAE din. Dafa kasan yayi ya lumshe idanunsa, ga kuma matsalar Jasmine, abubuwa na kokarin dagule masa. Da sauri yake typing a cikin laptop din ya turawa PA dinsa email akan ta daga masa appointments dinsa na abuja sai bayan ya dawo daga Dubai. Emails dinsa ya cigaba da replying amma hankalinsa yana kan Jasmine, tunanin tafiya yake da ita business trip din nasa idan ta yarda, dan yasan bazai iya tafiya ya barta a cikin wannan hali ba. Gashi daman zai je Germany wajen Mahaifinsa sai su tafi tare tunda daman yayiwa mahaifin na sa alkawarin zai kai masa ita. Rufe laptop dinsa yayi bayan ya turawa PA sa wani email din akan ta yi masa replying din sauran Emails din da basu da mahimmaci sosai ta bar masa masu mahimmaci.

Yana duba lokaci yaga har 8:30pm na dare yayi, mikewa yayi ya shiga bathroom yayi wanka ya shiyar cikin kananan kaya jeans da simple shirt ya fito yana ta tashin kamshi. Dakin Jasmine yaje yana bugawa taki budewa haka yasa ya koma dakinsa ya dauko extra key din dakinta ya bude, a kan gado ya ganta zaune ta cusa kanta a tsakanin cinyarta da alama bata daina kukan ba, a hankali ya karasa inda take ya zauna a kusa da ita "Jasmine," ya kira sunanta a hankali. Kin dagowa tayi har sai da ya dora hannunsa a kanta yace "Kin san dai kuka baya magani ko, but a problem shared is problem solved," a hankali ta dago kanta ta kalleshi tace "Alamin bata so na she doesn't want me,"


Hannusa yasa ya goge mata hawayen da ke kwararowa akan fuskarta ya janyota ta kwantar da kanta akan kafadarsa sannan yace "Shh sweetheart, babu uwar da bata son ɗan ta duk lalacewarsa bare ke Jasmine, babu wanda bazai yi alfahari ba idan har ya sameki a matsayin Ya'a,"

Jasmine Baturiyya ceWhere stories live. Discover now