chapter 86_100

26 1 0
                                    

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*🏡A GIDANMU SUKE🏡*

®️🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[  '''Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women''']
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/ 110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*

                *_Z• W• F•🏝_*

MALLAKAR👇
*LEEMART PINKY*
           AND
*MRS BASAKKWACE*

_WANNAN LABARIN DAGA FARKON SA HAR ƘARSHEN SA SADAUKAR WA NE GA IYAYEN MU ALLAH UBANGIJI YA ƘARA MUSU LAFIYA DA NISAN KWANA,DA DUKKAN MUSULMAI BAKI ƊAYA,YA ALLAH KAJIƘAN IYAYEN MU TUNDAGA ZAMANIN ANNABI ADAM HAR ZUWA YAU._

*LAST PAGE*
*PAGE 86&100*

Adaran kowani ango ya shiga ɗakin shi don raya sunar  ma'aiki SAW.

*AGURGUJE*

Haka rayuwa taci gaba da tafiya,ako wani ɓan gare da daɗi ba daɗi.

Ɓangaran Jahda ciki nata ƙara girma ,inda take samun kulawa daga wajan Hajiya Jasmin da ada ba wanda yakaita yi mata rashin kunya sam bata ganin girmanta

Ayanzun ko kunya da dana sanin abinda tayi mata takeyi.

Sam bata shiga cikin gida,kullum tana ɓangaran Hajiya Jasmin,ita ke mata komi,ita tasata a gaba sukaje tayanka form ɗin awo,duk ran awo ita ke kaita.

Ako da yaushe Jaheer na maƙale a ranta,ranan da aka ɗaura mai aure kasa bacci tayi tana ta kuka tasan yanzun yana can kwance da wancan kahirar yana jin daɗi ,harsai da tayi zazzaɓi.

Jaheer da Juliet kuwa ɓarje soyayyar su sukeyi kamar zasu haɗiye juna,suna gudun ɓata ma juna rai,ba abinda ke wakana a tsakanin su kamar so da kyautatawa da kulawa danuna ma juna ƙauna ko kaɗan basa son ɓacin ran junan su.

Jawahir ko tun suna wata ɗaya tafara laulayin ciki,Jahoor yayi farin ciki sosai saida ya haɗa ƴar ƙwarya-ƙwaryan walima.

Amie haryanzun bata saduda ta sauko ba,har maƙwaftan nigeria zuwa take biyan malamai,ko gaisuwan Jahoor bata amsawa acewar ta Hajiya Juwairah ta asirce shi.

Ummie ko har yanzun bata sake ma Juliet in sunzo gaishe su,daga gaisuwa bata ƙara amsa mata magana.

Abin na damunta a zuciyar ta,amma take ɓoye bataso sam Jaheer ya fahimci bata jin daɗin abinda mahaifiyar shi ke mata.

Ansa ranan auran Jesica da  Jahal,abokin Jaheer da tunda yaganta da biki ya liƙe mata,suka fara soyayya.

Ya nuna da gaske yake badawasa ba yaturo iyaye akai maganan komi,duk da iyayen shi sunso su tubure ma maganan jin ba musulma bace.

Da ƙyar ya shawo kansu suka barshi  kafin sukazo akai maganan auran.

Jadida ko sam batajin daɗin auren nan mijinta Jawad mashayi ne ga neman mata.

Wata rana ma inyanajin iskancin shi har gida har kan gadon auran su.

Gashi bata isa tayi magana ba  yaci ubanta,yace tallan ta aka kawo mai yatemaka ya aura,saide tayi kuka ta share hawayen ta ba mai lallashinta,don tanajin kunyar  taje ta faɗa ma iyayenta ko iyayen shi,gani take ba zaa yarda ba don a zahiri Jawad yana fuskan mutanen kirki,ba ace zaa samai ɗan yatsa  abaki ya tauna ba.

Amma a baɗi abinda yake aikatawa na ashha ne,addua kawai take mai akoda yaushe,inda da ƙyar ta samu yasata wani islamiya nan kusa da su take zuwa.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Feb 13, 2021 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

 A GIDANMU SUKE Labari ne akan Soyayyar arniya da Kuma musulmi Where stories live. Discover now