chapter 2

39 3 0
                                    

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*🏡A GIDAN MU SUKE🏡*

®️🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[  '''Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women''']
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/ 110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*

                *_Z• W• F•🏝_*

MALLAKIN MARUBUTA BIYU:- 👇
*LEEMART PINKY*
           _DA_
*MRS BASAKKWACE*

_WANNAN LABARIN DAGA FARKON SA HAR ƘARSHEN SA SADAUKAR WA NE GA IYAYEN MU ALLAH UBANGIJI YA ƘARA MUSU LAFIYA DA NISAN KWANA,DA DUKKAN MUSULMAI BAKI ƊAYA,YA ALLAH KAJIƘAN IYAYEN MU TUNDAGA ZAMANIN ANNABI ADAM HAR ZUWA YAU._

*PLEASE DUK WANDA YA KARANTA YAI MA IYAYEN MU  ADDU'A*

JINJINA GA -: _MASOYAN GA MASOYAN MU GABA ƊAYA_

*PAGE 3&4*

Mikewa yayi a fusace tare dayin kwafa ya galla mata muguwan harara yace,"wallahi inkika kara zuwa min gabana babu dankwali,ince kikawo min abinci Kona sha,kika zomin babu dankwali kai buya-buya saina buga kanki da bango,wawiya mai suffan yahudu,mtswwww.


Yana maganan yana nunata da dan yatsa yana murzasu suna k'aara, inda ya kafeta da ido.


Itama kafeshi tai da ido tasake baki da hanci,don yanayin da yake mata magana yayi matukar burgeta yayi mugun tafiya da hankalin ta ,batama ji masifar da yake ba sam don hankalinta yatafi duniyar tunanin sunyi aure ji take kamar ta je ta rungume shi.


Mtswwww "wai kai Jaheer  wani irin taurin kai kake dashi?,wuce kafitar min a side,katafi side din uwarka kajira in ka yi aure ka haifa kaima Yayanka  iko ,amma sam bazan dauka anan ba".

Hajiya Kaka ce ta saki dogon tsaki kafin ta Fara magana a hasale.

Kwafa yayi ba tare da yayi magana ba ya fice.


Da ido tabi bayan shi tana murmushi,inda Hajiya Kaka tabishi da mugun hara-ra


********
Waike Juwairah mai nene hadin d'anki Jaheer da wa yannan yaran ne?.


Hajiya Jamilah kenan itace mahaifiyar su Jahdah mata wajan kanin mahaifin  Jaheer,bata da hak'uri sam da mutunci,danginta ne danginta ne dangi,amma dangin miji ko ba ta d'auke su abakin komi ba,inuwar giginyace tanesa kan sha dad'i.

"Mai ya farune Hajiya Jamila?.

Hajiya Juwairah kenan mahaifiyar Jaheer ,tana da kirki da tausayin na kasa da su,tana son dangin mijinta sosai kafin zuwan Hajiya Jamila tazo ta zuzzugata tasata a Hanya,in basa son mutum basa son sane,shiyasa duk a family Ja'afar Dank'asa kansu yafi haduwa sai kuma Hajiya Jumainah wacce bata riga ta shigo ba tana da baki a side d'inta.

Taba baki Hajiya Jamilah tayi ta gyara dauri ta turo shi gaban goshi tare da dukan cinya tace,"wa yannan yayan arnan mana,ina daga side dina daga sama na hango su a parking lot suna magana kinga yanda yake rawan jiki yana washe hak'ora".

Uhumm kide bari abinnan yana min ciwo nai magana nayi magana bakina kamar na shantu , Jaheer sam baijin magana-na".

"Kimai wuta-wuta ki bude mai idanu,ni ka isa in haife ka inyi magana kak'iji,wallahi ba'a haife d'an-nanba".

Cike da ziga take maganan.

Taba baki Hajiya Juwairah tayi kafin tace,"mai kikeso inma Jaheer?,shide ba yaro ba balle in samu bulala in zane shi,abinda nasani in ma akwai alaka tsakanin su anan wajanne dole ya sauke makaman  taurin kansa yabi umurnina,don da yai mu'amala dasu gwamma ya mutu,shiyasa Jarood nakeson yaronnan yanajin magana ko sosai,ba ruwan shi shiru-shiru".


 A GIDANMU SUKE Labari ne akan Soyayyar arniya da Kuma musulmi Where stories live. Discover now