chapter 41_45

8 0 0
                                    

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*🏡A GIDANMU SUKE🏡*

®️🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[  '''Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women''']
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/ 110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*

                *_Z• W• F•🏝_*

MALLAKAR👇
*LEEMART PINKY*
           AND
*MRS BASAKKWACE*

_WANNAN LABARIN DAGA FARKON SA HAR ƘARSHEN SA SADAUKAR WA NE GA IYAYEN MU ALLAH UBANGIJI YA ƘARA MUSU LAFIYA DA NISAN KWANA,DA DUKKAN MUSULMAI BAKI ƊAYA,YA ALLAH KAJIƘAN IYAYEN MU TUNDAGA ZAMANIN ANNABI ADAM HAR ZUWA YAU._

JINJINA GA -: _MASOYAN GA MASOYAN MU GABA ƊAYA_

*PAGE 41&45*

"Nifa in gaya miki Jawahir yarannan tun daga uwarsu har su ba wanda ya taɓa min abu ƙi ko abun Allah wadare hakanan kawai ban son su ban ƙaunar su".

"Amma de Ummie sam hakan bai kyautu ba wallahi,yanzun Alal misali Ummie hakanan kawai kiga wani ko wata sun ɗaura min karan tsana ya zakiji a ranki?.

Shiru Hajiya Juwaira tayi kamar mai nazarin wani abu,can kuma ta ƙara duban ƴar tata tace,"wallahi bazan ƙaunace shi ba har abada,wai kinsan soyayyan dake tsakanin ɗa da uwa kuwa,koko kin san soyayyan dake tsakanin wanda ya nuna yana son ɗan ka,kibari ki aure zaki tantance yanzun ko mai zan faɗa miki bazaki fahimta ba".

Murmushi Jawahir tayi tare da tashi daga kishingiɗan da tayi ta gyara ɗaurin kalabinta tace,"Ummie duk kinsan da wa ƴannan amma kike nuna musu kyara don ba addinin mu ɗaya ba,kyaran da muke gwada musu bazai sa su musulinta ba,ba abinda zai jawo ma musulinci illa a rinƙa cewa ashe haka musulincin yake,basu son mutane,ƙyamar wa ƴanda ba addini ɗaya suke ba,amma in muka ja su a jiki,ba ƙyama balle kyara hakan zaisa suji suna ƙaunar addinn mu suji har suna sha'awan shiga".

"Tou tabbatacciya baki abin magana mai bakin tsuntsu kawai,nizaki tasa a gaba da wa'azi,tun kafin a haifeki nasan nan tashi kiban waje,don ko musulinta yau sukai bazan bari in haɗa jini dasu ba,sabida mutane zasu rinƙa nuna ni anacewa ga surukan tubabbu".

Cike da masifa tana zaro manyan idanuwan ta take maganan.

Dariya Jawahir tasa tare da miƙewa ta fita,don Ummie su ta haddace faɗan daba gairi ba dalili.

*******
Awajan party da su Jadidah suka je da ƙyar suka sha a wajan maza.

Mata masu wayo ne da sunga ankusa tashi suke kama hanyar gidan iyayen su don gudun ɓarna a wajan ɓatattun maza.

Da yawan matan sun tafi sai tsiraru irin su Jahda daJadidah da wasu ƙawayen su,inda da ƙyar suka sha suka bar wajan kayan su duk a yayyage  Allah ya kawo wani soja ya cecesu.

Koda suka dawo gida anshiga sallah isha'i ba wanda yasan sun dawo kamar yanda ba wanda yasan fitar su.

Koh Hajiya Jamila batasan shigowar su ba,suna can ɓangaran Hajiya Jumaina suna tufka da warwara.

*******
"Wai Ammie har yanzun aikinnan shiru Jahir fa ko kallona baiyi balle ya kulani".

Cike da damuwa Jahda ke gaban mahaifiyarta tana mata magana

"Mtseww shiɗin banza,kina zaune zaizo yana risina miki yana miki daɗin baki,a lokacin zaki juyashi kamar kin samu masa  a tanda anan zai gane cewa duk kyan takalmi ƙafa zai taka".

 A GIDANMU SUKE Labari ne akan Soyayyar arniya da Kuma musulmi Où les histoires vivent. Découvrez maintenant