chapter 66_70

6 1 0
                                    

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*🏡A GIDANMU SUKE🏡*

®️🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[  '''Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women''']
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/ 110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*

                *_Z• W• F•🏝_*

MALLAKAR👇
*LEEMART PINKY*
           AND
*MRS BASAKKWACE*

_WANNAN LABARIN DAGA FARKON SA HAR ƘARSHEN SA SADAUKAR WA NE GA IYAYEN MU ALLAH UBANGIJI YA ƘARA MUSU LAFIYA DA NISAN KWANA,DA DUKKAN MUSULMAI BAKI ƊAYA,YA ALLAH KAJIƘAN IYAYEN MU TUNDAGA ZAMANIN ANNABI ADAM HAR ZUWA YAU._

*GODIYA TA MUSAMMAN GA MASOYA NAFILI DANA ƁOYE,INA GODIYA SOSAI DA KULAWAR KU GARENI,WA ƳANDA SUKA KIRANI SUKAI MIN GAISUWA DA WAƳANDA SUKA MIN MESSAGE TA WhatsApp NAGODE SOSAI ALLAH UBANGIJI YABAT ZUMUNCI AMIN YA RABB*

*PAGE 66&70*

Awani sukwane Amie ta cakumota tace,"dan ubanki kina da cikin boka,dama ne ta same mu wanda zaki zauna kai da ƙafa kice Jaheer ke da alhakin cikinan kinga ko dole ya aure ki".

Agigice take maganan,mai cike da tarin ruɗani.

Atsorace Jahda ke kallon Ammie ta idanuwanta duk sun fito ,bakin ta da halshen ta sun mata nauyi,tsananin tsoro da firgici ya shigeta.

Ammie bata damu da yanayin ƴartata ba,taci gaba da faɗin,"adaka abuga atankaɗa a rairaya,duk matsa da rintsi karki sake kice bashi bane ,ki dage kai da ƙafa,a haka zamuci ma manufarmu in sunsan wata ai basu san wata ba".

Ya za'ayi tace Jaheer baccin komi da ya faru ya sani,hakan ya ƙara masa tsananin tsanan ta,gaskiya ko maganan Ammie zata bi don ji take in bata aure shi ba mutuwa zatayi,bazata zauna tana ji tana gani ba wata ta aure shi,da ƙyar ta iya ɗaga halshen ta da yayi nauyi zatayi magana aka turo ƙofa.

Kai kallon su sukayi lokaci ɗaya ga ƙofar dukkan nin su ƙirjin su yana ƙara tsananin bugu.

Alhaji Jalal bayan shi Hajiya Jasmin ne da Juliet da Jawahir sai Jadida kowa kakalle fuskan shi cike yake da tarin damuwa.

Alhaji Jalal ya ƙarasa bakin gadon yayin da Jahda tai ƙasa da kanta ƙirjinta na tsanan ta bugu .

Cikin sanyi murya tace,"Dady wallahi Jaheer ne Jaheer yayi min ,shiyamin wayo da alƙawarin zai aure ni".

Cikin muryan kuka take maganan.

Hajiya Jasmin sai da ta nema kai ƙasa sabida firgicin maganan Jahda Jawahir da tai ƙarfin halin tare ta.

Juliet ko zama tayi ƙasa daɓas ta rasa tunanin da zatayi ƙwaƙwal wanta yamata wani irin nauyi sosai ƙirjinta wani matsanancin bugu yakeyi,yayinda tafara gani wasu taurari nafitowa daga idonta,ta rasa sam wani tunani zatayi akan Jahir ashe mazinaci ne,zuciyar ta tabata amsa.

Alhaji Jalal ko baya-baya yayi kan shi na sarawa.

Jawahir girgiza kai takeyi hawaye nabin idon ta bayan ta zaunar da Aunty Amarya akan kujera da itama zuban hawaye takeyi masu ɗumi.

Tace,"Dady Jahda ƙarya takeyi Yaya Jahir bazaiyi haka ba,bashi bane na yarda da yayana,nayarda da tarbiyan da iyayen mu sukayi mana,bazai aikata zina ba".

Cikin sanyin murya take maganan,kamar zata fashe da kuka.

"Ke dalla can munafuka dake Jahir ɗin yake yawo,sanda ya lalubeta kin sani ne ko zaiyi shawara dake ne,zanci mutuncin ki ƴar iska mara kunya".

 A GIDANMU SUKE Labari ne akan Soyayyar arniya da Kuma musulmi Where stories live. Discover now