chapter 7_8

27 1 0
                                    

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*🏡A GIDAN MU SUKE🏡*

®️🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[  '''Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women''']
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/ 110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*

                *_Z• W• F•🏝_*

MALLAKIN MARUBUTA BIYU:- 👇
*LEEMART PINKY💖*
           _DA_
*MRS BASAKKWACE*

_WANNAN LABARIN DAGA FARKON SA HAR ƘARSHEN SA SADAUKAR WA NE GA IYAYEN MU ALLAH UBANGIJI YA ƘARA MUSU LAFIYA DA NISAN KWANA,DA DUKKAN MUSULMAI BAKI ƊAYA,YA ALLAH KAJIƘAN IYAYEN MU TUNDAGA ZAMANIN ANNABI ADAM HAR ZUWA YAU._

*MAƘIYA AITA ACI GABA DA HAƘURI IRINSU O'O DA O'O😂*

JINJINA GA -: _MASOYAN GA MASOYAN MU GABA ƊAYA_


*PAGE 7&8*

"Har suka bar kofar gidan Jennifer Bata daina d'aga masu hannu ba Saida suka bar layinsu sannan ta daina waigensu sosai take Kuka kamar wace aka cirewa Rai juyo da kanshi alhaji Jabeer yayi yamaida dubansa gareta sosai kukanta yake taba Masa zuciya har ga Allah ya tsani yaga macce na zubda hawaye wani zafi yakeji a zuciyar'sa  shiyasa duk inda Mace take alhaji Jabeer Yana ganin girmanta sosai Kuma yana girmama mace ko wace irice balamma wannan da yake gani amanace agaresa gyaran murya yayi yaja glass din fuskarshi 'kasa sannan yace

"Jennifer This cry is enough for you to take away all your worries and I will never hurt you."

'Dago da kan'ta Jenifer tayi da rinanun idanun'ta da suka kada sukayi ja saboda azabar kukan da takeyi ta maida dubanta gareshi kamar wace zatayi magana sai Kuma tayi shuru gyada Masa kanta kawai tayi alamar tou.

Murmushi yasakar Mata yace "I love you so much Jennifer I will never let you down".

Murmushi ita tasakar Masa  tace "thanks" share hawayen idanun'ta tashigayi saboda Jenifer duk da tana arniya Amma tasan girman manya duk yanda babba yayi Mata magana bazata taba kin karbar maganar shi ba shiyasa ko agarinsu tsofafin garinnasu suke saka Mata albarka ba kamar sauran yaran garin ba.

Sosai alhaji jabeer yaji dadin yanda yaga ta karbi maganar sa ba gardama ko rashin karba murmushi yakarayi Dan daga gani yasan bazatayi taurin kaiba yasamu kalar macen da yake fatar samu gyara zamansa yayi yamaida dubansa ga alhaji Ibrahim da tuni yanan Yana lekasu ta mirror din motar sai murmushi yakeyi Dan yasan abokinsa ba abaya ba wajen iya sarrafa mace ya gwane a wannan fannin din harara Alhaji jabeer ya wurga Masa Dan yalura da irin kallon da yakeyi masu Sosa keyar kansa yayi sannan yace "ango ango".

Ango kasha kamshi mijin mace biyu na hajiya Jamila ga Kuma Jenifer duk Kai kadai Allah dai yataya riko abokina.

Murmushi Alhaji jabeer yayi saboda  har ga Allah yaji dadin wannan kirarin da yayi Masa sosai suna cikin Wannan wasan barkwancin ne har suka iso Jahar kebbi Sha'aban super market suka Fara shiga Saida yayowa familys dinsa sayaya sosai sannan yashiga mota suna Kama hanyar gida gabanshi yashiga dukan uku_uku Amma sai yadake yacije saboda tsaf ya karanchi hajiya Jamila idan taga yanayi Mata sulu_sulu shiyasa take Kara yimasa masifa suna Isa kofar gida'n sukayi Horn Mai gadi da gudunsa yazo yabude masu gate yanayi masu sannu da zuwa suna Danna kansu acikin gidan ya'yanshi suka fito sunayi Masa oyoyo Amma Banda hajiya Jamila dake bedroom dinta tana bacci bama tasan sun isoba hajiya kaka ce kawai itama tana gidan sama tana hangosu

Firfito wa sukai daga motor
inda jikin Jennifer yayi mugun sanyi bayan taci kuka ta koshi idanuwanta harsun gaji da kumbura.


Suna gafda shiga cikin gida'n inda yaran gaba daya suka fito suna musu oyoyo suna bin Jennifer da ido inda Jenifer ke sanye da weeding gown kanta lullube da veil fari  yayinda gashin kanta aka gyara shi ya kwanta a bayanta luf-luf.

 A GIDANMU SUKE Labari ne akan Soyayyar arniya da Kuma musulmi Where stories live. Discover now