chapter 71_75

8 1 0
                                    

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*🏡A GIDANMU SUKE🏡*

®️🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[  '''Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women''']
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/ 110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*

                *_Z• W• F•🏝_*

MALLAKAR👇
*LEEMART PINKY*
           AND
*MRS BASAKKWACE*

_WANNAN LABARIN DAGA FARKON SA HAR ƘARSHEN SA SADAUKAR WA NE GA IYAYEN MU ALLAH UBANGIJI YA ƘARA MUSU LAFIYA DA NISAN KWANA,DA DUKKAN MUSULMAI BAKI ƊAYA,YA ALLAH KAJIƘAN IYAYEN MU TUNDAGA ZAMANIN ANNABI ADAM HAR ZUWA YAU._

*PAGE 71&75*

Abieee wallahi ƙarya takemin sharri tamin,Abie ban taɓa riƙe hannun wata don naji daɗi ko in aikata zina da ita ba,Abie Jahada ƙanwata ce bazan so in ɓata mata rayuwa ba,Abie ku yarda dani bani bane,bani nai mata ciki ba,taji tsoron Allah tafaɗi gaskiya".

Cikin dakusassiyar murya yake magana idon shi hawaye masu ɗumi suna sauka.

"Wallahi Abie shine ranan yace,"in kawo mai fresh milk,naje na iske shi kwance wai marar shi naciwo,in kulle ƙofa inzo in temaka masa,duk nabi na ruɗe Abie ganin baida lafiya na dafa ruwan ɗumi a kitchen ɗin side ɗin su nazo da towel a tinani na buguwa ne yasa  zan gasa masa,kawai-kawai-kawai".

Jahda ce ke magana cikin muryan ban tausayi kamar da gaske labarin da take badawa.

Bako kunya take saki magana gaban iyayen ta.

Abie cikin tsawa mai cike da tsantsan ɓacin rai yace,"kawai mai munafuka,ki magana ko  inkashe ki tun kafin ki kasheni,dabadin ƙarfin addu'a ba da yanzun kun samin hawan jini keda munafukar uwarki".

"Eh dole kace haka,ancuce mu a hanamu kuka,tou wallahi ko ya aureta ko nakai shi kotu".

Hajiya Jamila ke magana cike da murje ido bako kunya tana ganin asirin su zai rufu.

"Jawahir kije side ɗina ki ɗauko flash a jikin  laptop ɗina ɗakina akwai CCTV za'a ga kom".

Cewan Jahir da yake ƙoarin gyara zaman shi.

Daga Hajiya Jamila har Jahdah lokaci ɗaya suka miƙe suna kallon Jaheer ,ɗakin duk su suka zuba ma ido,kowanne su cike da tashin hankali tsantsa a fuskan shi.

Jawahir ko jiki na rawa ta miƙe tafita har tanacin tuntuɓe,haɗa ido sukai da Jahoor ta galla masa hararan da sai da yaji gaban shi ya faɗi,don cin mutunci a gaban ta ya doke yayanta akan laifin da ba nashi ba.

Munites kaɗan ta dawo ta miƙa ma Abie.

Abie sawa yayi jiki tv bayan ya kunna,Jahir ya zuba ma Jahda ido don ya tsinke da alamarinta wato boka har ciki yai mata.

"Jahir wane folder ne?.

Faɗan Abie kowa ya zuba ma Tv ido zasu sha labari.

Jahir yabuƙace a bashi remote ko aka bashi ya duba folder sai gashinan  kamar a film,tunda  Jahir yashiga ɗakinta yai mata treatment  tai bacci da harhiran da sukai tabashi labarin amfani da boka da yayi da ita awatan ramadan.

Kuka kawai Jahda take bayan ta zube guywowinta a ƙasa.

Hajiya Jamila ta ɗaura hannu akai ta kurma ihu ta faɗi ƙasa tana ta birgima,tana faɗin Jahda shegen bakin ki ya jawo da baki faɗa ba,gashinan ya ɗauka wayyo Allah na.

 A GIDANMU SUKE Labari ne akan Soyayyar arniya da Kuma musulmi Where stories live. Discover now