chapter 5_6

33 2 0
                                    

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*🏡A GIDAN MU SUKE🏡*

®️🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[  '''Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women''']
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/ 110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*

                *_Z• W• F•🏝_*

MALLAKIN MARUBUTA BIYU:- 👇
*LEEMART Pinky*💖
           _DA_
*MRS BASAKKWACE*

_WANNAN LABARIN DAGA FARKON SA HAR ƘARSHEN SA SADAUKAR WA NE GA IYAYEN MU ALLAH UBANGIJI YA ƘARA MUSU LAFIYA DA NISAN KWANA,DA DUKKAN MUSULMAI BAKI ƊAYA,YA ALLAH KAJIƘAN IYAYEN MU TUNDAGA ZAMANIN ANNABI ADAM HAR ZUWA YAU._

JINJINA GA -: _MASOYAN  GA MASOYAN MU GABA ƊAYA_

*Page 5&6*

*CIGABAN ASALIN LABARI*

Gida gaba daya ya rikice da kamshin girku kala-kala,da kamshin turarukan wuta masu kamshi da sanyaya zuciya.

Kowa kagani cikin farinciki yake banda Hajiya saboda gaba d'aya tayi kicin kicin da rai suna shiga gidan kaitsaye d'akinta tawuce

Alhajinne kawai yatsaya suna gaisawa da mutane kamar yadda yasaba

Tunda sukadawo  komai ya chakule musu saboda yadda Hajiya ta d'aga hankalinta tunyana rar-rashinta haryazo yadaina maida Hankalinsa kanta

Zaune suke shida abokansa firarsu kawai suke amma hankalinsa nakan Hajiya saboda yadda yabarota tanata kuka .

Maganar Alhaji Ibrahim ne yace "Yadai Alhaji meyake damunkane haka yakamata kadaina sanya tunani acikin zuciyarka saboda karma kamu dawata cutar".

Girgiza kai yayi tareda murmushi yace"lafia lau , yakamata kushirya gobe dawuri kunsan nisan garin nan ga-gajiya gashi jibine d'aurin Auren".

'Danjim! Alhaji Ibrahim yayi yace "inagafa Alhaji gara muje a jirgi saboda nisan tafiyarnan koya kace?.

Dariya yayi yace, " ai tafiya mabud'in ilimi ne banta'bayin tafiya menisaba daga birnin kebbi zuwa Taraba-ba inaso nayi naga gari nasake ganin baiwar da Allah yaimana a 'kasarmu".

Nansukaci gaba da tat-taunawa saida aka kira sallah sannan kowa yatashi suka nufi masallaci.

Ranar alhamis tunda asuba yatashi haryagama shiri Hajiya batasaniba tayi d'ai-d'ai tanata sakin munshari tana bacci
Kallo ya 'kare mata yadda tasaki jiki jin anakiranshi awaya shiyasa yafita kawai dan bayason yatasheta daga bacci kuma tasan da tafiyar sunmayi salsundaceh

Cikin kwanciyar hankali suka nufi taraba cikin matarsa su hud'une dukansu har, abokinnasu Wanda za'ayi auren 'kaninsa
Tafiya yankin azaba kuma mabud'in ilmi basu suka isa Taraba ba sai k'arfe shida na safe gaskiya direban nasu yayi matu'kar 'kokari yadda yayi tuk'i babu ko gyangyad'i
gaskiya sunga tarba sosai awajen fulanin Taraba mutane masu matuk'ar kamala da addini gaskiya sundace.

Kwanansu biyu dan sai ranar lahadi da safe san-nan suka taho but d'in motarsu cikeda tsaraba ma'kil su kwai ne nono da sauran kayayyaki danma sunki karb'ar wasu,tunda suka fara tafiya basu tsaya ba har suka shiga jihar Adamawa sannan ne suka tsaya sukayi sallah suka d'anci wani abu sukaci gaba da tafiya.

Saidai basuyi nisaba motarsu ta lalace wanda yasa dole suka tsaya suka fito 'karewa wajen kallo suke gasu dai a babban titi amma babu alamar manyan gidaje saidai bukkoki dakuma gidajen 'kasa suma saika matsa kad'an shiga ciki kuma da alama garin kiristoci sunfi yawa saboda yadda suke ganinsu yara da manya sunabin wata hanya sunyi wanka hannayensu ri'keda bible .

 A GIDANMU SUKE Labari ne akan Soyayyar arniya da Kuma musulmi Where stories live. Discover now