CHAPTER 26_30

10 0 0
                                    

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*🏡A GIDAN MU SUKE🏡*

®️🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[  '''Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women''']
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/ 110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*

                *_Z• W• F•🏝_*

MALLAKIN MARUBUTA BIYU:- 👇
*LEEMART PINKY*
           _DA_
*MRS BASAKKWACE*

_WANNAN LABARIN DAGA FARKON SA HAR ƘARSHEN SA SADAUKAR WA NE GA IYAYEN MU ALLAH UBANGIJI YA ƘARA MUSU LAFIYA DA NISAN KWANA,DA DUKKAN MUSULMAI BAKI ƊAYA,YA ALLAH KAJIƘAN IYAYEN MU TUNDAGA ZAMANIN ANNABI ADAM HAR ZUWA YAU._

*MUNAFUKAI KWALLAHIYAN KU  ALLAH YAKARA MAKU WARIN BAKI KUDADE KUNA MUNAFURCHI KUYI YANDA KUKESO DA WANNAN PAGE DIN SADAUKARWA NE AGAREKU MASU WARIN...... hahhhhh  MUNAFUKAI HOW MARKET MASU BACCI DA ONE  EYE🧐*🤭😂

JINJINA GA -: _MASOYAN GA MASOYAN MU GABA ƊAYA_

*PAGE 26&30*

Yo kan Jahda tayi,Abie a zuciye yayo kanta ya cakumota ya falla mata wani mugun mari da saida ta koma ta zauna kan ƙafafuwan  ta,suka sake wani ƙara,Hajiya Jamila ƙaran da ƙashin ƙafanta yayi saida yasata sakin itama mugun ƙara ,kallon kowa ya koma kanta,sai cija lips take amma ba wanda yace mata sannu,don Hajiya Jamila bata da mutunci kowa baisonta sai ƴan koran nata.

"Haba Jabeer miyasa kake dukan ta?.

Ran Hajiya Mamah a ɓace take maganan.

Ƙwafa yayi yace,"Jahda kifaɗa mana inda uwarki ta kaiki tsawan kwana tara".

Yai maganan idon shi na kanta ya kafeta tsam.

Ƙara takure kanta tayi waje ɗaya,duk tagama firgita da tsorata ga yanayin kowa dake ɗakin musaman mahaifinta .

Daka mata wani mugun tsawa yayi dasai da ƴan hanjin ta suka kaɗa.

Baki na rawa zatafara basu labarin inda Ammien ta takaita,Ammie tai kukan kura ta buga tsalle ta manta da ciwon da azabar da takeji a ƙafanta tayo kan Jahdah tai mata shaƙa,irin ta ban mamakin nan,take idanuwan Jahdah suka fito ƙulu-ƙulu kamar za'a zare mata rai.

Kuka Hajiya Mama ta ɓarke dashi,yayinda da ƙyar aka ƙwace Jahdah,wanda ko ƙwa-ƙw-ƙwaran numfashi batayi.

Hajiya Jamila gefe ta koma tana ta zaro ido kamar sabon hauka.

Jaheer ɗaukar Jahdah yayi a kafaɗan shi,sai tashin wari takeyi,irin na janaba,gaban shi yankewa yayi ya faɗi,tsoro yacika shi,karde yarinyar nan maza takebi?.

Ya tambaye kanshi tambayan da ba mai bashi amsanta sai in ita kanta,tou mai Ammie take ɓoyewa,miyasa ta hanata gayan inda taje?.

Dafe goshin sa yayi daidai lokacin da ya shiga part ɗinshi da ita,kwantar da ita yayi akan doguwar kujera,ya nufi bedroom ɗinshi ya ɗauko kayan aiki.

********
A side ɗinsu ko da ƙyar aka lallashe Hajiya Mama tayi shiru.

Hajiya Jasmin ta tallafa mata sukaje side ɗinta,can suka iske su Juliet da basusan wainar da ake toyawa ba.

Abie tunda Jaheer ya fita da Jahda shima ya miƙe ya nufi sama,wani jiri na ƴaban sa,ƙarfin hali kawai ya gwada dana mijin ƙoƙari har yashiga bedroom ɗinsa,yasa key ya faɗa kangado ya dafe kai,tunani iriiri suna zuwa kansa game da halin matar tashi.

 A GIDANMU SUKE Labari ne akan Soyayyar arniya da Kuma musulmi Where stories live. Discover now