chapter 36_40

9 0 0
                                    

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*🏡A GIDANMU SUKE🏡*

®️🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[  '''Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women''']
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/ 110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*

                *_Z• W• F•🏝_*

MALLAKIN MARUBUTA BIYU:- 👇
*LEEMART PINKY*
           _DA_
*MRS BASAKKWACE*

_WANNAN LABARIN DAGA FARKON SA HAR ƘARSHEN SA SADAUKAR WA NE GA IYAYEN MU ALLAH UBANGIJI YA ƘARA MUSU LAFIYA DA NISAN KWANA,DA DUKKAN MUSULMAI BAKI ƊAYA,YA ALLAH KAJIƘAN IYAYEN MU TUNDAGA ZAMANIN ANNABI ADAM HAR ZUWA YAU._

JINJINA _*GA REKU UR FANS GASKIYA FANS MUNA GODIYA KUMA MUNA YABA MUKU DA NAMIJIN ƘOƘARIN DA KUKEYI AKAN ƘARFAFA MANA ƘWARIN GUYWA TA HANYAR COMMENTS,ALLAH UBANGIJI MUMA YABAMU IKON FARANTA MUKU TA HANYAR SUBURBUƊO MUKU POST A KOWANI RANA LOVE  YOU LODI-LODI  UR FANS💞*_

*PAGE 36&40*

Awanan ranan itace rana ta farko da zuri'an Jaafar Ɗanƙasa ba  gaba ɗayan su suka taru a ɗakin da aka tanada don cin abinci.

Inda Hajiya Jamila  tasa aka kawo musu nasu da ƴaƴanta ɓangaran su sukaci.

Abbie duk da ransa ya ɓaci ,amma ya danne ma zuciyar shi yai kaman bai damuba.

Hajiya Mama ko sai ƙorafi take ina Jamila da yara a kirasu,koda akaje kiransu cima  *JABAL* mutunci tayi ɗan Hajiya Jumainah ne,don ita Jumaina duk ƴaƴanta maza ne kuma basu da girma ƙananune.

Hajiya Mama haƙura tayi tai shiru daga ƙarshe.

Jaheer yaji daɗin abinda Juliet ta haɗa masa yaci sosai kuma yasha drinks ɗin.

*******
Washagari bayan an sakko daga masallacin edi,a aladan gidan babban falon Hajiya Kakah ake zuwa a taru,aita ciye-ciye da hotuna cikin nishaɗi.

Kowa na zazzaune ansa Hajiya Mama a tsakiya amma ba Jahdah da Jadidah suna ɓangaran su da uwar su.

"Wai ina Jahda da Jadida ne?.

Faɗan Jalal mijin Hajiya Jasmin.

"Suna ɓangaran su".

Sunan ta kawai da yaji an ambato saida ƙirjin sa ya yanke ya faɗi,innalillahi wa,inna ilaihi rajiun kawai yake nanatawa a zuciyar shi.

"Kai Jamal jeka kirawo su ".

"Aa ka barsu zasuzo".

Faɗan Abie da yasan ko shakka babu Jamila ta hana Jadidah fitowa cikin gida,amma yasan maganinta a ruwan sanyi zai dafa ta.

Jaheer lokaci ɗaya yaji zaman ya gundire shi ya miƙe yana ɗan yamutsa fuska yasa kai ya fice batare da ya ma kowa magana ba.

Ɓangaran mahaifiyar shi ya nufa.

*********
Zaune take a gefen makeken gadon ta tana waya ya shigo ya kwanta akan gadon yai matashi da cinyarta tare da lumshe ido yana shaƙan ƙamshin mahaifiyar shi.

"Kaiiiiiiiiii Yaya shagwaɓa".

Shigowan ta kenan ganin yafito yasa ta biyo bayan shi,don tana so tayi mai wata tambaya.

Kallon shi take tana cuno baki.

Buɗe ido ɗaya yayi ya kashe mata,tare da cewa a ina nai shagwaɓa ni kece ki magana kinji nayine".

 A GIDANMU SUKE Labari ne akan Soyayyar arniya da Kuma musulmi Where stories live. Discover now