chapter 76_80

10 1 0
                                    

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*🏡A GIDANMU SUKE🏡*

®️🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[  '''Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women''']
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/ 110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*

                *_Z• W• F•🏝_*

MALLAKAR👇
*LEEMART PINKY*
           AND
*MRS BASAKKWACE*

_WANNAN LABARIN DAGA FARKON SA HAR ƘARSHEN SA SADAUKAR WA NE GA IYAYEN MU ALLAH UBANGIJI YA ƘARA MUSU LAFIYA DA NISAN KWANA,DA DUKKAN MUSULMAI BAKI ƊAYA,YA ALLAH KAJIƘAN IYAYEN MU TUNDAGA ZAMANIN ANNABI ADAM HAR ZUWA YAU._

*PAGE 76&80*

Murmushi tayi tare da shafo fuskan shi tace,"Yaya ka kwantar da hankalinka sister tana sonka,shiyasa take kishin ka,zanje in mata magana nasan zata fahimce ni".

"Yauwa Jawahir nagode sosai".

Cikin sanyin murya yake magana kamar zai fashe da kuka yake magana.

*******
"Sister please ki fahimce ni wallahi ba Yaya yai mata ciki ba,boka ne inda Amie takaita kwanaki".

Jawahir ce zaune gaban Juliet tasa guywowin ta a ƙasa ta riƙo hannayen ta duka biyu gam a cikin nata hannuwan.

Juliet ko sai kauda kai takeyi tana haɗa rai jin Jawahir maganan Jahir tazo mata dashi,jin abinda Jawahir ta faɗa yasa Juliet gwalalo ido tana kallonta cike da tsoro

Nan Jawahir ta kwashe komi da ya faru ta faɗa mata,itako sai kuka takeyi taji tausayin masoyinta,ta hukunta shi ba akan laifin shi ba,ta azabtar da zuciyar ta.

Ɗaukan wayarta tayi ta tura masa mesaage naban haƙuri.

Jin ƙaran mesaage yashigo wayarshi yai saurin dubawa ganin masoyiyar shi ce jikin shi har rawa yake ya buɗe yana sakin ƙayataccen murmushi kamar tana gaban shi sai maimaitawa yake yana ƙara karatawa ,tura mata reply yayi shima.

Tundaganan suka shirya sai wani kulawa da tarairayan juna,basu kunyar nuna ma juna kulawa agaban ko ma waye.

Ummie ko bata son soyayyar dake tsakanin Juliet da Jaheer

Kullum sai tayi mai faɗa,amma saide yai ta bata haƙuri.

*******
Hajiya Jamila ko gidan bokaye lungu da saƙo suna shiga suna bada ƴan kuɗaɗe amma ba biyar  buƙata.

Burinta ta koma ɗakinta,sannan Jahir ya aure Jahdah.duk da bata bi takan Jahda ,Jahda na side ɗin Hajiya Jasmin.

*******
Antsaida ranan auran Jaheer da Juliet,Jahoor da Jawahir,Jadida da Jawad yaron abokin Abie,wata ɗaya aka saka inda ake ta shirye-shirye akeyi ,yayinda zuciyar Jahda kamar ta fashe don baƙin ciki.

Jaheer da Juliet da Jesica sun shirya sunje ƙauyen kakannin su,inda sukai kwana biyu suka dawo,bayan sun cika su da sha tara ta arziki.

Haka rayuwa taci gaba da tafiya da daɗi ba daɗi wata rana fari wata rana baƙi.

Yayinda ko wane ɓangare ake ta shiryeshiryen biki,Hajiya Jasmin ita tazamo uwar Juliet tana mata komi na uwa,daya dangance gyaran amarya da saye-saye.

*********
Kai da komowa kawai take yi a tsakiyan tangamemen falonta ranta haɗe ,takai gwauro takai mari,kallo ɗaya zakai mata kagano tsantsan tashin hankalin dake ɗauke akan fuskan ta.

Juyowa tayi daidai yashigo tsakiyan falon ta ɗauke lafiyayyan fuskan shi da mugun mari wanda ,dabadin jarumtar daya gwada ba da sai yakai ƙasa.

Dafe kumatun shi yayi yana kallon ta kallo mai cike da mamaki zai buɗe baki ya ƙara magana bata bashi daman haka ba ta ƙara ɗauke shi da mari.

Huci kawai take kamar na namijin zaki.

"Hajiya Jamila kin min dai-dai kin kyauta".

Faɗar Hajiya Jumainah da shigowan ta kenan falon,itama ranta haɗe.

Da mamaki yake kallon Hajiya Jumainah.

"Hajiya takaicin yaronnan nakeyi,ni wallahi da haihuwar ka Jahoor gwamma mutuwar ka".

Rai ɓace take maganan.

A gigice yake kallon mahaifiyar shi da yanzun sam bata ƙaunar shi,tafita hayyacinta,wani zafi kalaman ta yakeji xuciyar shi take tai masa nauyi da baƙi.

"Wannan ɗan ɗan Allah bani ne,ace asaki uwarka baka ko damu ba ta auren wata ƴar iska kake".

Faɗan Hajiya Jumaina datawani hayayyaƙo kamar zata duke shi.

"Wallahi Jahoor zan baka zaɓi,wato kana rawan kai gobe zaa ɗaura maka aure akai maka mata ka kwanta da ita ko?,tou ka zaɓa koni ko wancan ƴar iskan,ko kuma kaje ka sa ubanka ya maidani ɗakina".

Jahoor lokaci ɗaya ya zube guywowin sa a ƙasa ya zuba ma mahaifiyar shi jajayen idanuwan shi da suka canja kala suka rine,jin maganan mahaifiyar shi yake kamar garwashin wuta acikin zuciyar shi.

Bata damu da yanayin da ya shiga ba,saɓanin da ko ciwon kai yake hankalinta bai kwanciya sai taji yace yaji sauƙi tukunnan ,amma yanzun ta rufe ido tana cimasa mutunci kamar ba ɗan da tafara naƙuda ta haifa ba.

"Wallahi tallahi,billahillazi kabari gobe aka ɗaura ma aure da wancan ƴar iskan yarinyar wallahi sai kabiyani nono na da kasha,don sai na ɗage maka su".

Jahoor innalillahi wa inna ilaihi rajiun kawai yake maimaitawa acikin zuciyar shi,don gani yake kamar a mafarki wannan abinda mahaifiyar shi ke yi,gani yake kamar ba Amie su bane maison su da ƙaunar su.

"Mai ake da jinin Juwairah gayyan tsiya,gayyan na ayyaro,in kanason albarka kabi maganan uwarka".

Faɗar Hajiya Jumaina da take zaune ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya.

Da ƙyar Jahoor ya iya buɗe bakin shi da ya masa nauyi ji yake halshen sa ya cika masa baki yace............!

MORE COMMENTS
MORE TYPING

*MRSBASAKKWACEPINY*

 A GIDANMU SUKE Labari ne akan Soyayyar arniya da Kuma musulmi Où les histoires vivent. Découvrez maintenant