chapter 16_20

23 3 0
                                    

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*🏡A GIDANMU SUKE🏡*

®️🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[  '''Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women''']
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/ 110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*

                *_Z• W• F•🏝_*

MALLAKIN MARUBUTA BIYU:- 👇
*LEEMART PINKY*
           _DA_
*MRS BASAKKWACE*

_WANNAN LABARIN DAGA FARKON SA HAR ƘARSHEN SA SADAUKAR WA NE GA IYAYEN MU ALLAH UBANGIJI YA ƘARA MUSU LAFIYA DA NISAN KWANA,DA DUKKAN MUSULMAI BAKI ƊAYA,YA ALLAH KAJIƘAN IYAYEN MU TUNDAGA ZAMANIN ANNABI ADAM HAR ZUWA YAU._

*KACOKAN WANNAN PAGE DIN SADAUKARWA NE GA MUNAFUKAI MUNA SANE DAKU ALLAH YAKARA MAKU WARIN BAKI KUDADE KUNA MUNAFURCHI KUYI YANDA KUKESO DA WANNAN PAGE DIN SADAUKARWA NE AGAREKU MASU WARIN...... hahhhhh  MUNAFUKAI HOW MARKET*🤭😂

JINJINA GA -: _MASOYAN GA MASOYAN MU GABA ƊAYA_

*PAGE 16&20*

Jin maganan sukai kamar diran aradu,lokaci ɗaya suka kalla inda maganan ke fitowa,duk gaban su  na dukan uku-uku,atake suka zaro ido.

Yayinda Jadidah jitayi wani fitsari yazo ya ƙulle mata mara ƙoƙarin kufce mata yakeyi.

"Juwairiya angaya miki shiru-shiru tsoran ku ake ji?, wannan kyara da hantarar da kuke musu shi zaisa su koma addinin ku koko?,wallahi andaɗe ana ruwa ƙasa na shanye wa in faɗa miki na gaji da wannan mugun halin naki da dabaki dashi,zuwan Hajiya Jamila ta lalata ki".

Cike da tsan-tsan ɓacin rai mai cike da tarin takaici yake maganan.

Shiru Juwairah tayi tana rarraba idanuwan ta,don ta tsorata da yanayin mijin nata,rabon da taga ɓacin rai haka a fuskanshi bazata iya tuna rana ba.

Yayinda Jadida,jikinta harrawa yake yanda taga ɓacin rai akan fuskan Abban su,don shi bai fiye faɗa ba komai za'ai sai dai ya kauda kai yayi kamar bai gani ba.

"Tou wallahi ya isheki kin soma kaini maƙura,kin ma kaini zan gaya,akan bayin Allah nan zamu iya samu mummunan matsala dake wanda baki taɓa tsammani ba,inbanda dabbanci kalan naku na mata,kun azabtar da mahaifiyar su,kungwada mata kishi na kafirci,sannan ta mutu ƴaƴa sun girma kishi ya dawo kansu ko wai shin ke akai ma kishiyar koko Jamila,halan Jamila itace mahaifiyar ku,ade girme kin girme Jamila amma ta maida ki sakaran mace samna,duk inda tayi da bindin tanan kuke biye".

Magana kawai yake idon shi a rufe yana ta zazzaga mata masifa,ta inda yake shiga batanan yake fita ba,ya tabbatar mata cewa inhar Jaheer  na son Juliet wallahi in itama na son shi sai ya tsaya kai da ƙafa yaga ta aure shi,saidai su mutu.

"Ke kuma Jadida munafuka ce ashe ke mai fuska kamar na uwarki,tou zanga Jabeer ɗin daga ke har ƴar uwanki kun gansame a gida ,ko kufito da miji ko insamo duk wanda naga ya dace in laƙa muku,bokon banza bokon wofi".

Fuuuu ya haura sama  don wani mugun haushin Juwairah yakeji amma yasan maganin ta.

Jadidah ko tana zaune kamar anjiƙa ta da ruwa duk sanyin Ac dake ɗakin bai hanata tayi zufa ba,daga ita har Hajiya Juwairah,ganin ya wuce  yasa Jadidah tashi da gudu ta faɗa toilet ɗin falon ta sake fitsarin da ya cika mata mara.

Juwairah ko zama tayi tai tsuru-tsuru,tana tunanin maganan mijin nata,har Jadidah ta fito ta tafi side ɗinsu bata san ta fita ba.

********
Kwance yake yayi rub da ciki tunda Jahdah ta fita ya leƙa kitchen ɗin sa yaga bata ba alaman ta ya tabbatar ta tayi tafiyan ta ne komawa yayi ɗaki ya faɗa kan gado yai rub da ciki,yayinda ya lumshe ido tunanin Juliet ya addabe zuciyar sa,yana mugun son yarinya,a duk wani second dake bugawa a agogon duniya ji yake sonta na ƙara shiga zuciyar,Allah yasa taso shi kamar yanda yakeson ta  koda ma ɗan rabin son da yake mata ne,da tunanin ta har bacci ya ɗauke shi.

*********
Aure!Aure!!Aure!!!,faɗar Jahda da Hajiya Jamila da Hajiya Jumainah,dukan su cike da mamaki suka faɗa kalman.

Jadidah dake zaune ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya nan ta kwashe komi ta basu labari harda gishiri a miya saida ta zuba.

Jahdah gabanta tsanan ta bugu kawai yake ta tabbatar Jaheer bazai taɓa cewa yana sonta ba Juliet zai zaɓa.

Kutumar kaza-kazan can nan ta fara lailayo ashar tana watsawa kafin tace,"wallahi ba ɗan iskan da ya isa yai ma ƴata auran dole,abinda takeso ko sai anbata,saide suyi biyu babu arniyar can ta rasa itama ta rasa".

Dariya Hajiya Jumaina ta kwashe dashi tana tafa hannu,duk suka koma kallonta da mamaki mai take ma dariya.

Saida tayi mai isarta kafin ta kalle Hajiya Jamila a kai-kaice, tace,"Hajiya kaɗan kika gani,na gaya miki hanya mafita kun maidani sha-sha-sha sauna,kuci gaba da kallon ruwa kwaɗo ko sai yayi muku ƙafa".

Cizon ɗan yatsa Jamila tayi kamar mai tunanin wani abu tayi shiru tsawan daƙiƙai can tace,"ai yanzun Jumainah dole inbi ta taki itace hanya mafi sauƙi wacce zata ɓulle min inga ƴata ƴar autata ta aure abinda takeso".

Ohh Hajiya Jamila in gaya miki ruwan da ya dakeka shine ruwa,don haka yanzun duk wacce kika ganta a ɗakin miji zaune ta wanke biyar ta tsoma goma tou ta miƙe da addu'a,gidan malamai ba tsoho ba tsohuwa,ba yaro ba babba,kowa neman mai galmi yake".

"Sauke ajiyar zuciya  Jamila tayi tace,"hakane kuma aidole in miƙe yanzun tunda naga zaa min ƙarfa-ƙarfa".

Nan Hajiya Jumaina ta rinƙa kwantar ma da Jahda hankali akan tayi haƙuri Jaheer sai ya mata kuka.

Nan ta rinƙa murna da farinciki.

*********
Shirye-shiryen tashi ake da azumi washagari,tunda sassafe suka shirya suka nufi gidan Hajiya Naa'ima ,suka rankaya gidan malamin ta,duk layin da akwai saida suka zauna suka jira har layi yazo kansu.

Tunkafin suyi bayani,bokannan ya raftaka musu duk abinda ke tafe dasu,nan yace su aje kuɗi suyi ta fiyar su,suyi imani dashi kawai zasu ga aiki da cikawa,amma aljanin da zaiyi aikin yace yana buƙatar kwanciya da yarinyar don da maniyinta zaiyi aikin ,inde akai ɗakin Jaheer ko uwar sa bazai ƙara jin maganan ta ba inba na Jahdah ba.

Hajiya Jamila ba tare da tunanin komi ba idonta ya rufe tace za'a kawo ta,biyan kuɗi masu yawa sukai suka tafi,bayan ya gaya musu a goman ƙarshe zaa kawota da rana in tana azumi,anfi so ayi in baki na kulle.

Hajiya Jamila ko batare da damuwa ba ta amsa,suka wuce baccin kowa ta gama gayan abinda takeso.

*HASBUNALLAHU WA NI'IMAL WAKUL,ALLAH YA RABAMU DA KISHIN SAURI IRIN HAJIYA JUMAINA,ALLAH YA RABA MU DA MAHAIFIYA IRIN HAJIYA JAMILA MASU TO SHASHSHIYAR ƘWAƘWALWA DA BASU KALLON MI ZAIJE YA DAWO.*

********
Ranan litinin aka tashi da azumi,ganin ana azumi kuma duk ƴan aikin gidan musulmai ne,sun tashi-tashin asubah suna bacci,yasa Juliet da Jesica,tashi suka gyara side ɗin su  tass ,don dama su basu da gandar aiki,Hajiya Kaka ke hanasu aiki ko zasuyi,don su asali sun tashi cikin yin aiki sosai wajan kakanin su.

Da kansu suka shiga kitchen suka dafa ma kansu abinci suka gyara kitchen ɗin suka tafi side ɗin kakan su suka zauna  suka ci duk tana bacci,gyara side ɗin sukai kafin suka tafi sai ɗin Momynsu Jasmin itama sukai mata gyara,kafin suka koma side ɗinsu sukai wanka suka shirya suka tafi church,sai two suka dawo gidan ,wanka kawai sukai suka canja kaya suka fito kitchen.

Ƴan aiki sai aiki sukeyi,sannu sukai masu yayinda Jesica ta zauna ta fara taya su aiki yayinda Juliet ta ɗaura musu imdomie duk da Baaba Asabe  ta so hanasu suka kafe.

Tundaga wannan lokacin kullum    dasu Jesica ake aikin buɗe baki,duk da Hajiya Kaka na hanasu amma sunƙi ji,haka ta haƙura ta barshi.

Abinnan da suke ba ƙaramin ƙara burge Jaheer yake ba,wani ƙara son Juliet yake shigan sa don tunda yake   bai taɓa ganin ƙannan shi ƴan son jiki a kitchen ba,saide suci azo a ɗauke plate ɗin.

Jahoor da Jawahir ko tsantsan soyayya suke ma junan su burin su kowa ya faranta ma ɗan uwanshi,basa ƙaunan ɓacin ran juna,duk da soyayya zomu zauna zomu saɓane,amma ko sun saɓa kanmintina ƙalilan sun shirya.

******
"Ammie da aljani fa kikace zanyi sex?.

Cike da tsoro da firgici ƙarara take maganan.

Wani mugun kallo Ammie nata ta wurga mata kafin tace,".........!

*SHIN JAHDA ZATA YARDA TAJE KOKO????*

MORE COMMENTS
MORE TYPING
*PINKYBASAKKWACE.COM*

 A GIDANMU SUKE Labari ne akan Soyayyar arniya da Kuma musulmi Where stories live. Discover now