chapter 31_35

7 0 0
                                    

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*🏡A GIDANMU SUKE🏡*

®️🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[  '''Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women''']
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/ 110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*

                *_Z• W• F•🏝_*

MALLAKIN MARUBUTA BIYU:- 👇
*LEEMART PINKY*
           _DA_
*MRS BASAKKWACE*

_WANNAN LABARIN DAGA FARKON SA HAR ƘARSHEN SA SADAUKAR WA NE GA IYAYEN MU ALLAH UBANGIJI YA ƘARA MUSU LAFIYA DA NISAN KWANA,DA DUKKAN MUSULMAI BAKI ƊAYA,YA ALLAH KAJIƘAN IYAYEN MU TUNDAGA ZAMANIN ANNABI ADAM HAR ZUWA YAU._

JINJINA GA -: _MASOYAN GA MASOYAN MU GABA ƊAYA_

*PAGE 31&35*

Mutuwar tsaye Jaheer yayi da ƙyar ya iya buɗe baki yace,"Jahdah mai kikeso ki gayamin please ki faɗa min kinji,ki faɗa min komi".

Duƙar da kanta tayi ƙasa cike da tsananin kunyar abinda zai fito bakinta ,zata faɗa mai don shine mafita,ta tabbatar da hakan zaisa yasota ya aureta.

🙄🙄🙄🙄🙄🙄🙄  *WOLLE KINA RUWA KUSA DA ƘATON KADA A TUNANI NA,AMMA BANSAN TUNANIN JAHEER BA🤗*

"Yaya Jaheer zan faɗa ma  ,amma dan Allah karka gaya ma Abie hankalin shi ya tashi".

"InshaAllahu ba wanda zaiji dagani sai ke ki yarda dani ki faɗa min".

Cike da zaƙuwa yake maganan.

Ɗaga shanyayyun idanuwan ta tayi ta zuba masa ido,yayin da shima zuba mata idanuwan yayi,jikin shi harrawa yakeyi don ya ƙosa yaji mai zata furta tace,"Aljani,aljani,aljani,wajan aljani Amie ta kaini yai sex dani ina azumi".

Atsorace yake kallonta,jin maganganun ta yakeyi kamar saukan aradu suna mai amo bibbiyu acikin dodon kunne.

Sa hannun yayi ya toshe kunnan sa yana girgiza kai,yayinda idanuwan shi duk suka fito sabida tsaban firgici,zube guywowinsa yayi a ƙasa lokaci ɗaya.

Tsoro da firgici yashiga Jahdah sosai ganin yanayin Jaheer ya sauya take yanke,yana nema ya zame mata wata halitta na daban.

Sa hannu yayi ya kashe kansa da mari yana girgiza kai,a hankali yake furta alhamdulillahillazi ahayana,baada ma 'ama tana wa ilaihin nushur,a tunanin shi bacci yake wanda sheɗan yazo masa da mummunan mafarki mai wiyar fasaltawa,yasa yake addu'an tashi daga bacci.

"Ya rabbb in bacci nake nakeyin wannan mummunan mafarki,mai ƙunci da jarabta,Allah kai gaggawan tashina daga wannan baccin".

Awani mummunan murya,mai cike da tashin hankali yake maganan,yana magana tana sartsewa a maƙoshin sa.

Atsorace a firgice ta miƙe tare da fashewa da kuka,ta zube guywowin ta a gabanshi gabda shi,numfashin su na bugan na juna.

********
"Ummie kinga ga kalanta nan,mutanan da kika maidasu aminai,kika maidasu wata tsiya yau su suke cin mutuncin ki a gaban idon ki,Ummie shiyasa nakeson Aunty amarya sam bata munafinci,da kayi ba daidai ba zata kiraka ta faɗa ma".

Jawahir ce dake kwance kan cinyar mahaifiyanta bayan ta gama lallashinta tayi shiru take  wannan maganan.

Murmushi Juwairah tayi tare da sa hannu ta shafo suman kan ƴartata tace,"kicire komi a ranki ,rayuwar nan sauƙi ne da ita,kuma ƴar haƙuri ce,duk yanda kazomata haka take ɗaukan ka,sannan ki rinƙa kauda kai ko kin gani kiyi kamar  baki gani ba,inkinji kiyi kamar bakiji ba,kici gaba da basu girman su amtsayin su na iyayen ki kamar yanda da kike basu,banso ki masu wani kallo ko kalma mara kyau,shawara nabaki a matsayina na mahaifiyar ki ba umurni ba".

 A GIDANMU SUKE Labari ne akan Soyayyar arniya da Kuma musulmi Where stories live. Discover now