chapter 56_60

7 0 0
                                    

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*🏡A GIDANMU SUKE🏡*

®️🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[  '''Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women''']
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/ 110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*

                *_Z• W• F•🏝_*

MALLAKAR👇
*LEEMART PINKY*
           AND
*MRS BASAKKWACE*

_WANNAN LABARIN DAGA FARKON SA HAR ƘARSHEN SA SADAUKAR WA NE GA IYAYEN MU ALLAH UBANGIJI YA ƘARA MUSU LAFIYA DA NISAN KWANA,DA DUKKAN MUSULMAI BAKI ƊAYA,YA ALLAH KAJIƘAN IYAYEN MU TUNDAGA ZAMANIN ANNABI ADAM HAR ZUWA YAU._

JINJINA GA -: _MASOYAN GA MASOYAN MU GABA ƊAYA_

*PAGE 56&60*

Saide sukaji saukan abu glass ya fashe tartsatstsatsaaa.

Salati mutane suka farayi,Hajiya Jumainah ko kamar jira take itama tafito da nata.

Nan suka fara ruwan fasa glass ɗin  motoci da ƙyar aka fidda amarya da ta gama tsorata.

Binta Jamila tayi ta cakumota gammm ,hankalin mutane ya tashi ƴan uwan amarya sukai kan Hajiya Jamila da Jumaina da bugu,nan waje ya kaure da dambe.

Sarkin yawa yafi sarkin ƙarfi nan sukai ma Jamila da Jumaina dukan tsiya.

Maza ma kasa ansar su sukai saide suka zama ƴan kallo.

Kiran Alhaji Jabeer akai aka sanar mai hankali tashe ya dawo gida da abokanan sa.

Lokacin har anshiga da amarya ɓangaranta danginta sai bala'i sukeyi,basu haƙuri yayi sosai,da ƙyar aka rarrashe amarya *JUHURA* ƴan uwanta suka tafi.

Hajiya Jamila ko jikin ta ƙaura yai la'asar don sun jibgu.

Hajiya Mama da Hajiya Jasmin abin ya musu daɗi wannan bugun da su Jamila suka sha.

Saida ta rinƙa gasa jiki da ruwan zafi don Abie ya hana Jaheer ya taɓa ko ɗayan su kulle shima yayi a ɗaki ya kwashe key ɗin ,sannan yace tana fita a bakin auranta koda ko mizataje yi.

*********
Kai da komowa take a tsakiyan bedroom ɗinta ,tunanin ta da hankalinta yana wajan mijinta,yanzun yana can yana tarayya da yarinya ƙarama ƴar cikin shi.

Duban ta takai kan agogon dake manne a bangon ɗakin ƙarfe 04:49am,gani tayi daran yayi tsawo ta ƙosa taga  safiya ta waye taga idon wannan ta tsi-tsiyar yarinyar da ta ƙwammace ta aure tsoho da yara.

Batabar kai da komowa ba saida aka kira sallah asubah ta zauna bakin gado,taci gaba da tufka da warwara bacci ɓarawo a lokacin yai nasaran sace ta.

********
Zaune suke a garden  ɗin gidan su,wanda yasha korayen furanni da pink colour.

Jikin su na manne da juna yayin da gashin kanta ya barbazo ya rufe mai fuska ,shaƙan numfashin juna suke,atare fitan bugun zuciyar su yake fita sabida tsananin ƙauna.

Shafo fuskanta yayi da tattausan hannun shi cikin san yayyar murya yace,"Baby kinyi shiru,tunanin mai kikeyi haka?.

Murmushi tayi ta ƙara shigewa jikin sa kamar zata tsaga fatan shi ta wani ƙara kwantar da murya tace,"tunanin ka Babyna,jinake a zuciyata kamar wata tanaso ta ƙwace min kai".

Murmushi yayi tare da lakuto hancin ta yace," ai zuciyar Jahir har abada ta Juliet ne,inshaAllahu sai mun zama mafi kwatanci wa ƴanda ake kwatantawa acikin masoya".

Hot kiss ta sake mai a kumatu,sabida tsananin jin daɗin kalaman sa da tayi.

Lokaci ɗaya kuma ta miƙe daga kwance da take akan kafaɗar sa ta zuba masa ido kamar mai nazarin wani abu.

Ɗaga mata gira ɗaya yayi tare da kashe mata ido guda,lokaci ɗaya tai ƙasa da kanta tana murmushi don salon Jaheer gabaki ɗaya ƙara rikitata yakeyi yana ƙara jefa ta a soyayyan sa tsundum.

******
"Ammie bokannan macuci ne har yanzun Jaheer ko kallona baiyi sannan ance aikin sa kamar yankan wuƙa,kullum yana liƙe da wancan arniyar ƴar najasa,ni wallahi yau sai naci uban ƴarnan sai naja mata layi da masoyina na gaji zuciyata sam bazata iya ɗauka ba".

Cike da tashin hankali Jahda ke ma mahaifiyarta magana.

"Ke dalla haushina dake kin cika wutan ciki,kwanaki arba'in ya ƙayyade yau saura kwana takwas ki zuba ido,ni yanzun ma naki bai dameni ba,wancan shegiyar amaryan nakeso karku raga mata,inde kunsha nono na kuci ubanta in tashiga har kan ku,kai koma bata shiga ba".

Ɗan gajeren tsaki Jahda ta sake tare da miƙewa fuuuuu ta fita.

********
"Jesica kiyi sauri lokaci ya ƙure yanzun nasan pastor y.......!

Saukan marin da taji akan lafiyayyan fuskanta yasa wayar hannun ta da take tsaye bakin part ɗinsu  takira jesica da ta shanyata waje a tsaye daga bari ta ɗaura ɗankwali ta rigata fitowa don tai sauri amma  shiru kusan ten munites yasa ta kirata.

Dafe ƙuncinta tayi a razane take kallon mai tsaurin idon da ta bata mari irin wannan,ganin wacece yasa tabar mamaki.

Tsaye take ta riƙe ƙugu tana karkaɗa jiki tana jifan Juliet da wani kallon wulaƙanci da ƙasƙanci tace,"ke yarinya hawainiyar ki ta kiyaye ramata ,don baki da mutunci da hankali ƴar iska kike wanda nikeso shi kike so ,ni sa'ar wasan kice da zaki rinƙa haɗa kafaɗa da zuciya dani?.

Shiru Juliet tayi tai ƙasa da idonta tana kallon wayarta da ta watse.

Daidai lokacin Jesica ta fito ta buɗe baki zatayi magana ta tsaya turussss tana kallon Jahdah dake girgiza kamar kanya.

Shegiya arniya ƴar......!

Kan ta ƙarashe cin mutuncin nata taji wani wawan saukan mari a bakinta ta ƙarajin saukan sa.

Atsorace Juliet ta riƙo hannun Jesica da take ƙoƙarin ƙara marin Jahdah da ta dafe baki tana zaro ido.

Jan hannun ta tayi suka fara tafiya.

Jahdah ta zabura ta jawo bayan rigan Jesica da idonta ya rufe don ɓacin rai,ko yaushe zasu samu ƴanci a gidan mahaifin su oho.

Da guywar hannu takai mata duka sai a ƙirjinta tai baya  ta faɗi ƙasa wanwar ta wani sake ƙaran da yaja hankalin mutane zuwa wajan.

Azuciye Jesica  ta bita tasa ƙafa ta take  mata ƙafa ɗaya da takalmin ta mai tsini.

Hankalin Juliet ya tashi tasan Jesica ta fitar ma Jahda da jini ajiki ƙaramin aikinta ne.

Sa hannu tayi zata ɗagota ta tureta tayi baya saura kaɗan ta faɗi.

Murza ƙafar tayi da tsinin takalmin ta wani saki mugun ƙara da sai da gidan ya ɗauka.

Ƴan aikin gidan gashi duk sun zagaye su ba wanda yace komi ,ido kawai suke ba abinci.

Duk ranan da kika ƙara ce mana arna ko shegu,in mu shegune kema shegiyace,ba gwamma arne ma dake ba,mu da muke ba addinin mu ɗaya ba,munfiki tarbiya da hankali da natsuwa,sallah biyar kukeyi a rana amma ban taɓa ganin kinyi ba,ashe haka musulincin take?,musulinci yazo muku da rufe jiki,amma ban taɓa ganinki da shiga irin ta musulmai ba,musulinci yazo muku da son ƴan talakawa na ƙasa da ku,amma burinku kullum ku wulaƙanta wanda ke ƙasan ku ,muda muke ba musulmai ba kullum muna zuwa bauta muna girmama kowa miye a musulinci da azaman mu daku muka amfana ba mu amfana da komi ba,da badin mun samu tarbiya ba da yazun mun ɗau hali irin naku".

Rannan nata a haɗe take magana,cike da kakkausar murya kuma bata dena juya takalminta aka ƙafar Jahda ba dake kwance.

Nisawa tayi taci gaba da faɗin.

*MANAGE PLS*

*MRS BASAKKWACEPINKY*

 A GIDANMU SUKE Labari ne akan Soyayyar arniya da Kuma musulmi Where stories live. Discover now