chapter 51_55

5 1 0
                                    

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*🏡A GIDANMU SUKE🏡*

®️🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[  '''Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women''']
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/ 110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*

                *_Z• W• F•🏝_*

MALLAKAR👇
*LEEMART PINKY*
           AND
*MRS BASAKKWACE*

_WANNAN LABARIN DAGA FARKON SA HAR ƘARSHEN SA SADAUKAR WA NE GA IYAYEN MU ALLAH UBANGIJI YA ƘARA MUSU LAFIYA DA NISAN KWANA,DA DUKKAN MUSULMAI BAKI ƊAYA,YA ALLAH KAJIƘAN IYAYEN MU TUNDAGA ZAMANIN ANNABI ADAM HAR ZUWA YAU._

*KACOKAN WANNAN PAGE DIN SADAUKARWANE GA A GIDANMU SUKE FANS GROUP 1 and GROUP 2 MUNAJIN DADIN YANDA KUKE NUNAMA NA KAU'NA KUYI YANDA KUKE SO DAWANNAN PAGE DIN NAKUNE*🥰🥰😍

JINJINA GA -: _MASOYAN GA MASOYAN MU GABA ƊAYA_

*PAGE 51&55*

Faɗar boka bayan ya ƙyalƙyale da dariya da jajayen haƙoran sa.

Awani razane ta miƙe ta ɗaura hannu akai ta kurma uban ihu da saida dajin ya ɗauka gaba ɗaya.

Wani mugun tsawa boka ya buga mata da sai da ta kusa sakan fitsari tare da haɗiye sauran  ƙaranta da zata ƙara bugawa.

"Kullllllllll ɗan jugaji baya son ihu".

Ya faɗa ranshi a murtuke.

Komawa tayi ta zauna kan ƙafafuwan ta daɓas.

Hajiya Jumainah ko farinciki kamar ya kasheta jin har an ɗaura auran Abie .

"Ki zauna ki natsu ,ki ɗebo min jinin aladar amaryan ki kawo akwai abinda zan haɗa miki".

"Alada kuma boka,ina zan samo shi?.

Cike da tashin hankali take maganan.

"Kiyi ƙoƙari ki samo nan da kwana biyu".

Daga haka ya sallame su ya ciga ba da ganin mutane.

*********
"Ki kawo min abinci side ɗina yanzun".

Jahoor ne ke zaune kan lumtsatstsun kujerun falon shi da yasha gyara da ƙamshi yake magana a waya,kuma yana gama maganan da yake ya katse wayar ya koma ya kishingiɗa ya lumshe sexy eyes ɗin shi.

******
"Ummie zankai ma Yaya Jahoor abinci ,shine ya kirani".

"Ok aishi baison shiga mutane cin abinci tun yana ƙaramin shi ɗan ɗakine da wiya kiga Jahoor dianing room,kinga shine babban jika a gidannan saide akai mai ɗakin shi".

Murmushi Jawahir tayi tace,"ai Yaya baida hayani ba ruwan shi da kowa".

"Wai wannan shirin da kukeyi na lafiya ne da Jahoor?.

Dariya Jawahir ta kamayi kafin ta miƙe tace,"Ummie nida yayana in baisoni ba wa zaiso".

"Tou ai naga ko su Jahdah bai sakewa dasu ,amma komi yakeso sai dai ya kiraki".

"Yafi sona a ƴan ƙannan shine".

Tai maganan tana kashe ma Ummie su ido ɗaya.

Throw pillow  Ummie ta ɗauka takai mata jifa ,tafita da gudu tana  dariya.

********
Sai da taje ta ƙara yin wanka ta canja kaya tai lightmakeup ,don tasan masoyin nata baison kwalliya acika fuska kafin ta fito taje ta haɗo mai abinci tayi ɓangaran sa.

 A GIDANMU SUKE Labari ne akan Soyayyar arniya da Kuma musulmi Where stories live. Discover now