chapter 61_65

10 1 0
                                    

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*🏡A GIDANMU SUKE🏡*

®️🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[  '''Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women''']
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/ 110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*

                *_Z• W• F•🏝_*

MALLAKAR👇
*LEEMART PINKY*
           AND
*MRS BASAKKWACE*

_WANNAN LABARIN DAGA FARKON SA HAR ƘARSHEN SA SADAUKAR WA NE GA IYAYEN MU ALLAH UBANGIJI YA ƘARA MUSU LAFIYA DA NISAN KWANA,DA DUKKAN MUSULMAI BAKI ƊAYA,YA ALLAH KAJIƘAN IYAYEN MU TUNDAGA ZAMANIN ANNABI ADAM HAR ZUWA YAU._

JINJINA GA -: _MASOYAN GA MASOYAN MU GABA ƊAYA_

   *PAGE 61&65*

"Nisawa tayi taci gaba da  faɗi,"in wannan shine ɗabi'an musulmai har abada bazan yi fatan shiga musulinci ba in tabbata a ɓata".

Kowa tsaya yayi tsuru yana kallon Jesica dake masifa bako fuskan tausayi take mutsika ƙafar Jahdah.

"Bala'i minake gani ƴata kike takawa ,sannan da yake munafinci baa son mu a gida ana kallo arniya na wulaƙanta min ƴa agaban ƴan aiki".

Cike da bala'i take maganan ƙarasowar ta kenan wajan,tasa hannu ta ture Jesica tayi gefe.

A ƙufule Jesica take kallonta  ,don dabadin darajan taci ita matar ubanta bane da ta kasheta da mari itama ladan ce musu arna da tayi.

Ƙwafa tayi ta juya ta shige ciki da sauri don intaci gaba da tsayawa za'ai ba daɗi a wajan.

Juliet da gudu tabi bayanta.

Nan Hajiya Jamila ta rinƙa zage-zage bayan ta ɗaga Jahdah da daƙyar take motsa ƙafar don  ƙashin ƙafarta ta taku ta juyu da kyau.

Kowa a gidan abin ya mai daɗi ,sabida ba ƙaramin cin kashi ake gwada ma yarannan ba.

*********
Zazzaune suke a falo daga iyayen maza har mata da ƴaƴan su kowacce mata da mijinta .

Abie mai mata biyu amarya na dama uwar gida na hagu.

Hajiya Jamila tsaki kawai take saki ƙasa-ƙasa tana harare hara-re.

Hajiya Mama ko kujeran ta ita kaɗai tana tsakiya  tana kallon kowa ɗai-ɗai.

Shagwaɓe face Juhurah tayi ta kalle Abie ta kwanta kan kafaɗar shi tace,"Honey kasa yarinyar mu ta kawo mani ruwa ba mai sanyi ba".

Cikin wani yanayin salo mai rikita duk ɗa namiji  ,jikin Abie take ya fara rawa ya birkice.

Yace," tou-tou-tou ke Jahda tashi ki kawo ma Maman ki ruwa".

Jikin shi har wani mazari yake yana magana.

Ammie buɗan baki tayi tace,"kutumar uban can".

Tawani miƙe a razane.

Kowa a falon ya naɗe ƙafa yaga abinda zai faru.

Jahoor kauda kansa yayi haka Jaheer ciro wayan shi yayi ya tura ma masoyiyar shi saƙon da   soyayya wanda lokaci-lokaci suke kallon juna suna miƙa ma juna saƙon soyayya.

"Wallahi Jabeer ahir ɗinka ƴaƴan da nayi naƙudan su na basu nono wata ƴar iska da ta gama gantalin bin maza a titi tazo da wani salon karuwanci  tazo tace ita uwar sune".

 A GIDANMU SUKE Labari ne akan Soyayyar arniya da Kuma musulmi Where stories live. Discover now